Murmushi Hafsat ta yi tana bin mama da kallo a zuci ta raya 'mamata kenan! Tana son farincikina'. Sai ta tashi tana sanya kayanta da ta gama linkewa cikin akwatinta, ko kafin ta gama ta ji ƙarar wayarta ko ba a faɗa ba ta san Nura ne don kiɗan da ta sanya masa daban ne da na kowa, shi da Fatima da mamarta duk ta bambata kiran wayarsu da na kowa. Sai da ta kusa tsinkewa sannan ta ɗaga cikin faɗan wasa wanda suka riga da sabawa da shi take cewa
"Wato don na ce maka babu inda zan tafi shi ne ka kai ƙara ta wajen ma ko?"'Lallata rigima' Nura ya raya a zuci sannan ya ce da ita
"Shi auta duk inda yake sai ya nuna halinsa!""Ba fa za ka min wayo ba yaro ehee" In ji Hafsat tana hayewa saman gado saboda a zaune take don ta san in suna waya da Nura suna jimawa suna hira musamman yanzu da ta san akwai labari na makaranta da za su yi da shi wanda ya kamata ace sun yi kafin zuwan ranar komawa.
Sai Nura ya ce
"Lallata me ya sa kika raina ni? Ni fa yayanki amma kike ce min ƙanenki""Kai fa Nurana son girma ne da kai, yaushe ne ka cika shekara sha biyu?"
In ji Hafsat cikin tsokana tana sakin dariyar ƙeta don daman duk ia ya ce mata yarinya haka take ce masa. Sai ta ji ya ce mata
" Ke kuma watan gobe kike cika shekara sittin ko ƴar tsohuwa mai cin goro?"
Ya yi maganar yana dariya shi ma don ya san ya takulo wa kansa faɗa saboda ba ta son ana ce mata tsohuwa faɗa take yi kuma in ya ce mata yarinya ta ga laifinsa don ta fi son a kira ta da auta fiye da wani suna.
Wannan maganar da ya yi mata na kiranta da tsohuwa sa tuno da abin da mama ta ce mata yanzu na kiranta da kakarsa Ladi. Sai ta kyalkyale da dariya wacce ta ba wa Nura mamaki don shi zatonsa fushi za ta yi sai ta yi dariya amma ya san watakila da biyu wannan dariyar tata. Sai ya ji tana cewa"Ka san me nake yi wa dariya?" Kamar tana gabansa sai ya gyada kai don shi dariyar tata mamaki ta ba shi saboda ya san wata tsokanar ce za ta yi masa. Sai da ta sake magana ne sannan ta ce masa
"Yanzu da na ce maka yaro a gaban mama har na ce mata na girme ka, sai ce min ta yi sannu Hajiya Ladi "
Shi ma murmushin ya yi wanda ya ɗan bayar da sauti sannan ya ce
"Ai mama ta san gaskiya yarinya, shekara biyu ba kwana biyu ne ba.""To ai shikenan yaya Nurana! Yanzu dai ya labari?"
Cewar Hafsat
"Labari sai an ganku masu shirye-shirye komawa makaranta" Cewar Nura.
"Kai ba shiri ne? Amma ai na ga har aski ka yi na komawa." In ji Hafsat
"Sai na yi kitso da lalle kuma" Nura ya ce haka cikin tsokana don jin abin da za ta cewa, sai ta ce masa
"Haka ne fa! Yanzu fa ya kamata mu je siyen jakar makaranta don ka ga jibi ne komawa kuma ba mu siye ba."
"Okay ki yi wa Fati magana sai mu tafi gobe in sha Allah."
"Okay Allah Ya kai mu." Ta amsa da amin sannan suka ɗan taɓa hira daga bisani suka yi sallama.
Washegari suka je ƴar kasuwa tsohuwa suka siye jakar makaranta ta goyo sannan suka siye abubuwan buƙata na kowanne ɗan makaranta.
Washegari suka koma makatanta suna addu'ar Allah Ya sa a haɗe su aji guda don shi ne burinsu. Sai dai ba su samu aji guda ba kuma babu yadda suka iya haka suka hakura don babu yadda za su yi.
Haka suka ci gaba da zuwa makaranta su uku a tare,duk da ba ajinsu guda ba amma tare suke komawa gida. Wani lokacin Fati in sun tashi karfe goma su kuma su Hafsat sai ƙarfe ɗaya,kuma in ta samu mai kai ta gida cikin ƙawayensu masu mashin hayewa take yi don ta san Hafsat tana tare da Nura.
Wannan lokacin sun fara girma sun jima da faɗa wa a soyayyar junansu sai ba su taɓa fahimtar haka ba. Hatta ƴan makarantarsu suk fahimci hakan don ƴan ajin su Lalla sun sha ce mata Nura saurayinta ne sai dai ta ce ba haka ne ba, ita ɗan'uwanta ne kuma abokinta ne. Mutane sai dai su ce ta raina masu hankali ne ko kuma ta ɓoye masu wasu kuma sai dai su ci in ta yi wari sa ji. Murmushi kawai take yi, ba ta cewa komai don ko da ta ce ba yarda ba za su yi wani lokacin har rantsuwa take yi amma duk a banza don ita ba ta san minene so ba.
Shi ma Nura a nasa ɓangaren haka take don haka wasu ƴan ajinsu suke ce masa don kullum suna ganin yadda suke yawo tare. Kuma abin da zai birge mutum game da su shi ne yadda suke da kamun kai , sai dai a gansu tare suna tafiya amma ba su aikata wani abu na assha.
Wannan dalilin ne ma ya sa mutane suke yi masu kallon masoya wanda in aka cewa Nura haka bai wani yarda don shi bai san so ba. Amsa ɗaya yake bayarwa kamar wacce Hafsat take badawa wato ƙanwarsa ce ita kuma ƴar'uwarsa ce.Haka rayuwa ta cigaba da tafiya suna karatunsu suna fahimtar abin da aka yi masu, sannan in sun koma gida suna bita don ƙara fahimtar abin da aka koyar da su.
💞💝💞💝💞💝
Tun da Hafsat take ba ta taɓa jin ɓacin rai irin na yau ba, ba ta taɓa jin haushin Nura irin na yau ba. Ba ta taɓa tsanar wata irin na yau ba, wani irin bugu kirjinta yake yi mata kamar zuciyarta za ta fito daga kirjinta ta dire ta tarwatsa. Wani abu ne take ji wanda ba ta taɓa jin irinsa ba , wani yanayi ne ta shiga wanda ba ta san na miye ba sakamakon idanuwanta da suka yi tozali da Nura yana magana da wata yarinya ƴar ajinsu har yana mata dariya. Wacce yarinyar kullum take son hulɗa da shi saboda ganin da ta yi yana da fahimta shi ya sa take son kulla alaƙa da shi don sosai wanda yake da ilmi yake birge ta. Don ita ma tana son karatu sosai. Ba ta taɓa samun damar yi wa Nura magana ba sai yau don kullum suna fitowa daga aji yake fecewa ko ajin su Fati ko na Lalla don sun fi yawan zama a can. Yau kuma malaminsu ya sake su da wuri ne don ya ba su sakamakonsu na jarabawar da ya yi masu ne a maths ya ci 19,75/20 shi ne tun a aji yarinyar take son yi masa magana don ita har ga Allah tana son koyon maths saboda tana da ilmi amma wajen maths an bar ta a baya. Wannan dalilin ya sanya ta malaminsu yana sakin su da wuri cikin saurin har tana shirin bangaje wani don ta yi saurin fita wajen Nura. Tana zuwa ta iske suna magana da wasu mazan suna maganar makin da ya ci. Ita ma sai ta yi wa Nura magana tana kiransa da Thalès murmushi ya yi mata don bai san me zai ce mata ba. Sai ta ƙara yi masa wata magana wacce ta sanya shi dariya.
Wannan dariyar da Hafsat ta gani ita ce ta hadassa mata faɗuwar gaba wacce ba ta taɓa sanin tana da ita ba, kuma ko a yanka ta ba za ta iya cewa ga abin da take ji game da abin da ta gani ba. Wani haushi da taikaci ne suka lulluɓe ta don gani take yi yarinyar ce ta tsayar da Nura don sun yi da shi za su je ƙofar makaranta siyen wani abu kuma ajinsu ne hanyar fita daga makarantarsu don haka shi zai biyo mata. Tana fitowa ba ta gansa a ƙofar ajinsu ba sai ta taho nasu aji wanda tun daga nesa idanuwanta suka yi tozali da Nura da wata. Babu mamaki tsayar da ita ne da ya yi ya haddasa mata faɗuwar gaba amma duk da haka ta ji haushi don saurin barin wajen ta yi da sauri don kar ma su ganta sai dai kash! Yarinyar ya ganta sai ta ce da Nura
"Ga Jerry ɗinka nan tafe fa"
Ɗago kan da zai yi sai ya tsinkaye ta tana komawa ajinsu, kiranta ya yi amma ta yo masa banza sai ma sauri da ta ƙara yi ta shiga ajinsu.
