🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻Littafi na farko 📝
Shafin kyauta na huɗu
Bayan Baba ya zauna dinning ya fara cin abinci sai Samira ta tashi ta tafi wajen mama tana sakar mata hawayen makirci, ganin da ta yi mama sai kallonta take yi ba ta ce komai ba sai ta fara magana cikin kissa da kisisina
"Mama ina gani gida zan koma gobe da safe don ina ga zamana ba shi da wani amfani a nan gidan."
"Saboda me ƴata?" Inji Mama ta ida maganar haɗe da zaro ido waje tana mamakin abin da zai sanya Samira sauya shawara kuma, ita da kullum in har Ibrahim ya zo hutu sai ya yi wata guda cur tana gidansu amma wannan karon daga zuwansu har ta fara zancen tafiya gida, lallai dole ne ta ɗau mataki don ba za ta riƙe yaro ba tun yana ƙarama, tana kula masa da dukiyarsa, ya zo ya auri wata bare bai auri ƴarta ba, wannan ba zai taɓa yiyuwa ba sam. Kar dai a zo maganar da Farida ta yi mata ne ya sanya ta yin fushi har take zancen tafiya gida, lallai sai ta hukunta Farida a kan wannan iskancin da take yi mata na son raba ta da ƴar ƴar'uwarta, in ita ba ton danginta ta fi son bare fiye da su to ita tana son son nata dangin.
Sai ta mayar da kallonta ga Samira da ta yi shiru ba ta ce komai tana kallon mama kawai na tunanin da take yi, ko dai hakanta ya cimma ruwa ne, sai kuma ta fara addu'ar Allah Ya sa Alhaji Abubakar ya ce wani abu tunda yana jin abin da take cewa amma ga mamakinta sai ta ga kamar ma bai san tana nan ba saboda ya yi shiru bai ce komai ba, lallai kam tana ganin da wiya ne a gasa kaza a yada, da wiya ma in babansu ya san da maganar aurensu da Ibrahim, amma dai bari ta ga iya gudun ruwansu gabaɗaya tunda sun ƙi cewa komai.
"Tashi ki tafi daki za mu yi magana da babanku." Wannan maganar da Hajiya Sabira ta yi ita ce ta katse mata zancen zucin da take yi, ba ta yi musu ba ta tashi tsaye haɗe da cewa
"Okay mama sai da safe." Tana gama maganar kai tsaye ɗakinta ta shiga tana waiwayen bayanta don ta ƙagu ta ji abin da Hajiya Sabira za ta ce wa Alhajj Abubakar da kuma amsar da zai ce mata in an yi masa maganar aurensu ita da Ibrahim.Hajiya Sabira ta tashi ta nufi wajen Alhaji Abubakar tan wani cikin magani kamar ba ta son magana ita Ala dole an ɓata mata rai.
"Alhaji ina so mu yi magana da kai." Iya abin da ta ce kenan sannan ta nemi waje ta zauna haɗe da ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya.
"Ba ni da lokaci bacci nake ji, da safe ma yi maganar in sha Allah." Inji Baba ya ida maganar yana yin gaba ya wuce dakinsa don sosai ya ji haushin abin da ta aikata yanzu nan na cin zarafin Ibrahim, shi kuma yana jin tausayinsa fiye da sauran ƴaƴansa saboda kasancewarsa maraya tun yana ɗan shekara bakwai zuwa takwas, sai dai matsalar bai samu uwar riko ta kwarai ba kasancewar tun tasowarsa har zuwa yanzu gallaza masa take yi amma abun taikaci ta ƙi ta saduda dukda bai taɓa daga kai ya kalle ta ba da nufin yana jin zafin abin da take yi masa balle har ya ce zai rama abubuwan, sai dai kawai ya yi ta ba ta haƙuri ko da ba shi da laifi, wacce take jin tausayinsa kuma ana neman a hana ta ita ce kaɗai mai kirki cikin ƴaƴansa wato ƙanwarsa Farida. Shi ne don ta ga yana ɗaga mata ƙafa a kan abubuwan da take yi wa Ibrahim take neman ta raina sa, har za ta zo masa da zancen su yi magana amma take wani ɗaure masa fuska, shiyasa ya ce mata bacci yake ji saboda yana da yaƙinin da wiya maganar da za ta yi masa mai muhimmanci ce don haka ya buƙaci gara ya je ya yi baccinsa har zuwa safe can sai ta faɗa masa don bai buƙatar ƙara wata damuwa a kan wacce yake ciki yanzu.💞💞💞💞💞💞💞💞
Tun a hanya Ibrahim ya ba wa Farida labarin yadda aka yi ya kamu da soyayyar yarinyar da bai sani ba (Lalla Hafsat) bai kuma taɓa ganinta ba, illa muryarta kawai da ya ji ne ya kamu da sonta har kuma yake mafarkin samunta a matsayin matarsa. Mamaki sosai ya kama Farida da jin wannan lamarin na yayanta, lallai so mugun sartse ne kuma shi ne wanda yake shiga a lokacin da ya so ba tare da neman izini ba ko neman shawara ba, amma ta tausaya wa yayanta jin labarin da ya ba ta na wayar da suka yi sau ɗaya da Lalla Hafsat, ga kuma na kiran da ya ce mata Nura ya yi masa da alama saurayinta ne kuma irin sosai ɗin nan saboda ga yadda ya bata labarin tana tunanin yana kishi sosai kuma sun yi nisa a son juna. Kai so me ya sa ka yi wa yayana haka? Ko kaɗan na ni son ya sha wahalar soyayya, na fi son ya fara son wacce ba ta taɓa soyayya ba amma ina, hakan ba ta samu ba sai da wata ta sace masa zuciya a cikin abin da bai gaza mintin ɗaya ba. Kai ta tausaya wa yayanta sosai kuma ta san zai sha wahala in dai bai yi da gaske ba don shiga rayuwar masoya sai wanda ya jajirce sosai kuma yake da haƙuri don sai ya sha wulankaci kala-kala har lokacin da zai samu cikar burinsa.
Fatan alƙairi ta yi masa haɗe da kwantar masa da hankali da izinin Allah zai same ta kuma za ta zama matarsa ya dage da addu'a Allah Ya zaɓa masa mafi alkairi a rayuwarsa. Ya ji daɗin addua'arta sosai sannan suka cigaba da hirarsu har suka kawo unguwar su Lalla. Daidai inda Fati ta yi masa kwatancen gidansu nan ya yi parking ɗin motarsa yana duba lambar Fati dayake lokacin da suke waya ya ɗauki lambar ya sanyata a wayarsa. Kiranta ya yi tana yi ringing ba ta ɗaga ba saboda wajen da take akwai hayaniya sosai sai da ta ɗan tashi kaɗan sannan ta daga wayar a lokacin sauran kaɗan wayar ta kusa tsinkewa, bayan sun gaisa take ce masa
"Ban gane da wanda nake magana ba?"
Sai ya ce da ita
"Haba bestynmu har kin manta da ni kuma?" Cewar Ibrahim. Sam Fati ta mance da wanda suka yi waya ɗazu sai ta ce da shi
"Ko dai ka yi ɓatan lamba ne, wallahi ban gane da wa nake magana ba ka yi haƙuri don Allah"
"Ba ɓatan lamba na yi ba, ke ce dai nake nema wacce muka yi waya da ita ɗazu har kika faɗa min inda zan kawo maku waya." Inji Ibrahim, sai a lokacin hankalin Fati ya dawo jikinta ta tuna da wanda ya tsinci wayar Lalla, sai ta yi saurin fita daga mutane saboda hayaniya ƴan kan amarya sai ta ce
"Ayya! Ka yi hakuri don Allah, wallahi sai yanzu na fahimce ka, fatan kana lafiya?"
"Lafiya ƙalau AlhamduLillah,har kin mance da mu ko?" Inji Ibrahim
"Wallahi ba haka ba ne, ka san muna wajen aure ne, yanzu haka kan amarya za mu tafi, hankalinmu duk ya ɗauku a can ne amma ka yi haƙuri Please." Cewar Fati tana zama a saman kujera.
Sai Ibrahim ya ce da ita
"Allah sarki! Kuma ga mu nan unguwarku wallahi mun zo kawo maku wayar besty."
"Allah sarki! Afuwan wallahi shagalin biki ya sanya mu manta sam da hirar da muka yi da kai, yanzu kuma muna unguwar gawo wajen auren cousin sister ɗinmu." Inji Fati ta yi ida maganar a sayyaye saboda rashin jin daɗin wahalar da shi da suka yi na zuwan da ya yi kawo wa Lalla waya kuma ba su gida. Sai Ibrahim ya ce
"Ayya! Kin ga kuwa can ne unguwarmu, da ace na sani da na iske ku can amma bari ga mu nan zuwa."
Fati ta yi saurin cewa
"Mu kuma ga mu nan za mu tafi kan amarya wallahi har motoci ma sun iso na ɗaukar amarya."
"Don Allah besty ki yi haƙuri in na zo sai mu tafi tare kar ki ce komai." Inji Ibrahim ya ƙara da cewa
"Ki faɗa min daidai gidan auren ga mu nan tafe ni da sisterna"
"Wajen CSI KASSOUM MOCTAR ne kwana ta biyu za ka ga taron mutane, sai ka zo." Cewar Fati don babu yadda ta iya saboda ya ce kar ta ce komai ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta faɗa masa inda suke.💝💝💝💝💝💝
Ba a yi minti goma ba sai ga shi har ya iso unguwar, dayake babu nisa sosai kuma yana son ya iske su ɗin, kuma ya sharara gudun tsiya saman hanya. Yana isowa ya kira wayar Fati ya faɗa mata ya iso yana ƙofar gidan ma. A lokacin kuwa ta koma cikin mutane wajen Lalla suna zaune suna hira har take ce mata ma ga wani bako nan tafe zai zo wajenta kuma a tare da shi za su tafi kan amarya. Duk Lalla ta zata sabon saurayi ne Fati ta yi don ta san saurayinta wanda take so ba garin yake ba kuma ba ta saba yawo da wani saurayi ba ko kan amarya za su tafi sai dai cikin dangi su tafi tare da wani. Ko da ta ga kiransa sai ta ce da Lalla ta tashi su tafi bakonsu ne ya zo wanda zai kai su kan amarya, ba ta ce mata komai ba suka fito wajen da ya ce mata ya yi parking ɗin motarsa can nesa kaɗan da gidan. Kasancewar unguwar da hasken fitila sosai shi ya ba Ibrahim damar kallonsu yadda ya kamata. A take ma ya gane su saboda daman tunda Fati ta yi masa kwatancen gidan ya gane gidan aminin mahaifinsa ne kuma kawu ne ga su Lalla saboda ya san su farin sani in ya zo gidan yana ganin Lalla da Fati wani lokacin suna gidan in sun zo yi masu wuni ko kuma ana wani biki hakan nan suke tarewa lokacin da suke yara yanzu ne dai bai sani ba saboda ya jima rabonsa da gidan, ko kuma in sun zo gidan shi ma ya zo wajen takwansa yayan amarya amma shi ma yanzu ba garin yake da zama ba.
Duk ya gane fuskokinsu su ne dai da wiya su gane sa saboda ba yau ba ne ya san ma sun mance sa saboda ba yau ba ne yake zuwan gidan an ɗan jima rabonsa da nan, tun kafin ya fara aiki a Niamey ne lokacin duka suna Sakandari ba za su gane sa ba saboda ko can ma ba wani saninsa suka yi ba shi ma dai don ba shi da mantuwa ne. Lallai abun ya zo masa da sauki tun da yarinyar gida ce da izinin Allah zai aurata kuma. Har suka iso wajensu yana tunanin mafitar da zai yanke na neman aurenta ko sallamar ma da suka yi masu bai ji ba saboda hankalinsa kacokan yana gare su sai da Farida ta amsa tana cewa " wa aleikumassalam, sannunku mes cheries"
Fati ce ta amsa da
"Yauwa ma chérie ça va?( How are you?)" Saɓanin Lalla da ta tsargu da kallon da Ibrahim yake yi mata don ita ta tsani kallo a rayuwarta, amma ga wani mutum sai kallon tsiya yake yi mata, ba don ta ba ƙawarta Fati kunya ba da wallahi ta koma inda ta fito, ta ya ya zai wani tsareta da ido yana kallo kamar ita ce budurwa tasa ba Fati ba.
Shi ma sai da Fati ne ta yi maganar hankalinsa ya dawo jikinsa kuma tun a lokacin ne ya gane ba Fati ce fa wacce ya kamu da sonta ba don ya gane muryarta sosai, take bugun zuciyarsa ya tsananta abin da bai taɓa faruwa da shi ba tunda yake, zuciyarsa ba ta taɓa bugawa ba saboda soyayyar wata ƴa mace bq, amma yau rana tsaka zuciyarsa tana barazanar rabuwa da shi saboda wata ko ma dai ya ce tuni ta rabu da shi ta koma wajen Lalla saboda babu zuciyar a kirjinsa sai dai burbushin inda ta yi zama, sai da ya nemo jarumta sannan ya ce da Fati
"Bestynmu na same ku lafiya? Ya gida ya hidimar aure?"
"Lafiya ƙalau AlhamduLillah ɗan'uwa, ai na zata ba ka magana." Cewar Fati ta ida maganar da murmushi a fuskarta.
"Wata tauraruwa ce ta wuce sha kallo, shiyasa na tsaya kallonta saboda hankalina ya karkata a wajenta sosai, kar ki ga laifina don ban yi magana ba, ita ma ƙawarki na ga ba ta magana ko an yi mata wani laifi ne?" Inji Ibrahim yana tsare Lalla da ido, sai Farida ta ce
"Ni ma haka na ce big bro, na ga ta yi shiru ba ta ce komai ba,. Kar a zo dai wani ya yi mata laifi ne?"
"Haka take ai, ba kodayaushe take magana ba in dai Lalla ce." Cewar Fati tana hararen Hafsat na rashin gaishe da Ibrahim da ba ta yi ba. Ita kuma kallo ne ba ta so shiyasa ma ba ta ce komai ba amma gudun kar ta ɓata wa ƴar'uwarta rai, sai da ta tattaro jarumta sannan ta ce "Ba haka ba ne, mun wuni lafiya?"
"Haka ne mana, lafiya ƙalau muke"
Hello everybody 🙋, ya kuka ji labarin? To ya kuke ganin za ta kasance? Ku biyo sau da kafa za ku ji daɗin labarin da izinin Allah.
Ku biya nera 200 kacal domin cigabansa, in kin tashi siye ki tuntuɓi wannan lambar 👉+22784506476.
Real Nana Aisha 🥰
