Page 20

1 0 0
                                    

Fatima, Nura da Lalla Hafsat duk sun zana jarabawar shiga makarantar mai suna Lycee d'Excellence de Niamey wacce makarantar sai wanne da wacce ne kaɗai suke samun jarabawar saboda suna da dokoki sosai sannan kuma ana bayar da karatu sosai saboda duk shekara 100% suke yi a jarabawarsu ya fita daga sakandari. Duk wanda ka gani can to gwani ne shi kuma akwai ilmi gare sa. Wannan dalilin ne ya sanya suka yi jarabawar don suna burin zama wani abu a nan gaba.

Lokaci ya ja abubuwa suna yi ta tafiya yadda ake so. Sannan kuma a cikin wannan hutun ake shirin yi wa su Hafsat saukar Alƙur'ani. Sosai suke murna ga samun exam ga kuma sauka don ba su wasa sam da zuwa islamiya. Wani lokaci daga makaranta ma in ba a yi suna zuwa gida za cire kayan makaranta su saka na Islamiya su wuce. Ana yi ta shirye-shiryen sauka. Ƴan'uwa na nesa da na kusa duk suna yi ta shirye-shiryen saukar aurar mama Amina, da ƴar'uwarta Fati. A cikin watan Satumba aka yi saukar sun sha kyaututtukan litattafai da kuma kuɗi daga ƴan'uwa da wasu malamai.

Bayan sauka da wasu kwanaki kuma aka fitar da sakamakon jarabawar shiga Lycee d'Excellence inda Lalla kaɗai ce ta ci jarabawar sauran ba su samu ba. Ko kaɗan ba ta nuna wata alama ta farinciki ba don cewa ta yi ma an yi munafurci an hana wa sauran ƴan'uwanta kuma alhali komai nasu tare yake, ai wannan ba adalci ba ne. Da tana da yadda za ta yi da tuni ta yi an karkare sunanta ko kuma an sanya sunan ƴan'uwanta don a cewarta inséparable ne su, sai dai babu halin haka sai haƙuri don jarabawa ta gadi hakan. A ranar take gaban mutanen da suka zo yi mata batka ta ce ba za ta tafi ko'ina ba ta bar ƴan'uwanta nan ba, gara ta yi zamanta nan tare da su don da nan da can duk ɗaya ne a cewarta. Kasake kowa yake kallonta don sun san yadda take son makarantar amma yanzu ta ce ta fasa zuwa saboda su Nura? Babu wanda ya tanka ma aka cigaba da hira don duk an zata wasa ne take yi ko kuma ta ji ta bakin mutane._

Abu kamar wasa ashe da gaske Lalla take don kememe ta ce babu inda za ta tafi ba tare da yan'uwanta ba don ba ta da abokai sama da Nura da Fatima kuma ba za ta iya tafiya ta bar su ba. Duk yadda aka yi da ita ta tafi haka ta sanya wa idanunta toka ta murje akan ba fa za ta tafi ba, ana tunanin ma ta fada ne kawai amma za ta tafi daga baya. Sai dai har lokacin komawa makaranta ya yi suka ga ba ta fara shiri ba don sun yi tunanin wasa ne saboda soyayyarta da makarantar don ana bayar da horo sosai, ba kowa ba ne yake samun sa'ar shiga can ba sai ɗai-ɗai-ku cikin mutane. Ana jibi za a koma makaranta Lalla Hafsat ta yi kitso da lalle ta yi kyau kamar ka saceta ka ruga da gudu, mama ta iske ta har dakinta tana linke kayanta saboda ta yi wankin komawa makaranta wanda duk a tunanin mama na tafiyar nan don kullum tana yi mata zancen tafiya amma sai dai kawai ta yi shiru don ta yi alkawarin babu wanda za ta sake yi wa zancen don daukar abun suke yi a wasa.

Zama saman gadon mama ta yi sannan ta taya ta linka kayan, suna hira sama-sama. Sai mama ta sanyo mata maganar tafiyarta Niamey gobe ne ko jibi.

"Mama wacce tafiya kuma bayan tun tuni na ce ba zan tafi ba?" Cewar Hafsat tana kallon mama a shagwaɓe saboda sangartatta da aka yi ganin babu kowa a   tare da ita, kuma ana kiranta da auta saboda ba ta san da wata kanwa a gare ta ba don ta mance da wata Maryam a rayuwarta shi ya sa take kiran kanta da autar mama har mutane suka ɗauki sunan suna kiranta da hakan.

" To fa!" Cewar Mama Amina sannan ta ƙara da cewa
" Yaushe kika sauya shawara ba tare da sani ba?" Mama ta idasa maganar da alamar mamaki kamar ba ta san da zancen ba, yanzu ta yi maganar ne don ta gwadata saboda wani dalili.

Saurin kallon mama Hafsat ta yi jin mama ta ce ba ta da masaniyar ta sauya shawara, alhali kuma kullum sai ta fadi haka a gidansu. Sai ta fara magana a sanyaye  tana cewa
"Mama kin fi kowa sanin na fasa tafiya fa. Ai da zan tafi da tuni na fara shirin tafiya."
"Wannan lallen fa da kika sha har da kitso? Na zata na tafiyar ne tun da ba lalle kike yi ba."
In ji mama tana kama haɓa.

"Nura ne da Fatima suke min gorin ban kitso shi ya sa ni kuma na tafi aka yi min shi. Amma fa mama saura kaɗan in yi kuka don zafi."
Cewar Hafsat.

"Ai sun kyauta ba ga shi ba duk kin yi kyau. Amma auta me ya sa ba za ki tafi ba? In ji mama Amina."
Sai Hafsat ta ce
"Mama ta ya zan tafi ba tare da su Nura ba?" Hafsat ta yi maganar cikin yarinta kuma tsakaninta da Allah.

"Ta yadda aka yi kika ci jarabawa ba su ba ci. In ban da abunki auta ai ko su ba za su jin dadin ƙin tafiyarki ba saboda ko Nura ɗin ya kawo min ƙararki akan ki shirya ki tafi don makarantar tana da matukar amfani ya kamata ki shirya ki tafi don ya ce min wai ya yi maki magana kin yi fushi da shi." Mama Amina ta idasa maganar tana kallon Hafsat wacce ta yi kasake tana kallon mama na jin abin da ta ce don ba su jima da gama da waya ba a kan tafiyarta tana ce masa ba za ta tafi ba shi kuma yana zancen ta shirya tafi.  Tunanin wayar da suka yi da shi ne take yi

"Lallata yaushe za ki tafi ne? Na ji har yanzu shiru."

"Na sha fada maka babu inda zan tafi Nurana." In ji Hafsat

"Amma kin san ba za ki tafi ba kuma kika yi jarabawa? Cewar Nura.

"Kenan ka matsu na tafi ka sake ko? Ashe daman ka gaji da ni?" Cewar Hfasat cikin fushi kamar yana gabanta don ta ki tafiya ne saboda su amma shi ya nuna kamar ma bai damu da ita ba. Abin da ba ta sani ba ya fi ta damuwa da tafiyar da za ta yi ta bar shi don ko kaɗan bai son abin da zai raba shi da ƴar'uwarsa. Shi ma ya yi maganar ne don jin amsarta amma ko kaɗan bai son tafiyar tata don babu yadda zai yi ne kuma ga makrantar tana da matukar amfani. Cikin lallami sai ya ce
"Wallahi Lallata na san zan yi kewarki sosai. Amma ina so ki sani komai mukkadari ne daga Allah, ba ki san abin  da yake cikin wannan jarabawa da kika samu ba mu ba mu ci ba,watakila wannan abun da ba mu samu ba, ba alkairi ba ne a gare mu. Don Allah ki yi haƙuri ki shirya ki tafi kin ji ƴar ƙanwata?" Ya ida magana cikin kwantar da murya sai ita kuma ta ce da shi
" Ba fa zan tafi ba. Ta ida maganar tana kashe wayar wai ita aladole ta yi fushi da shi. Sai ya sake kiranta don a tunaninsa sabis ne ya ɗauke sai dai yana kiran ba ta ɗagawa

shi ne ya zo gidan ya faɗa wa mama tana fushi da shi don ya yi mata maganar dayake sun saba da mama sosai tun yana karami kuma babu abin da ya sauya har yanzu da yake da shekara goma sha takwas

Bayan ta gama tunano wayar da suka yi ita da Nura ne sai ta ɗaga kai ta kalli mama sannan ta ce,

" Mama ko na je ba zan ji daɗin karatun ba tun da babu waɗanda na saba da su."

"Babu damuwa autata, Allah Ya sa haka ne ya fi zama alƙairi, amma ki daina fushi da yayanki kin ji autata."

Mama ta yi maganar tana shirin mikewa tsaye, sai Hafsat ta yi saurin cewa

"Nura fa ƙanena ne mama, na fa girme sa"

"Sannu kakarsa Hajiya Ladi." In ji mama tana fita daga ɗakin.

LALLA HAFSATOù les histoires vivent. Découvrez maintenant