Je dédie cette page a toi ma maman chérie, Madame Fatima depuis Dakoro. Je t'aime ma maman chérie🥰🥰
Octoba 1999
A wannan lokacin duk wanda yake jamhuriyar Nijar ya san lokacin komawar yara ne makaranta tun daga firamari har zuwa matakin sakandari daga hutun karshen shekara wanda ake bayarwa na wata uku tun daga ƙarshen watan june har zuwa farkon watan octoba. A wannan lokacin ne kuma su Lalla suke shirin shiga aji na ɗaya a makaranta sai ɗoki take yi saboda kayan makaranta da babanta Sulaiman ya siye mata, ta matsu a koma ko ta fara zuwa don kullum sai ta ɗauki kayan tana taɓawa haɗe da tambayar mama Amina ranar komawa makaranta. Sannan kuma duk in Nura ya zo gidansu sai ta nuna masa kayanta na makaranta, wanda shi ma sai da ya tayar da zanga-zanga a gidansu sai da aka siye masa irin kayan makarantar Lalla duk da wanda aka siye masa shekarar da ta gabata bai yi amfani da su ba.
An yi kan daidai makarantar da aka sanya Nura can ne uncle Sulaimain aminin mahaifin Lalla ya sanya ta. Abun ka ga yara babu ruwansu da alhinin mutuwar mahaifinsu shirye-shirye komawa makaranta kawai suke yi duk da dai an yi wata uku da rasuwar a wannan lokacin har ma sun kusa fita daga takaba.
An yi wa Lalla ita da Saratu yayarta kitso mai kyau gashi ya zubo masu har gadon baya saboda sun yi gadon gashi na Fulani iyayensu. Bayan an yi masu kitso kuma an yi masu lalle mai yanki-yanke, ta yi baƙi sosai ya fito a kafafunsu abunka ga farar fata. Sosai suka yi kyau abun su.October, 4th 1999
A ranar litinin ta farkon wannan wata ne wanda ta yi daidai da huɗu da wata, a ranar ne ƴan makaranta suka koma karatu daga hutun karshen shekara, kuma ranar ne ake ɗaukar sabin shiga aji na ɗaya a firamari. Tun safe Amina ta yi wa yaranta wanka ta shirya su kodayake sauran sun iya wanka da kansu saboda duk suna da wayonsu, Lalla ce da ke yarinya don sauran suk sun shiga sakandari saboda tazarar da take tsananinsu da yayannunta don Saratu wacce Lalla take bi wa wannan shekarar ta gama firamari shi kuma Samaila yanzu ya gama JS3, don haka su da kansu suka shirya, ita kuma ta shirya Lalla wacce sai ɗoki take yi fuskarta cike da annuri wanda yake wanzuwa a fuskarta a duk lokacin da ta tuna ita ma za ta fara zuwa makaranta. Tana matuƙar son makaranta sosai in yayannunta sun tafi har ji take yi kamar ta bi su. Bayan an gama shirya ta aka sanya mata kayanta sabi ƴan kanti wanda aka tanadar mata don wannan ranar. Sannan mama Amina ta sanya mata kwalli ga ido, ta fito ras abun ta gwanin kyau, ta ɗora fullar ƴan kantin da aka sanya mata saboda masu fitowa da fulla ne da kuma jaka ƙarama wanda yara suka iya sanya kuɗinsu a ciki.
Bayan an gama yi mata shiri cikin sauri take shirin fita daga gidan zuwa gidansu Nura wanda suka yi da shi za su biyo masa. Sai mama Amina ta hana ta fita ita ɗaya saboda ranar farko dole sai an haɗa da babban mutum wanda ya san kan abun da kuma inda ake kai sabbin shiga. Ranta bai so ba don cewa ta yi ai Nura ya san hanya tare za su tafi amma ko kula ta ba a yi ba har yayannunta suka gama shiriTare da Samaila suka tafi saboda rakkiyarta zuwa makarantarsu, suna fita kememe Hafsat ta ce babu inda za ta tafi matuƙar ba a biya gidansu Nura ba. Samaila kuma yana ba ta baki ta yi haƙuri a kan zuwa warhaka Nura ya tafi saboda ƙarfe takwas har ta gota, amma ina! Ta ƙi yarda da zancen Nura da ya tafi ya barta don ba haka suka yi da shi ba. Saboda tun safe sai da ya shigo gidansu lokacin da za a yi mata wanka. Sai magiya take yi masa a kan su biya gidan tana cewa
"Ai shi ya ce in biyo masa mu tafi tare."
Samaila ya yi mata banza duk da maganar da Saratu take yi masa na zancen Hafsat gaskiya ne amma haka ya share su ya yi kamar bai ji ba don ya matsu ya isa makaranta yana son gwamna ya iso suna makarantar. Ita kuma Hafsat ganin da ta yi an kusa wuce gidan su Nura sai ta fashe da kuka haɗe da saurin ƙwace hannunta daga rikon da ya yi mata tana kwasawa da gudu sai cikin gidan su Nura wanda suka yi kicibus da shi cikin zauren gidansu ya fito ya sha ɗinkinsa na shadda riga da wando dogaye. Lalla ta kalle shi haɗe da cewa
"Nura kayanka sun yi kyau, wa ya siye maka su?"
"Babanmu ya siye min su har da wasu suna can cikin akwatin mamanmu." Cewar Nura suna nufar wajen su Samaila wanda takaicin tsayar da shi da suka yi, ya sanya shi kama hanya ya yi tafiyarsa sai sauri yake yi har ya yi masu nisa. Sai Sarati ce ta ɗan tsaya masu don kar ta tafi ta bar su ba su san hanya ba a cewarta duk da dai Nura bara can ya fara zuwa amma karatun da ko wata bai yi ba ya daina zuwa.
"An sha kyau Nura!" Cewar Saratu tana murmushi.
"Ke ma kun yi kyau ke da Hafsat, amma ita ta fi ki kyau ko Hafsat?" Cewar Nura yana kallon Hafsat.
Kafin Hafsat ta ce wani abu sai Saratu ta ce
"Daman ai na san haka za ka cewa, son kai ne dai ka yi don Hafsat tana ƙawarka."
"Da gaske na fi kyau." In ji Hafsat sannan ta kara da cewa
"Ka san ko Nura?"
"Ai daman na ce kin fi ta kyau, kayanki ma ƴan kanti ne amma ita atanfa ce ta sanya." Nura ya yi maganar yana kama hannu Saratu wacce ta riƙe hannun Hafsat da ɗaya hannun tana mika wa Nura ɗayan hannunta ya riƙe ba tare da ta yi magana ba saboda za su tsallaka titi. Sai bayan sun tsallaka titin ne Saratu ta ce da Nura
"Kai yaro ka ji tsoron Allah! Atanfa ƴar cote d'ivoire ce kuɗinta zai siye wannan kayan na jikinka da na jikin kawarka."
"Wai da gaske ne Hafsat?" Nura ya yi tambayar cike da yarinta. Ita ma Hafsat sai ta ce da shi
"Ni ma ban sani ba, amma in mun koma gida za mu tambayi mama sai a raba gardama."
"Ikon Allah! Nufinku na yi karya kenan! Ai na ga wanda zai dawo da ku tun da kun haɗe min kai." In ji Saratu ta yi maganar tana ɗaure fuska kamar gaske ta yi fushi da su ɗin, ita kuma don ta gwada su ne ko za su ce kayanta suna da kyau. Sai dai ga mamakinta sai ta ji Hafsat tana cewa
"Ai na san hanya, Nura ma ya san hanya.""To ai shikenan, sai ku dawo da kanku."
In ji Saratu. Daga nan ba ta ƙara magana ba sai ta bar Nura da Hafsat suna zancensu don ba za ta iya biye wa shirmen zancensu ba. Ita dai tana saurarensu ba tare da ta yi magana ba. Bayan sun iso makarantar su Hafsat ta rakka su har wajen da aka tanadar wa ƴan aji na ɗaya sannan ta wuce tasu makarantar.Bayan tafiya Saratu sai suka fara wassaninsu na yara tare da yara ƴan aji na ɗaya kamar su. Sannan suka tafi wajen masu talla suka siye abin da suke so da kuɗin da aka ba su daga gida na makaranta. Sai suka dawo wajen malamai sannan aka fara kiran sunaye kowa yana amsawa sannan a nuna wa kowa ajinsu. Nura yana CI A ita kuma Hafsat tana CI C. Kasancewar yara ne su ba su fahimci da ba ajinsu guda ba duk da sai da aka kira ƴan A nan Nura yake, sannan aka kira ƴan B nan babu sunan Hafsat, sannan sai a C ne ta ji sunanta. Duk babu abin da suka fahimta da hakan. Haka suka ci gaba da zuwa makaranta har zuwa ranar da aka fara shiga class, kuma kullum in sun je san an yi kiran sunaye amma ba su fahimci komai ba dangane da ba ajinsu guda ba.
Ranar da aka fara kama karatu bayan sun iso ne sai aka nuna wa kowa ajinsu saboda a ranar bayan an gama kiran sunaye sai aka ce kowannensu ya bi Malamarsu. Duk babu wanda ya kula da Hafsat ajin su Nura ta shiga. Sai washegari da suka zo aka yi kiran sunaye ne bayan an gama aka tambayi wanda bai ji sunansa ba ya yi magana, Hafsat ta ɗaga hannu ko da aka duba babu sunanta sai aka ce ai ba nan ne ajinsu ba. sai Malamarsu ta kama hannunta har zuwa ajin da aka kaita. Suna shiga da ita, dubawar da za ta yi bayanta sai ta ga Nura shi ma ya biyo bayansu. Duk yadda ta so ya biyo ta zuwa ajinsu amma ya ƙi binta shi wajen Hafsah zai tafi ba zai tsaya can ba. Dole shi sai dai aji guda shi da ita. Duk yadda aka so a fahimtar da su ba ajinsu guda ƙi suka yi har aka faɗa wa principal ta makarantar.
