Page 22

2 1 0
                                    

Hankalin Nura in ya yi dubu to ya tashi a lokacin, sama da ƙasa ya neme ta ya rasa don lokacin break ne akwai mutane sosai, ita kuma ta shige cikinsu. Duk inda yake tsammanin zai ganta ya je amma a banza, ga kuma Fati ta tafi gida don ita ƙarfe sha ɗaya suka tashi yau ba ta tsaya jiransu ba ta wuce abinta ita da ƴar ajinsu.
Nura ya rasa gane me ya sa ta yi masa haka? Amma ya fi ɗaura laifi ga rashin zuwansa rakkiyarta inda suka yi za su tafi tare in sun fito hutu sai dai wancan sudar ta hana sa tafiya wajen ƙanwarsa a cewarsa ƴar ajinsu da ta tsayar da shi.

Ko da ya dawo daga nemanta har an koma aji, malaminsu ya shiga har ya sare ga shiga lakca ɗin don ya san halin sa bai cika bari a shiga aji bayan ya shiga ba, sai dai ga mamakinsa yana neman izinin shiga ya yi masa izini haɗe da ba shi kashedi, saboda ganin yana da kokoro shiyasa ma ya sanyo shi. Sai dai kaf tunaninsa ya tafi kan ƙanwarsa kuma ƙawarsa. Hatta malaminsu sai da abin ya ba shi mamaki don ya san yana yawan participate in yana darasi amma ko rubutawar ma da kyar yake yin ta balle ma ya daga hannu, abin da kullum in ana darasinsa tare da shi malamin yake darasi sai dai yau abun ya sha bamban da na kullum. Har aka tashi daga makaranta yana tunanin Hafsat kar a zo ba ta lafiya ta tafi gida ba ta faɗa masa ba.

A ɓangaren Lalla kuwa tana ganinsa ya tahi wajenta sai ta yi saurin ɓoyewa bayan aji inda ta ga ƴan'mata da yawa suna zaune suna cin abinci, kuma har wajen ya taho amma bai kula da ita ba saboda bai tsammanin za ta zauna cikin su don ba su yi kama da ajinsu ba shi yasa don ya fara gane wasu don yana yawan zuwa har ya fara gane fuskokin wasu. Sai kawai ya yi gaba zuwa wajen danan nan ma kuma bai ganta ba. Duk da tana son ganin nasa amma abin da take ji a ranta na yadda ta gansa tare da wata suna hira hada darita sai ya hana ta yi masa magana shi ya sa ita ma ta share sa duk yadda take ganin shige da ficenwa har zuwa lokacin da suka shiga aji,ita ma dai tunanin ne ta yi a ajinsu amma ita da sauki da Nura don ya fi ta shiga damuwa.

Tun ƙarfe sha biyu da rabi aka tashe su amma sai da ta tsaya jiran Nura har zuwa ƙarfe ɗaya da rabi lokacin tashinsu, kamar kullum yadda suka saba tafiya bayan an tashi daga makaranta.

💝💞💝💞💝

Yana fitowa daga cikin ajinsu ya ganta zaune tana zaman jiransa saman wani banci da yake kofar ajinsu. Hannunta rike da wayarta tana game yi ta yi kamar ba ta gansa ba don ta ga yarinyar ɗazu tana fitowa daga aji kuma, sai ya iske ta wajen da take zaune yana kallonta kafin ya fara magana yana cewa
"Ƙanwata ina kika shiga duk kin tayar min da hankali?"

"Ni ma ai ka tayar min da hankali ƙanena." Cewar Lalla tana tashi tsaye daga zaunen da take.

"Na fa ganki lokacin da nake tsaye tare da ƴan ajinmu amma ko da na juyo sai kika ɓace ɓat. Na neme ki sama da ƙasa ban gan ki ba" In ji Nura ya yi maganar a sanyaye yana kallonta da nazarinta.

Yau ɗaya ta samu kanta da yi masa ƙarya don ba ta san me za ta ce masa game da ɓoye masa da ta yi ɗazu ba, ba ta san me za ta ce masa dalilinta na yin hakan ba, sai kawai ta yi masa ƙarya abin da ba ta taɓa yi masa ba tun da suke da shi, iya wiya tana faɗa masa gaskiya infact ba sa ɓoyewa juna sirri ma amma yau tana jin nauyin ta ce masa don ta gansa da wata ne ta ɓoye duk da sun yi da shi za su fita, ba za ta iya ba gaskiya gara kawai ta ɓoye masa ɗin.

"La ba ni ka gani ba ƙanena! Ana fita break na tafi siyen awara kuma na je ajinku ban iske ka ba ga shi kuma akwai layi sosai a wajen mai suyar awarar." Ta samu kanta da cewa haka. Bai yi mata musu ba duk da bai wani yarda ba saboda ba ta cika fita ba ita ɗaya ai ko da ta salula ne tana iya kiransa,don kar ya karyata sai kawai ya kawar da tunanin can a ransa sannan ya ce

LALLA HAFSATOù les histoires vivent. Découvrez maintenant