Bayan kwana biyu sosai jikin Nura ya tsananta saboda ya daina bacci, ya daina cin abinci ko wanka bai yi. Ya kulla alaƙa da tunani don ba shi da wani aboki sama da shi a halin yanzu. Kuma abun ban tausayi shi ne daga ya fara tunanin Hafsat sai kuka kamar ƙaramin yaro ya gaza mantawa da cin amanar da Hafsat ta yi masa a cewarsa, ta cuce shi ta zalunce shi ta koya masa son shi sannan ta tafi ta bar shi cikin mayiyacin hali, bai taɓa tunanin za ta yi masa haka ba sai a wannan lokacin da ya ji labarin kawo kuɗin aurenta, ba zai taɓa yafe mata cin amanar da ta yi masa ba. Duk da ya ji an ce dole ne aka yi mata amma ai da ba ta yi kuskuren nuna wa saurayin gidansu ba ai da ba zai nemi auranta ba. Ta kira sa ya fi a kirga duk ita ma tana can cikin wani hali amma tunanin Nura kawai take yi shi yasa ta sha masa kai da kira da sakonni, amma ko kula ta bai yi ba duk da yana buƙatar ta a kusa da shi a wannan halin amma haka ya share ta saboda tunanin yadda suka fara gudanar da rayuwarsu yake yi har kawo yanzu da yake cikin wannan halin. waɗanda suke ɗaki guda da shi sun yi ban baki sun yi ban haƙuri amma a banza kamar zuga shi suke yi, ga shi ba gida yake ba balle ya samu wanda zai rarrashe sa,daman ita ce in yana cikin wani hali take rarrashinsa amma yanzu ita ce ɗin ta ɓata masa rayuwa da datse duk wani burinkansu da suka tsara.
Tuna baya
Alhaji Samaila mai gida a wurin Hajiya Hafsat haifaffan garin Toroɗi wani ƙauye da yake gaban Niamey, fulani ne na asali. A can aka haife su har suka yi auren su na zumunci na so da ƙauna. Dayake Alhaji Samaila ya yi makatar boko bayan ya gama digiri ɗinsa na farko ne aka yi auren. Ana ɗaura aurensa da Hafsat sai suka dawo babban birni da zama yana koyarwa a sakandari, duk baya suna zuwa ƙauye wajen hutu ganin daginsu.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya cikin so da ƙaunar juna, har suka yi shekarar biyar da aure amma ko ɓatan wata Hafsat ba taɓa yi ba, ba su wani damu ba tun da sun san haihuwa nufin Allah ne in suna da rabon su haihu za su haihu ɗin. A lokacin kuma Samaila yana da dukiya saboda yana ɗaukar albashi mai tsoka har ya samu ya gina gidansa a unguwar Bukkoki, suka tare a can sai a lokacin ne Hafsat ta samu cikin farko, sun yi murna sosai kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha saboda farinciki. Haka suka cigaba da rainon cikin su har Allah Ya sauke ta lafiya ta haifi ƴarta mace kyakyawa son kowa ƙin wanda ya rasa. Ranar suna yarinya ta ci sunan Maryam. Maryam tana da shekara biyu ta samu ciki ranar suna yaro ya ci sunan Lawali. ko shekara Lawali bai yi ba ta sake samun wani cikin na ƴan biyu wanda ya ba ta wahala sosai tun tana da cikin take shan wahala har ta haihu ƴan biyu mace da namiji Hasan da Usaina. Bayan haihuwar ƴan biyu ne Samaila ya dawo garin Maraɗi da aiki, yana zaune a unguwar Bagalam, sosai suke zumunci da mutanen unguwar kasancewarsa mutum mai matukar kirki daga shi har matarsa Hafsat mutanen ƙwarai ne. A Lokacin da ya baro garin Niamey sai ya bar wa danginsa gidansa na Niamey saboda halin watarana.
Bayan haihuwar ƴan biyu kuma sai da ta yi shekara biyar sannan ta haifi mace mai suna Sa'adatu, a lokacin Lawali yana aji biyu a firamari, ana shirin sanya ƴan biyu a makaranta su kuma. Sa'adatu tana da shekara uku aka haifi Sani, daga ita aka haifi Ibrahim sai auta Hauwa'u, auta tana da shekara biyu suka tafi Samaila ya tafi hajji.
Sun yi zama garuruwa amma ya fi zama Maraɗi saboda nan ne ya daɗe sosai don duka ƴaƴansa nan suka yi karatunsu, saboda daɗin zama garin ko tranfa aka yi masa daga garin bai zuwa tare da Hafsat, sai dai ya tafi shi kaɗai ya bar su a gida Maraɗi saboda bai san yawo tare da iyali sosai musamman aikin gwamnati da sai ana tsaka da karatu ake yi wa mutum trasfa kuma karatun yara duk ya tafarfare.
Alhaji Samaila yana da babban amini wanda suka yi zaman mutumci da shi a nan garin Maraɗi wanda zumuncinsu ya ɗore har ga ƴaƴansu. A tare suka yi karatu, sai kuma sai Allah Ya kawo Alhaji Samaila garin su Tanko dayake shi ɗan asalin Maraɗi ne. In mutum bai sani ba zai zata dangin juna ne, sai dai ba su haɗa jini ba sai ƴan'uwantaka ta musulunci saboda shi Alhaji Samaila Fulani ne shi kuma Tanko Bakatsine ne, sun zama tamkar ƴan'uwan juna don hatta ƴaƴansu suna mutumci da juna.
Yuni 1975
Da gudu Lawali ya shigo gida yana murna haɗe da kiran mahaifiyarsa Hafsat yana cewa
"Inna! Inna! Inna!"
Cikin sauri ta Hafsat ta fito daga ɗaki tana cewa
"Wannan kiran haka, me muka sa..." Bai ba ta damar ƙarasa maganar ba ya ce da ita
"Inna na ci jarabawata yanzu Sulaiman yake faɗa min shi ma ya samu."
Cikin farinciki da jin daɗi Hafsat take maimata kalmar
"AlhamduLillah AlhamduLillah AlhamduLillah" har sau uku sannan ta ce
"Na taya ka murna, Allah Ya sanya alƙairi, Ya sa a ci amfaninsa."
"Amin amin inna, bari mu tafi ni da Sulamain mu duba, shi ma baba ne yake faɗa masa mun samu mu duka." In ji Lawali cikin murna bakinsa ya kasa rufuwa tsabar farinciki, saboda jarabawar da suka samu ta shiga jami'a.
"Allah Ya kiyaye hanya, kar ku jima ƴaƴan albarka." Cewar Hafsat tana kallon ɗanta yadda bakinsa ya ƙi rufuwa tsabar farinciki da yake ciki.
Da "amin" ya amsa sannan ya fita waje da sauri sai gidan su Sulaiman, nan ma ya iske su suna yi ta murnar samun jarabawarsu. Ba su ɓata lokaci ba suka fita sai makarantarsu *Lycee Ɗan Baskore* wacce a lokacin tana unguwar bagalam kafin ta dawo zaria da zama. Bayan sun je sun ga sunayensu sannan suka yi ta murna da farinciki. Suka fara gyaran takardun karatunsu na matakin gaba da sakandari. Bayan wani lokaci suka aika takardunsu can Niamey wajen yayar Lawali Maryam dayake ta yi aure a can take da zama.
Na san da yawa sun shiga kwakwanton wannan labarin, ku biyo ni da sannu zan warware maku shi dalla-dalla
