Wata irin kunya ce ta kama Fati na dizgawar da Lalla ta yi wa Ibrahim, dukda tana da gaskiya amma wani lokacin ana barin halak don kunya. Ta san ba don komai ta yi hakan ba sai don a cikin unguwarsu ne, kuma a kofar gidansu ga shi ba wani saninsa suka yi ba sosai duka kwana biyu ne da saninsa. Sannan in har suka shiga motarsa hanyar da za su hucewa to ta kofar gidan su Nura ne za su bi kuma akwai mutane a wajen gidan sannan wani zai iya ganin su ko ita ko Lalla ɗin, ko ba a faɗa mata ba ta san saboda haka ne ta ƙi shiga motar.
Amma ai bai kamata ba ta yi masa hakan ba, ko ba komai ai kulawa yabawa, ko daa ce wani yace mata wanene shi ai tana iya ɓoyewa ta hanyar cewa dan’uwanta ne dukda dai Nura ya san danginta saboda kamar dan gida yake a gidansu.
Cikin murya mai nuna alamar rashin jin daɗi Fati ta fara magana tana cewa
"Ka yi hakuri don Allah ba laifinta ba ne, in har ta hau motar nan za a samu matsala saboda akwai wani dalilinta na yin hakan"
"Ba komai wallahi bestynmu ban ji haushi ba ko kaɗan, amshi wannan ki biya mata da shi don Allah" Cewar Ibrahim yana mika mata ledar wacce ya sanyo wayar da ya siyo wa Lalla, ba ta yi masa musu ba ta amshi ledar amma tuni har ta fara dasa ayar tambaya a kan Ibrahim saboda ya fara ba ta mamaki daga shekaranjiya da suka fara haɗuwa da shi zuwa yau ɗin nan, ga shi kuma hada wani sako yake cewa a ba wa Lalla, in har hasashenta gaskiya ne to lallai wannan bawan Allah abun tausayi ne wallahi, saboda zai sha wahala sosai a hannun Lalla saboda tuni ta sadaukar da zuciyarta ga waninsa, lallai akwai aiki babba a gabansa."Kar fa ta tafi ta bar ki" Shi ne abin da ya ce mata wanda ya dawo da ita daga tunanin da ta fada, sai ta ce da shi
"Ba ka fada mana sunanka ba har yanzu kuma ga shi an zama ɗaya."
"Afuwan tun ranar mantawa na yi wallahi ban fada maku ba, sunana Ibrahim Alhaji Abubakar, ɗan sanda ne ni kuma ɗa a wajen aminin kawunku wanda aka yi aure a gidansa shekaranjiya"
Ibrahim ya yi maganar haɗe da buɗe murfin motarsa yana shirin shiga motar gudun ka da ta sake tambayarsa wani abu don ya san sai ta yi tambayar, ai kuwa abun ya yi gudu ne ya faru don sai da ta yi maganar tana cewa
"Ban fahimci me kake nufi ba? In kuma na fahimta kana nufin ka san kawunmu kenan."
Ta yi maganar da mamaki saboda ta yi mamakin da ya ce mahifinsa abokin kawu ne, ita daman tun ranar sai da ta so ta ce masa kamar ta san fuskarsa sai kuma dai ta yi shiru gudun kar a zo ba shi ba ne kuma ga shi bai yi maganar ya san su ba. Sai ya ce sa ita
"Za ki fahimta nan gaba, ku kula da kanku kuma ki kular min sosai da besty sannan kuma a kula da kyau kar a yi dare." Ibrahim ya yi maganar yana rufe murfin motarsa kamar ba shi ne ya yi maganar ba.Sororo ya bar Fati sake da baki tana kallon ikon Allah, babu abin da ya fi ba ta mamaki kamar da ya ce ta kular masa da bestynta, me hakan yake nufi kenan? Lallai hasashenta ya fara zama gaskiya, wannan bawan Allah ya faɗa soyayyar *Lalla Hafsat*, sai da ta ji ƙarar motarsa ya tayar sannan hankalinta ya dawo jikinta ta taka a sanyaye zuwa bakin titi inda Lalla take tsaye tana jiranta. Kamar wacce babu lakka a jikinta haka ta iske ta babu wanda ta ce da ɗan'uwansa kala a cikinsu suka shiga adedeta sahu don kowa da bikin zuciyarsa, sai da suka ɗan yi nisa ne sannan Fati ta mika wa Lalla ledar da Ibrahim ya ba ta wacce ba ta san minene a ciki fa
"Wannan fa?" In ji Hafsat
"Buɗe ki gani." Fati ta ce tana kallon gefe guda. Ba ta yi musu ba ta buɗe ledar sai ta ci karo da kwalin waya kalar tata wacce ta faɗi shekaranjiya ta ci screen, ko ba a faɗa mata ba ta san Ibrahim ne ya siyo mata wayar, me za ta yi da wayar ita? Ita da har ta faɗa wa Nura wayar ta lalace kuma ya siyo mata kalarta a can inda ya tafi saboda soyayyarta ga wayar. Sai ta rufe ledar tana mika wa Fati haɗe da cewa
"Waya kika siye kalar tawa kenan?"
"Waya Ibrahim ya siye maki dai kalar taki wacce ta lalace." In ji Fati
"Ba ni buƙata ko an faɗa masa ina buƙata ne? Riƙe ki mayar masa da abar sa." Lalla ta ce tana ɗora wa Fati saman cinyarta. Sai mai adedeta sahu ya ce
"Hajiya ba a mayar da hannun kyauta fa, duk wanda ya yi maka alkairi amsa kake yi sai ka yi masa addu'ar Allah Ya ƙara masa buɗi."
"Faɗa mata dai mai adedeta" cewar Fati, ko kala Lalla ba ta sake cewa ba har a ka sauke su duk irin hirar da mai adedeta da Fati suke cewa amma ta yi masu shiru saboda hankalinta ya fara karkata ga tunanin akwai wani nufi ga wancan mutumin.
Ita kuma Fati sai ta sanya wayar cikin jakarta sai bayan sun dawo gidan amarya adedeta sahu ta ajiye su sannan ta sake ba ta wayar, ƙin amsa ta yi kuma duk yadda ta roke ta akan ta amsa ƙi ta yi a cewarta ba ta ga amfanin amsar wayar ba saboda za ta ja mata wani abu a wajen mahaɗin rayuwarta. A haka ta haƙura ta riƙe ta wajenta har zuwa wani lokaci ta ga yadda za a yi, sannan suka yi sallama kowacce ta shiga gidansu.💞❤️💞❤️💞❤️💞❤️
Bayan sati biyu abubuwa da yawa sun faru, ciki har da dawowar Nura daga tafiyar da ya yi, ya kawo wa Lalla tsaraba sosai kamar wanda ya yi tafiyar wata guda, kuma sun cigaba da gudanar da soyayyarsu sai ma abin da ya ci gaba, kuma ya kawo mata wayar da ya siye mata a can kalar wacce ta lalace. Sannan baban abin da ya fara damun Lalla shi ne yadda Ibrahim ya fara takura wa rayuwarta saboda ya sha mata kai sosai don har ma ya bayyana mata sirrin zuciyarsa, sai ta ba shi haƙurin tana da miji amma kamar ƙara zuga sa take yi saboda ce mata ya yi tunda dai ba a ɗaura mata aure ba zai jaraba ya gani ko zai dace, amma ina! Ba ta kula sa, sannan ba ta ɗaukar kiransa ta so ma ta yi block ɗinsa amma ba ta yi ba hakan ba, sai ya yi mata kira sau goma ba ta ɗaga kira ɗaya ba, message ne ma yake samun tana amsa masa ko shi ma sai dai in sallama ce ya yi mata take mayar masa da amsa saboda sanin muhimmancin sallama, amma daga shi ba ta sake mayar masa da amsa duk abin da zai ce mata, yana turo sakon take goge sa take ba sai ta karanta saboda gudun kar Nura ya gani ya ɓata masa rai ko kuma ya yi tunanin ta fara son waninsa ne.
Shi yasa duk yadda Ibrahim ya so ya shawo kanta abun ya ci tura kuma ya ƙi haƙura da ita, a waje guda yake jin muryarta in Farida ta kira ta sai ta ba shi su gaisa nan ne kaɗai zai ji muryarta,shi ma iya gaisuwa ce kaɗai take haɗa su ba ta sake yi masa magana za ta yi shiru daga humm sai a a kawai take cewa, kiran ma na Farida don dai tana jin kunyarta ne take ɗauka amma ba don haka ba da babu yadda za a yi ta amsa kiranta tunda tana haɗa da yayanta Mr Naci sunan da ta sanya masa kenan a lamabarsa.Ibrahim ya dukkufa da addu'a ba dare ba rana akan zaɓi na alkairi amma kamar ƙara masa soyayyar Lalla ake yi saboda kullum jin sonta yake yi yana linkuwa a zuciyarsa, yana fatan samunta saboda har yanzu bai sare ba burinsa shi ne ta zama uwar gidansa, amma ita dai yana ji ma ta tsane sa saboda rashin ɗaukar kiransa da ba ta yi, yana cutuwa sosai saboda tunani ya fara yi masa yawa kuma ga shi saura sati biyu ya koma daman hutun wata guda ne ya ɗauko.
Sai ya yanke shawarar tafiya gidan kawu don ya san can ne kawai za a share masa hawayensa, yana tunanin kawu zai iya ba ta haƙuri ta so shi saboda yana da labarin yadda take ɗaukarsa da muhimmanci a rayuwarta kuma shi ne uban ɗaurin aurenta.Domin samun cigaban labarin nan ku tuntuɓi wannan lambar +22784506476
200 ne kacal
Real Nana Aisha 🥰