Page 25

15 1 0
                                    

"Nura!"

Mama ta kira Nura cikin ɗan ɗaga murya don ta lura bai hayyacinsa. Tana mamakin wannan kallon kurillar da yake yi wa Hafsat wanda ta kase gane kallon mene ne. Kamar bai ganta ba ne ko me?
Saurin kawar da kansa ya yi daga kallonta saboda kiran da mama ta yi masa wanda ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya faɗa.

Kallon mama ya yi sannan cikin marairaicewa ya fara magana yana cewa
"Mama don Allah ki bar ni in tafi makaranta. Muna da jarabawa yau fa."

"Ka tafi ina a wannan halin? Mama kar ki bar shi ya tafi. Kuma ba su da jarabawa yau wallahi ya dai faɗa ne."

Hafsat ta yi furucin wacce ta tari numfashi mama kafin ma ta ce wani sai ta riga ta magana saboda yanayin da ta ga Nura a ciki ba za ta so ya fita a hakan ba.
Tana maganar hankalinta yana ga Mama don jin abin da za ta ce.

"Kyalewarki auta! Babu inda zai tafi ai."

Mama ta yi maganar tana kallon Nura  da yake faman hararen Hafsat don ya ga alamar ta kwafsa masa. Ba ta bi ta kansa ba don in ta tsaya kula sa zai hana Hafsat tafiya makaranta wacce ma tuni lokacin shiga ya wuce. Kuɗi ta mika Hafsat tana cewa

"Yawwa auta amshi wannan ki shiga taxi tunda kin riga da kin yi latti. Allah Ya kiyaye hanya ki hanzarta kin ji auta."

Rau-rau-rau da ido Hafsat ta yi kamar za ta yi kuka saboda ba za ta iya tafiya ta bar ɗan'uwanta a wannan halin ba. Ganin da ta yi masa ya kaɗa mata ƴan hanji don wata irin rama ta ga ya yi mata dare ɗaya daga rabuwarsu jiya zuwa yanzu da safe ta ga kamar an sauya sa ba Nura ɗinta ba ne.

Ganinsa da ta yi a haka har ta yanke shawarar fasa tafiya makarantar saboda ba za ta samu nutsuwa ba in ta tafi makaranta ɗin. Sai dai sautin muryar mama kawai take ji wai ta tafi ita ɗaya makaranta ba tare da shi ba. Tana ina za ta iya tafiya ba tare da shi ba? In ta tafi kuma suna nufin ta yi karatu kuma? Sai dai tunani don ba ta da nutsuwar da za ta tsaya ta yi karatu.

Tana shirin cewa wani abu sai Mama ta tari numfashinta tana cewa
"Mu je na rakka ki auta bakin titi ki samu taxi."

"Mama ba fa zan tafi ba sai tare da shi."
In ji Hafsat wacce ta yi furucin a shagwaɓe tana kallon Nura da ita yake kallon shi ma.

"Kin manta ke kika ce kar in bar shi ya tafi? Kuma ki ce tare kike son ku tafi yanzu?" Cewar mama cikin mamakin Hafsat don ta zata zuwa wannan lokacin sun daina wannan shiriritar da suke yi tun suna yara. Kodayake sun ɗan jima ɗaya bai yi rashin lafiyar da ta hana shi tafiya makaranta ba balle ta fahimci hakan.

"Ni ma ba zan tafi ba." In ji Hafsat tana sadda kai ƙasa.

"A a Lallata ki taka ki tafi kin ji?"
Nura ya yi furucin a sayayye kamar wanda ake wa duka. Har yanzu zuciyarsa bugawa take yi kamar ɗazu.

"Ba ni son gulma ka ji! Tashi ka yi wanka na ba ka minti goma ka fito ka wuce ku tafi ku ba ni waje."

Mama ta faɗa tana kama hannun Hafsat suka fice daga ɗakin don ta lura suna son ɓata mata lokaci ne. Kuma ta ga alamar Hafsat ba za ta tafi makaranta ba gara kawai ta bar Nuran ya tafi can su karata ɗin tunda haka suke so.

💞💝💞💝💞💝

"Yawwa don Allah Usman ka faɗa min yadda ake gane ana son mutùm. Amma kuma ban da cin fuska kuma ban da dariya don Allah."

Tambayar da Nura ya yi wa wani abokinsa kenan lokacin da suka fito break yake tambayarsa abin da yake damunsa da kuma zuwansa makaranta a latti don ya ga yanayinsa kamar ba shi da lafiya. Shi ne maimakon ya faɗa masa abin da yake damunsa sai ya yi masa wancan tambayar yana tsare.

Wata dariya Usman ya kece da ita wacce ta kusa kular da Nura ɗin saboda tashi ya yi yana neman tafiyarsa inda ya fito don ya ga alamar Usman iskanci kawai yake yi masa ba faɗa masa amsar tambayarsa zai yi ba.

Tsabar dariya har riƙe ciki Usman yake yi don abun nema ya samu ne gare sa. Da sauri ya tsagaita dariya yana nufar wajen Nura haɗe da kama hannunsa yana cewa
"Haba abokina na Harsat ikon Allah. Ba gaba da gaba sai ta baya sai an shirya. Duk garin da babu Hafsat mutanen garin su kama da wuta. Tsaya ka ji."

Cak Nura ya tsayar da tafiyar da yake yi bugun zuciyasa ya tsananta. Ƙwaƙwalwarsa babu abin da take yi sai amsa amon muryar Usman na abin da yake ce masa. Wato shi ma ya san yana son Hafsat. Wato in ya fahimta kowa ya san yana son da soyyayar Hafsat a zuciyarsa amma shi bai sani ba? Ko ya aka yi bai taɓa ganewa ba.

'Ban san so ba shi ya sa'
Nura ya faɗa a zuci.

"Me kake nufi da zantukanka? Ban fahimci komai ba."

"Ba za ka fahimta ba tun da ba ka san so ba." Cewar Usman yana yi masa murmushin haɗe da zama inda ya tashi yana nuna masa waje alamar shi ma ya zauna. Bai yi musu ba ya zauna ba don abun ya zunɗume sa haɗe da ba shi mamaki.

Alamomin kamuwa da soyayya duka Usman ya faɗa wa Nura wanda sak abin da yake faruwa da shi ne. Sosai ya shiga mamakin rashin gane hakan da bai taɓa yi ba a karan kansa. Ko don bai san so ba ne? Shawarwari sosai Usman ya ba shi yadda zai gudanar da soyayyarsa cikin jin daɗi da kwanciyar hankali sannan ya ƙara da cewa
"Ina mai ba ka shawara da kar ka tunkare ta da maganar. Mace ba kai tsaye ake faɗa mata da ana sonta ba. Mace koya mata soyayya ake yi sannan kuma a ba ta kulawar da ta dace har ta faɗa tarkon so. Namiji in har ya cika cikakken namiji wanda ya iya so bai kai sai ya je yana neman soyayya a wajen mace ba. Shiga jikinta yake yi ya koya mata sonta sosai sannan su ji su a duniyar so. Kai ba ka da matsala ma saboda ita ma na fahimce tana sonka. Ina yi maka fatan alkairi abokina."

Kasa magana Nura ya yi don dai zuwa yanzu ya gane tabbas son Hafsat ya yi masa mumunan kamu sai fatan dacewa.  Saurin kallon Usman ya yi jin kalamansa na ƙarshe. Sai ya ce masa
"Wai wa ya faɗa maka Hafsat ce nake so?"

"Na ga soyayyarta a cikin idanuwanka. Ko ce maka aka yi kowa ma irinka ne?"

Usman ya yi furucin yana tashi zaune don ya ga alamar lokacin komawa aji ya yi. Nura bai ce masa komai ba sai murmushi da ya yi masa shi ma ya mayar masa da martanin murmushi sannan suka wuce aji hannunsu sarke da juna suna sake tattaunawa a kai.

Vous avez atteint le dernier des chapitres publiés.

⏰ Dernière mise à jour : Jul 01, 2021 ⏰

Ajoutez cette histoire à votre Bibliothèque pour être informé des nouveaux chapitres !

LALLA HAFSATOù les histoires vivent. Découvrez maintenant