Littafi na farko 📝
Shafin kyauta na biyar
"Haka ne mana, lafiya ƙalau muke, da fatan ke ma haka?." Cewar Ibrahim. Kafin ta ce wani abu sai Farida ta ba ta amsa ta hanyar cewa
"AlhamduLillah ma chérie ya hidimar biki?"
"An gode wa Allah." In ji Lalla tana sadda kanta ƙasa kamar wacce take jin kunyarsu ko tsoronsu.
Sai Ibrahim ya ciro wayarta a aljihun rigarsa yana mikata haɗe da cewa
"Ga wayarki ƴan'mata, Allah Ya ƙara kiyayewa gaba." Ya yi maganar yana mika mata wayarta.
Sai a lokacin ne ma ta gane wanene ya zo? Kenan daman wanda ya tsinta wayarta ne ya zo, amma shi ne Fati ta ɓoye mata har da cewa bako ne ta ka yi, to kuma ko wa ya faɗa masa unguwar da suke yanzu don Fati gidansu ne ta yi masa kwatance amma sai ga shi ya zo gidan kawu neman su. Kai wannan mutumin akwai jarababbe gaskiya da kuma nacin tsiya saboda tun kiran da na yi masa na farko na tabbatar da hakan saboda yadda ya fara yi min magana hada wani cewa ba zai yafe kansa ba in aka hana min waya kamar na sanya shi dole.
Hannunsa da yake mika mata wayar ne ta kalla saboda bai janye hannun ba dukda ƙin maganar da ta yi da kuma mika nata hannun ta amshi wayar hakan ba sai ya janye nasa hannun ba shi ne ta kalli hannu nasa, ba ta da zaɓin da ya wuce ta amshi wayar. Sai ta mika nata hannu za ta amsa tsabar ta tsargu da shi ashe ba ta amshi wayar ba har shi kuma ya sakar mata ita , ai kuwa waya ta faɗi ƙasa kuma suka duka ƙasa a tare su ɗauko, nan kuma sai da hannuwansu suka haɗu a waje guda. Wani schok suka ji lokaci guda kuma suka kara sakin wayar. Lalla tashi tsaye ta yi saboda abin da ta ji yana barazanar tarwatsa mata farincikinta, sai shi ni ya mika hannunsa ya ɗaukota, sai dai yana danna ta ya ga screen ɗinta ya fashe, madubinta ya mutu ba a ganin komai sai haske.
"Ya Salam!" Shi ne kalmar da Ibrahim ya furta, sai suka kalle sa gabadaya suna son jin abin da ya sanya shi faɗin haka, ganin bai ce komai ba sai Farida ta yi magana tana tambayarsa abin da yake faruwa ta hanyar cewa
"Yayana lafiya dai ko?"
"Da sauƙi dai ƙanwata, na yi mata ɓarna wallahi." In ji Ibrahim ya ida maganar a sanyaye. Sai Farida ta yi saurin isa wajensa tana cewa
"Ta me kuma?" Bai iya ba ta amsa ba sai wayar ya mika mata ita ma sai ta furta
"Ya salam! Ba dai faɗuwar da ta yi ba yanzu?"
"Ita fa wallahi sister, abun kuma ya bani mamaki ganin wajen ba ƙasa sosai, watakila wani dutse ne ya buge ta." Cewar Ibrahim ya ida maganar hankalinsa yana ga Lalla don yana son ya ga yanayinta na ɓata mata waya da ya yi, duk da wayar ƙarama ce ba Android ba amma dai mai kyau ce tunda irin masu gidan layi uku ce, amma ya ji babu daɗi a ransa na lalacewar wayar kuma a daidai wannan lokacin da ya kawo mata wayar kuma yake son ta zama mallakinsa a lokacin ne kuma ya yi mata ɓarna. Sai ya karkata hankalinsa ga Hafsar yana cewa
"Ki yi haƙuri don Allah, ba a son raina hakan ta faru ba."
"Ba fa kai ne ka lalata wayar ba, ga hannuna ne ta faɗi." In ji Lalla tana mika wa Farida hannu alamar ta ba ta wayar. Sai Farida ta ce
"A a yayata ba za a yi hakan ba, bari dai mu koma da ita in mun gyara ko ni zan mayar maki da ita."
"Wallahi na gode , babu damuwa zan gyara da kaina " Lalla ta ce tana mayar da kallonta ga Fati saboda duk an cika motoci da mutane kuma ga su nan ba su tafi ba.
"Ku shiga mota mu tafi don na ga ƙawar amarya duk ta tsargu." In ji Ibrahim yana komawa ɓangaren dreba don kar ma su yi masa musu saboda ya ga ƴan ɗaukar amarya sun fara tafiya in kuma aka yi masu musu za su ɓata lokaci. Da kallo Hafsat ta bi shi tana mamakin ƙarfi halin irin na wannan mutumin da suka fara gani yau har yake zancen zai kai su rakkiyar amarya. Gaskiya ita dai na da ita ba don ba ta ji za ta iya shiga motar wani namiji ba ta Nura ba, ita ina ma za ta iya wannan ɗanyan aikin na tafiya rakkiyar amarya tare da wani namiji kuma cikin mota guda. Sai dai me? Ga mamakinta gani ta yi Farida ta kewaya ɗaya ɓangaren tana shiga bayan motar ita kuma Fati tana shirin shiga motar haɗe da cewa
"Besty shiga gaba mu tafi kar su ɓace mana."
"Kin san me kike cewa kuwa? Ni ɗin ce zan shiga gaban wata mota wacce ba ta Nura ba? Kuma wani namijin ne zai tuƙa ni? Lallai mafarki ne kike yi besty tun wuri ma ki fito daga motar nan kafin in kira yaya in faɗa masa." Lalla ta yi maganar ƙasa-ƙasa yadda babu wanda zai ji ta sai Fati don Farida Ibrahim duk sun shiga cikin motar kuma ba ɓangarenta suke ba, shi ya ba ta damar amayar da abin da yake cikinta.
"Don Allah minti biyu ina zuwa." Cewar Fati tana fita daga motar dukda daman ba ta ida shiga ba Lalla ta yi maganr.
"Me ya sa kike yi haka ne?" In ji Fati
"Me ya sa ba zan yi haka ba?" Lalla ta ba ta amsa.
"Kina so mu ɓata lokacinmu ko? Kina son ki ɓata wa wanda ya taimaka maki rai ko?" Fati ta ce haka tana harararta.
"Minene abun taimako a nan? Don ya kawo min waya? Tun farko sai da na ce masa ya bari zan zo in amsa amma ya ƙi sai da ya zo, kuma shi ne zai cewa mu zo ya kai mu gidan amarya ta ya ya zan yarda da shi lokaci guda? Ki faɗa min ta yaya ganin farko da zan yi wa mutum har in aminta da shi in fita da shi kuma cikin dare ba tare da sanin iyayenmu ba, in fa mai cuta ne? Ko ma ba mai cuta ba ne ba zan iya saɓa alkawarin Nur ba saboda na yi masa alƙawarin kare matarbar soyayyarmu, don haka ke da za ki ci amanar taki soyyayar sai kin dawo ni kin ga tafiyata." Lalla Hafsat ta ce haka ranta a ɗan ɓace ganin yadda lokaci guda Fati ta aminta da su Ibrahim, tana shirin barin wajen sai ta ji an riƙe mata hannu ta baya. Juyowar da za ta yi sai ta ga Farida ce ta riƙe mata hannu ashe ta fito ta yi wa Lalla magana na rashin ƙin shigo motarsu da ba ta yi ba sai ta ji abin da take cewa, ba ta yi mamaki ba ko kaɗan na jin furucin Lalla saboda ta san ba kowacce mace ce ba za ta aminta da wasu mutane waɗanda ba ta taɓa gani ba har ma su ce za su kai ta wani wuri ta yarda da hakan. Sai ta buɗe baki ta ce da Hafsat
"Ki yarda da mu sister da izinin Allah mu ba masu cutar da ku ne, ki shiga bayan motar don Allah, ni zan shiga gaba amaryar Nur."
Sosai Farida take yi wa Lalla kwarjini, ba ta iya yi mata musu ba musamman ma da ta kira ta da amaryar Nura, sai ta ce da ita
"Ki yi haƙuri."
"Babu komai ƴar'uwata ai ba ki yi laifi ba don duniyar ce ta lalace yanzu" in ji Farida, ta yi maganar tana buɗewa Lalla ƙofar mota sai da ta ga ta shiga sannan ta mayar da kallonta ga Fati ta ce mata
"Kar fa ki ga laifinta! Na ga kina hararenta to da gaskiyarta, yanzu dai shiga mota mu tafi."
Murmushi kawai Fati ta yi sannan ta shiga motar, ita kuma sai ta shiga gaban motar kamar jira Ibrahim yake ya tayar da mota ya ba ta wuta. Dayake motocin duk sun tafi sai tambayar Fati ta yi ina ne gidan amaryar ta faɗa masa unguwar Zaria ta biyu ne, tun shi babu wanda ya sake magana sai tsakananin Farida da Ibrahim ne kawai suke hira. Don Lalla ta yi haushin Fati na gayyato Ibrahim da ta yi har ta dalilin haka suka shiga motarsa abin da ba su taɓa aikatawa ba yau sun yi. Ita kuma Fati dukda ta san Lalla da gaskiyarta amma haka ta ji babu daɗi abin da ta yi don ma Allah Ya sa Ibrahim bai ji me ta ce ba, mutumin da ya yi maka hallaci ai bai kamata ka saka masa da zargi ba. A haka suke je gidan amaryar da kwatancen da Fati ta yi masa har suka je can suka yi abin da za su yi sannan kuma ya mayar da su gidajensu don dare ya yi ko da sun koma gidan kawu sai sun dawo gidajensu don ba za su iya bacci a can ba da mutane sosai ƴan biki.
Sosai Ibrahim ya so yi wa Lalla magana amma bai samu damar hakan ba saboda shawarar da ƙanwarsa ta ba shi a lokacin da suka je gidan amarya bayan sun shiga gidan ita kuma ta tsaya wajen yayanta, a nan ta ba shi shawarar sai ya yi da gaske in har yana so ta saurare sa kuma yanzu ba lokacin da zai yi mata magana ba ne don a fusace take na yi mata dole da aka yi ta shiga motarsa, sai kuwa ya yi amfani da shawararta bai ce mata komai ba har suka rabu suka yi sallama. Tun da dai ya ga gidajensu ai babu matsala zai dawo jibi.
Kowaccensu bayan ta shiga gida sai da ta yi wanka sannan ta kwanta cike da gajiya.A ɓangaren su Ibrahim kuwa bayan ya ajiye su sai da ya biya wata mall saman hanya sannan ya siye wa Farida biscuits da ice cream saboda ya san da wiya in sun koma gida ta samu damar cin abinci, ɗazu zumudin tafiya ya hana ta ci yanzu kuma abincin ya yi sanyi kafin su iso dukda dai yana cikin kula.
Bayan sun iso gida sosai Hajiya Sabira ta yi Farida faɗa na tsanar da take yi wa Samira acewarta Farida ta tsane ta dukda kasancewarta ƴar'uwata ta jini, kuma ta fifita ta a kan bare wai Ibrahim ne bare, shi da suke uba guda amma ake kiransa da bare saboda cousin sistee ɗinsa,ba ta ce mata komai ba sai haƙuri da take ba ta na ba haka ba ne amma ina sai ɓaɓatu take yi saboda abun ya zame mata biyu hada kuma ƙin saurarenta da Alhaji Abubakar bai yi ba a kan maganar auren Ibrahim da Samira da take son yi masa, duk shi ne ya ƙara tunzura ta ta huce haushin hakan a kan Farida, don ita ta fi ma ganin laifinta saboda yana jin maganarta da ta kai masa tayin Samira da tuni ya amince mata amma shi ne take yin shiru. Ya zama dole ta san abun yi kar a zo ma daga hira suke yanzu.Littafin kuɗi ne a kan nera 200 kacal, tuntuɓi wannan lambar +22784506476 domin ƙarin bayani
Mutanen Niger kuma 300fcfa chap chap moov airtel orange ko sahelcom.
Real Nana Aisha 🥰
