Page 12

3 0 0
                                    


A ɓangaren Ibrahim kuwa ikon Alllah kawai ya kai shi gida saboda mugun gudun da ya tsalala saman hanya. Ya ji zafin maganganun Lalla kawai dai ya ɓoye ne a gabanta saboda kar ta raina sa tunda ta ga kasarwarsa amma da a ce ba jarumi ne shi ba babu abin da zai hana shi kuka da hawaye don maganganun sun shige sa sosai, babu abin da yake ɓata masa rai ma kamar zancen Nura in tana cewa shi ne rayuwarta, da a ce garin nan da ya nuna mata kuskurenta na kiran Nura da rayuwarta don sai ya rama abubuwan da ta yi masa,sai dai kawai ya share ta tun da ba garin yake ba kuma yana son ta zama uwar gidansa mata a garesa.
Wani mahaukacin horn Ibrahim ya yi da ya iso gidansu don sosai ransa yake a ɓace, zuciyarsa a cunkushe. Mai gadi cikin sauri ya leko don ya san ga dukkan alamu ba daga gidansu ba ne mai yin wannan uban horn ɗin,saboda ba su da mai yi masu wanna kalar oda a gida daman daga babansu sai Ibrahim su ne masu mota a gidan kuma ba haka suke yi ba, sai dai ga mamakin mai gadi sai ya gani ƴanlaɓai Ibrahim da kansa ne, ai da sauri ya koma cikin gidan yana wangale masa kofar don ya san ba lafiya ba tunda bai saba hakan ba.
Da sauri ya cilla hancin motar a ciki harabar gidan , sai da ya seta kansa sanna ya fito daga motar yana nufa kai tsaye ɓangarensa. Kamar daga sama ya ji muryar Farida tana cewa
"Big Bro!" ko kaɗan bai son damuwa a wannan yanayi da yake ciki, yana bukatar keɓancewa shi kaɗai saboda halin da yake ciki. kamar ya shareta sai dai bai zai taɓa iya share farincikinsa ba. Baayan mahaifinsa bai jin akwai mai wani matsayi a gare sa kamar Farida, shi ya sa ba zai wulankatata ba don haka sai ya tsaya tafiya sannu-sannu har ta ƙaraso gare sa.

Kallo ɗaya ta yi masa ta gane yana cikin damuwa, daman ta san za a rina tun daga yadda ya shigo cikin gida, kuma ta ji yadda yake buga uban horn a ƙofar gida, ta zata ma wani ya zo gidan kamar yadda mai gadi ya yi wannan zaton a ransa, shi ya sa ta leko ganin ko wanene sai kuma ta ga yayanta abun alfaharinta ne ya shigo, ta san yana cikin damuwa saboda sanin daga inda ya fito don ya shaida mata kafin ya tafi gidan su Lalla, kuma ba makawa ta ɓato masa rai ne saboda damuwar da take tattare da shi don ta karance tsaf, daman son maso wani sai hakuri da kai zuciya nesa musamman irin soyayyar Nura da Lalla don suna da labarin komai sun samu labarin a wajen wata da suke unguwar su Lalla ɗin.

"Kallon fa! Kamar baki san ni ba ƴan'mata? To kar ki cinye wa Hafsat miji." Ibrahim ya yi maganar haɗe da kakalo murmushin dole, ganin da ya yi tana shirin harbo jirginsa na damuwar da yake tattare da ita sanin halinsa ciki da bai da ta yi, ga kuma kallon da take yi masa na kurilla.
"Dadin abun nima da nawa masoyin!" tayi maganar ta rufe fuskarta haɗe da murmushin tunawa da nata masoyin da ta yi ita ma.  Kafin ya yi magana sai ta ƙara cewa
"Me yake faruwa big bro ka shigo gida a fusace? Hankalina ya tashi matuƙa ganin yadda ka shigo gida wallahi, na zata ma wani baƙo ne muka yi wanda bai san kan gidan ba said da na fito na  ga ashe kai ne. Ka yi hakuri yayana komai yana da lokaci da izinin Allah, ka cigaba da addu'a ka ji ɗan'uwana mp"
Wata ƙima da mutumci ne haɗe da ƙara ganin darajar Farida ta kara linkuwa a zuciyar Ibrahim, kaso mafi yawa na damuwar da yake ciki sai ta ragu saboda kullum burinta ta yi masa addu’ar fatan nasara da samun cikar burinsa.  Sai ya ce da ita
"Na goda sosai yar'uwa mai matukar kirki, Allah Ya ba ki miji na gari"
"Ba ka da damuwa angon Hafsat! Ya labari? Da fatan an samu cigaba a lamarin?" In ji Farida tana kallonsa alamar tana jiran amsar da zai ba ta. Sai dai yau ya ɓoye mata saboda ba zai iya faɗa mata cin fuskar da Lalla ta yi masa ba. Ba ya son ko kadan ta ji haushin wacce yake so, sai ya sami kansa da cewa "AlhamduLillah ya! Har ma ta fiton mun yi bankwana. Ni dai fatana ki taya ni da addu’a saboda na fi bukatarta a wannana lokacin har yanzu da sauran aiki a gabana don ba ni ne a zuciyar ba."
"Da izinin Allah komai zai wuce, za ka same ta in sha Allah, ka manta komai ya kankama tun ranar da baba ya tafi..."
Kafin ta karasa wannan maganar Ibrahim ya katse ta yana cewa
"Hummm sister kenan! Kamar ba a ba ki labarin yadda ake ciki ba!"
"Na san komai shi ne nake cewa ka kwantar da hankalinka kawai, ka ci gaba da addu'a in sha Allah saura kiris ka mallake ta "  Farida ta yi maganar tana masa murmushi,sannan ta ce
"Bara in koma in da na fito, yayana yau dai da alama ka bar jarumtar gida don sai da ka zo gidan sannan ta dawo, bye!" Ta ƙarasa maganar tana dariya haɗe da barin wajen sai ya ce da ita
"Zan kama yarinya." Sannan ya wuce ɗakinsa.

Washegari da safe ya koma bakin aikinsa, sosai Farida ta sha kukan rabuwa da shi, shi ma ya ji babu daɗi har yana cewa in ya yi aure za ta dawo gidansa da zama kamar ita ma ba auren za ta yi ba da za ta tarea gidansa. Haka dai suka rabu cike da kewar juna tana yi masa addu'art samun nasara.

        💝💞💘💝💞💘💝💞💞

A ɓangaren Lalla kuwa tana yi ta shirye-shiryen tafiyarta Niamey babu kama hannun yaro. Sai dai yau mama ta zo mata da wani labari wanda ya girgiza ta haɗe da sanya ta cikin ruɗani, kuma babban abin da ya ba ta mamaki shi ne da mama ta ce da sanin mijin da za ta aura ne hakan ya faru wanda ita kuma sam ba su yi zancen da Nura ba, don ma lokacin da ta zo mata da zancen suna hira da Nura ne kuma bai faɗa mata ba duk da hirar da suke yi a kan tafiyar tata can Niamey ɗin ne.
"Mama abin da yake ba ni mamaki ya aka yi Nura bai taɓa faɗa min ya sauya ra'ayinsa a kan aikin da zan je na nema ba? Kuma ke kin ce da izininsa kuma shi ne ma ya hana tafiyar? Kenan ya ɓoye min don ya san sai na yi faɗa shi ya sa ya kwashe ya faɗa maki ko?" Ai wallahi sai na kira sa in ji dalilinsa na yi hakan? Tun farko me ya sa zai kwaɗaita min da neman aikin a can?"
Cewar Lalla cikin maganar da zai nuna ranta ya ɓaci sosai da maganar. Sai mama ta ce da ita
"Lalla Hafsat !" Saurin ɗago kanta ta yi da sauri don ta san tun da mama ta kira ta da wannan sunan maganar mai muhimmanci ce, sai ta ce da ita
"Tashi zaune da kyau mu yi magana."
Babu musu ta tashi zaune tana kallon yanayin mahaifiyarta yadda ta ɗaure fuska babu alamar wasa a tattare da ita sannan ta ce
"Da izinin mijin da za ki aura, ko kuma in ce shi ne ma ya hana ki tafiyar can ɗin don bai jima da kira na ba a kan tafiyar taki ba..."
"Amma mama ..." Ki saurare ni na ce har in gama maganata." Sai Lalla ta yi shiru tana sauraren mahaifiyarta. Sai Hajiya Amina ta ci gaba da cewa
"Tun ranar da aka kawo kayan aurenki ya ce bai buƙatar ki tafi neman aikin a can, in kin tare za ku yi maganar da...."
"Mama!" Lalla ta katse ma da sauri tana cewa
"Ban fahimci komai ba cikin wannan maganar taki mama, me ya sa Nura zai yi min haka? Ya min adalci kenan da har ya aiko gidanmu ba tare da ya faɗa min ba?"
"Na ce ki bari na yi maki bayani ko? Me ya sa ba kya jin magana auta?"

LALLA HAFSATOù les histoires vivent. Découvrez maintenant