"Babu komai autata! Ciwon kai ne yake ɗan damu na." Cewar Hajiya Amina.
"Ta ya za ki cewa babu komai mama? Ga fuskarki nan ta bayyana damuwar da kike ciki ƙarara, don Allah mama ki faɗa min me yake damunki ko wani abu ne ya faru?" Lalla Hafsat ta yi maganar cikin tashin hankali don yadda ta ga fuskar mahaifiyarta ta san akwai abin da yake damunta wanda yanzu nz ya same ta bayan fitarta wajen Nura, saboda ba haka ta fita ta bar ta ba, sai ta zauna kusa ga mama domin jin ƙarin bayani daga gare ta. Kallonta mama ta yi sosai kafin ta nemo jarumtar magana ta hanyar cewa
"Miko min paracétamol in sha, ciwon kai ne kawai ba wani abu ba ne, kar ki damu kin ji autata zan samu sauƙi in sha Allah?" Ta ida maganar ta kallonta a tsanake.
Ba ta yi musu ba ta tashi ta ɗauko wa mama maganin haɗe da miko mata ruwa marar sanyi, bayan ta sha maganin ta mayar da ruwan haɗe zaunawa tare da ita har sai da ta yi bacci sannan ta koma ɗakinta tana yi mata addu'ar samun lafiya. Tana zuwa ta iske tarin kira daga Mr Naci haɗe da sakonni kala-kala na soyayya, sako ɗaya ne ya tsaya mata a rai inda ya rubuta sa kamar haka:
_Amaryata, kuma uwar gidana, ina yi maki fatan alƙairi, ki kula min da kanki my future wife__Daga mai ƙaunarki fiye da kowa_
Lallai sai ta koyi rashin mutumci akan mutumin nan, ta ya zai dinga haɗa kansa da ita? Kamar ba ta faɗa masa ba tana da miji ne da zai dinga yi mata zancen amaryarsa? Hada wani cewa mai ƙaunarta fiye da kowa, lallai ma wannan mutumin, in akwai mai ƙaunarta ai bai wuce Nura ba in aka cire iyayenta! Ta gane nufinsa kawai don dai ya ɓata mata rai ne, ko kuma don ta kula sa ne ta hanyar ba shi amsa har ya ƙara ganin damarta ko ya nemi ya yi hira da ita, sai kawai ta share sa, suka fara hirarsu ita da Nura har bacci ya yi awon gaba da ita mai cike da mafarki kala-kala masu daɗi.
💞💘💝💞💘💝💞💘💝
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, yau daɗi gobe wiya, wataran a sha zuma wataran a sha maɗaci, rayuwa kenan! Lalla sam ta rasa gane kan mahaifiyarta kwanan nan, tun ranar da ta ce mata kanta yana ciwo har zuwa yanzu ta kasa gane ta, saboda in har ta yi zaune ita ɗaya to ta fara sabuwar sana'arta kenan wato tunani. Tambayar duniyar nan Hafsat ta yi wa mama amma magana ɗaya ce wato yanayin rayuwar ne da kewarta, saboda za ta koma Niamey neman aiki kuma a can za su zauna tare da mijinta in sun yi aure, wannan dalilin ne ya hana ta sukuni na rashin wani yaro a tare da ita don duk sauran ƴaƴanta ba nan suke da aure ba in aka cire sauran maza da ƴarta babba. In ta tafi za a bar gida daga ita ne sai kishiyarta da masu aikin gida. Wannan dalilin ne ya sanya ta shiga damuwa har ya haifar mata da ciwon kai a cewarta amma dai ba shi ne asalin damuwarta ba ta dai ɓoye mata ne, sai Lalla ta matsa mata su je asibiti amma ta ƙi saboda ciwonta ba na zuwa asibiti ba ne a cewarta damuwa ce da saka abu a rai kawai, kuma za ta warware nan gaba. Ita kaɗai ce ta san abin da yake damunta, ta san da a ce Lallar za ta ji me yake damunta ɗin, da abun sai ya fi haka tayar mata da hankali in ba a ci sa'a ma ba har da kwanciya a asibiti sai ta yi don abun akwai tausayi.
Ganin da Lalla ta yi mama ta ce rabuwa da ita ne ya sanya ta shiga damuwa sai ta ce ta fasa zuwa Niamey ɗin ma saboda farincikinta, za ta cigaba da zama a nan garin har zuwa lokacin da za ta yi aure, kuma auren ma ba za ta zama wani gari ba sai nan Maraɗi saboda kula da mahaifiyarta, wannan maganar da ta yi sosai ta girgiza mama kuma ta ƙara jin wani tausayinta ya linka na da, sai ga mama ta fara sakin jikinta tana karfin hali, don ta san da gasken ne Lalla tana iya ƙin tafiya Niamey ɗin. Sai da Lalla ta ga hankalin mama ya kwanta ta saki ranta sosai sannan ta fara shirin tafiya Niamey nan da wata guda in da rai da lafiya. Da har ta ce wa Nura ba za ta zo ba dayake shi ma har ya tafi can ɗin saboda shi ma zai karasa karatunsa a can na digirgir.
💝💘💞💝💘💞💝💘💞💝💘💞
Duk yadda Samira ta so ta shawo kan Ibrahim abun ya ci tura don ko saurarenta bai yi, ta saci lambarsa a wajen Farida tana kiransa haɗe da yi masa sakonni soyayya kala-kala wanda yake jin haushinsu, bai ga abun birgewa ba ga mace mai bibiyar samari har da tarewa a gidansu. Abubuwan da take yi masa ko kaɗan ba su taɓa birge sa ba sai ma haushinta da yake ji da tsanarta da ta darsu a ransa, a cewarsa ballagazar mace ita ga rashin kamun kai ga bibiyar namiji da take yi kuma ko kaɗan ba ta cikin tsarin matan da yake burin samu ko da a ce bai haɗu da Lalla Hafsat ba wacce yake mafarkin ta zama matarsa, babban taikacinsa shi ne yadda take turo masa hotunanta wanda ba su da kyan gani don wani hoto in ta turo masa shi duk surar jikinta a bayyane yake, ita a ganinta shi ne zai janyo hankalinsa gare ta har ya fara sonta, abin da ba ta sani sai tsana ma ta janyo wa kanta gare sa, ya yi magana har ya gaji ta daina turo su amma ta ƙi ga kuma voice da take turo masa tana kashe murya, ranar da abun ya ishe sa ya yi mata gargaɗi mai tsanani da munanan kalamai wanda ta ji haushinsu kwarai da gaske. Sai ta ci alwashin babu abin da zai hana ta cigaba da yin abin da take yi masa, ai kuwa ba ta fasa turo masa ba saboda ta ji haushin gargadin da ya yi mata don har zaginta sai da ya yi saboda ransa ya yi mugun ɓaci ran soji ya ɓace ai babu lafiya, shi yasa ta cigaba da abin da take yi don wanda take turo masa na yanzu sun fi na da muni saboda wasu hotunan da kananan kaya ne take turo su ɗin, babu arziki ya kira Farida da gaggawa ya ba ta labarin abin da ya faru don ya rasa ma abin da zai yi mata saboda kansa ya cushe, ransa ya yi mumunan ɓaci, damuwa ta bayyana ƙarara a fuskarsa, da a ce ita ɗin jininsa ce wato ƴar'uwarsa ce wajen uba ko uwa da ya yi mata ɗan banzan duka wanda sai ta yi nadamar aikata masa hakan, amma babu damar hakan yin hakan don zai iya ja wa kansa wani abu wajen uwar rikonsa har abun ya shafi mahaifinsa.
Bayan Farida ta gama sauraren bayaninsa, sai ta ba shi shawarar ya yi blocking ɗinta kawai, don a ganinta wannan hanyar ce mafita a gare sa in har yana son ya tsira da mutuncinsa don mace ce ita tana iya rinjayarsa har su aikata saɓon Allah. Sosai ranta ya ɓace ga wannan abun kunyar da ta aikata wa yayanta a matsayinta na mace wacce kuma take cousin sister a gareta, ba ta jin kunyar aikata masa hakan ba a matsayinta na wacce take burin zama matarsa, ta dau alkawarin sai ta yi mata magana don wannan abun da take yi ba zai kai ta ko'ina ba sai nadama da na sani, ko da a ce yana da burin aurenta za ta ɓata rawarta da tsalle zai iya cewa ƴar iska ce ita ya fasa auran nata balle ma ko sonta bai yi dole ce za a yi masa.
Bai yi musu ba ya yi blocking ɗinta haɗe karta mata rashin mutumci sosai wanda ta ji haushinsu matuƙa har ta huce haushin a kan Farida don isketa ta yi har cikin ɗakinta ta mare ta, dayake Ibrahim yana falo a lokacin kuma ya ji hayaniyar su yana zuwa dakin Farida ɗin sai ya shigar wa ƙanwarsa sannan ya ce wa Samira ta tattara ta bar masu gida, ta je ta karata gidansu sun gaji da ita ba su buƙatar ta a gidansu tana shirin ɓata masu zumuncinsu gara ta yi gaba tun ba ta haɗa iyayensu faɗa ba. Wannan maganar da Ibrahim ya yi wa Samira sai da ta sanya su shiga tashin hankali sosai a gidan don Hajiya Sabira tana zuwa ba ta tsaya tambayar abin da ya faru ba, ta falla wa Farida biyu a kowanne kuncinta, ta fara faɗa sosai inda take shiga ba ta nan take fita ba, Ibrahim bai iya tsayawa kallon faɗan ba ya fita zuwa falo don in ya tsaya wajen za a iya samun matsala, bayan fitarsa ne sai Samita ta fara yi wa Farida magana cikin kissa da kisisina haɗe da fashewa da kukan munafurci tana cewa
"Farida me ya sa kika tsane ni? Shin kin manta ni ɗin ƴar'uwarki ce? Amma har kike ƙoƙorin raba ni da wanda nake so kuma nake burin zama uwar ƴaƴansa ta dindindin, shin Farida mama ba ta taɓa yi maki bayani ba tun ina ƙarama ta ce min ba ni da wani miji da ya wuce Ibrahim ba? Shin me ya sa ba za ki ji tausayina ba a matsayina na ƴar'uwarki wajen shawo min kan yayanki ya amshi tayin soyayyata ba? Ko ba kya tausayina ne Farida? Shin Farida kin kuwa san zafin so? Ya za ki ji in ke ce kina son mutum yana yi maki wulakanci sannan kuma wanda kike ganin zai shawo kansa amma shi ne yake sake dagula abun? Gida ne dai kuka yi min gori ke da yayanki yau zan bar maku gidanku in koma gidanmu ko da ciwon sonsa zai kashe ni."Farida ta ɗan jin tausayinta don ita ma shaida ce a kan son da take yi wa Ibrahim ɗin, amma gaskiya duk da tana ƴar'uwata ba za ta so ba a ce yayanta wanda tun da ya taso cikin kunci da damuwa haɗe da rashin gata ya auri sangartattar mata kamar ta ba, saboda babu abin da ta iya na mata sai rashin kunya wanda saboda haka ne ma suke samun saɓani a lokunta da yawa. So hauka ne da za ta dinga tura masa hotonta cikin kanana kaya waɗanda suka bayyana surar jikinta? Me ya sa na za ta zo mata ba ta taya yadda za ta sace masa zuciya ba? Ai ita mace ce kuma ta san abin da yayanta yake so ai tana iya isketa ta tambaye ta sai ta faɗa mata wanda ta san sai ya sota sosai, amma ina! Ko rana ɗaya ba ta taɓa ce mata me yayanki yake so ba? Haka ake yin so? So ko hauka? Sai dai kuma maganar da ta yi mata ta ba ta tausayin saboda ta san zafin so ita ma tun da tana yinsa sai ta taka ta isa gare ta za ta fara magana sai Hajiya Sabira ta ce
"Kar in kuskura in ji kin ce mata wani abu , wallahi in har kika yi kuskuren magana sai na ji maki ciwo a gidan nan , wai ke da na tsugunna na haifa kike nuna wa ɗiyar ƴar'uwata da muka fito ciki ɗaya tsana ƙiri-ƙiri saboda wani banza a banza, wallahi sai kin yi nadamar ci mata mutumci da kika yi a nan gidan, hada yi mata gorin gida! Ke kanki kin san ubanki ko kama ƙafar mahaifinta bai yi ba wajen dukiya balle har a haɗa gidanku da nasu gidan. To bari ki ji! Samira babu inda za ta tafi, kuma sai ta auri Ibrahim in ya so ki hau saman bene ki faɗo ki mutu. Aure tsakaninta da shi babu fashi don haihuwarsa ce kawai ban yi ba amma ni na ci kashinsa da fitsarinsa don haka sai wanda na ga dama ya aura, kuma ko baki na yi masa sai ya kama shi don ni ce duniya ta sani a matsayin uwarsa. Shashasha kawai!" Hajiya Sabira ta ida maganar tana jan hannun Samira da take kukan munafurci suka yi waje, kai tsaye falon maigidan ta wuce, dayake yana gida a lokacin kuma yana jin hayaniyar da aka yi bai fito ba don ko ba a faɗa ba ya san dalilin Ibrahim ne ake faɗa ba. Babu sallama ba komai ta fara magana cikin ɗaga murya.LITTAFIN KUƊI NE MAI BUKATAR KARANTAWA ZAI TUNTUƁI WANNAN LAMBAR +22784506576
REAL NANA AISHA
