A wannan daren in har Nura ya ce ya rintsa to tabbas ya sharara ƙarya saboda yadda ya ga dare haka ya ga safiya. Tun bayan gama wayarsu da Fati ya shiga kogin tunanin hirar tasu da ita haɗe da son gano abin da take nufi da zancen.
Ya rasa wa zai faɗa masa damuwarsa ya nema masa magani. Ya rasa yadda zai yi bincike game da matsalarsa. Da a ce zai samu littafin da ake bayyana yadda soyayya take da ya karanta ya samu gamsashiyar amsa game da matsalarsa. Da ace yana da dama da ya tafi 'Cyber café' ya sanya a yi masa binciken soyayya yadda ake ji in ana son mutum. Sai dai ko kusa ba zai iya ba!
Ina zai iya wannan abun! Wayar tasa ma ƙarama ce balle ya hau Google ya bincike duk da ba iyawa ya yi ba saboda ƙarancin amfanin da kafae sada zumunta a wancan lokacin. Amma zai nemi aron waya gobe in sun je makaranta ya bincika ko kuma zai tambayi wasu abokansa waɗanda yake tunanin sun san komai game da soyayya.💞💝💞💝💞💝
Duk yadda ya so samun nutsuwa ya kasa samu don haka sai dai ya yi ta adddu'o'i neman zaɓin Allah don ita ce babbar mafita a gare sa. Sai ya mika wa Allah lamarunsa don abun ganinsa yake kamar al'amara wai shi ne yake son ƙanwarwa, to ta ina zai fara soyayya da ita ma alhali ita ɗin ƙanwarsa ce? Daman haka so yake? Daman so in zai shiga cikin zuciya bai neman shawara? To ya ake yin son ɗin ma? Ko ya ake yin zance in ana soyayya? Lallai da kwai aiki sosai a gabansa in har zargin Fati a kansu ya tabbata na soyayyar da ta ce suna yi da Hafsat.
Idonsa biyu har aka yi kiran assalatu yana yin raka'tul-fajar haɗe da sallar asuba sai ya ɗan jingina jikinsa da kujera yana saman sallaya yana azkhar a nan bacci ya yi awon gaba da shi. Bai kwanta daidai ba saboda daga jingine ne baccin ya kwashe sa wanda ko kaɗan bai kwanta daidai ba balle ya ji daɗin baccin.
💝💞💝💞💝💞💝
Cikin baccin da yake yi wanda ko kaɗan bai jin daɗinsa ya ji muryar mahaifiyarsa tana tashinsa. Wacce abin ya ba ta mamaki da ta ji sa shiru bai fito ba tafiya makaranta. Kusan kullum da shi ake yin sallar asuba a masallaci kuma babu wanda yake tashinsa daga bacci shi da kansa yake tashi ya wuce masallaci kai tsaye. Amma abun mamaki yau har ƙarfe takwas ta kusa bai fito ba ga alamu nan ya nuna ma a gida ya yi sallah.
Ita ta zata ma ba su yin karatu da safe shi yasa ba ta tashe shi ba sai da ta ji sallamar Hafsat gidansu tana nemansa sannan ta shiga ɗakinsa don a zatonta ma har ya shirya tun da ta ga Hafsat a shirye wanda ya tabbatar mata da kwai makaranta yau kenan.Sai dai me? Tana shiga ta iske sa yana bacci saman sallaya. Rass gabanta ya faɗi don abun ya bata mamaki ganin Nura yana bacci a wannan lokacin abin da bai saba ba yi ba, ko da babu makaranta ne ba za ka same sa a wannan lokacin yana bacci ba.
Yana buɗe idonsa ya ci karo da fuskar mahaifiyarsa tana cewa"Me yake damunka Nura?"
Kallon mamaki ya yi mata don bai gane tambayar tata ba. Sai ya yi shiru yana kallonta don wani azababen ciwon kai ya tashi da shi wanda baccin da bai yi ba ne ya haifar masa da shi. Ga kuma an tashe sa a bacci kuma bai ishe sa ba. Mafi yawan lokuta in har yana bacci bai ishe shi ba aka tashe sa da ciwon kai yake farkawa.
"Ba ka ji me na ce ba?" In ji Hassia mahaifiyar Nura wacce take faman kallon Nura tana nazarinsa yadda ya dawo wani kala lokaci guda daga daren jiya zuwa yau da safe."Mama kaina kamar zai fashe." Iya abin da Nura ya ce kenan yana ya zama saman katifa.
"Subahanallah ! Kar dai a ce da shi ka kwana."
Mama ta yi maganar tana zama bakin katifar da Nura ya zauna a kai haɗe da ɗora hannunta saman goshinsa don jin ko yana da masassara.