Page 19

5 0 0
                                    

Zuwan Sani ƙanen Lawali unguwar ya yi wa Hafsat daɗi don ta samu ƴar'uwa a tare da ita, duk da ba su saba da Fatima ƴarsa don ba gari guda suke ba kuma sau ɗaya ne ta taɓa ganinta, zuwansu wani hutu a nan garin, amma ta ji daɗin ƙawar da ta yi mace kuma cikin gidansu. Kasancewar yanzu duk yayannunta sun girma babu mai yawo da ita a yanzu. Kodayake can ɗin ma ba wani yawo suke da ita ba amma ba kamar yanzu ba da suke ganin kansu samari da ƴan'mata ita kuma kwaila.

A lokacin Samaila  yana Niamey ya fara karatu a EMIG(Ecole de Mines de l'industrie et de la Géologie) saboda shekarar da ta wuce ya gama sakandari, ita kuma Saratu tana SS1 tare da yaran Hadiza. Shi yasa Hafsat ta ji daɗi kwarai da zuwan Fatima garinsu saboda a aji ba ta da ƙawa sai Nura shi ne abokinta, amma yanzu sai suka zama su uku saboda ita ma Fatima ajinsu ɗaya da Hafsat. Lokacin da babanta Sani ya kai ta makarantar ya bukaci a haɗe su aji guda saboda yana son su taso tare kuma wajen mai yi masu darasi a gida kar su sha wahala sosai. Wannan dalilin ne ya sanya aka kai Fatima ajin su Hafsat. Sannan tare suke tafiya su huɗu wani lokacin tare da yayan Fatima saboda shi sa'ar Nura ne don Nura ya ba Hafsat shekara biyu an sanya shi da shekara bakwai kuma ya yi zaman gida na shekara ɗaya. Amma kuma shi Misbahu yayan Fatima sakandari yake JS1 shi yasa bai wani tsaya tafiya tare da su wani lokacin cewa yake ɓata masu lokaci za su yi don su ba ɗaya suke ba a cewarsa.

💞💝💞💝💞💝💞💞💞

Bayan wasu shekaru abubuwa da yawa sun faru na daɗi da akasin haka. Ciki har da rasuwar iyayen Sulaiman da na su kakanin su Hafsat wanda duka babu wata tazara a tsakaninsu sosai.

Bayan an yi rabon gado sai ƴan'uwan Lawali suka bar wa iyalansa gidan kyauta don daman da su da iyayensu ne mallakin gidan. Sannan kusan duk wani bako da yake zuwa garin nan gidan yake sauka wannan dalilin ne ya sanya su ma bar masu shi don gidan ya sake isar su yadda ya kamata. Sai Hadiza ta koma ɓangaren iyayensu ita kuma Amina ta cigaba da zama a nata ɓangaren. Dayake ba yara ne da ita ba sosai ɗayan ɗakin wanda yake mallakin mai gidan nasu ne sai aka bar wa Samaila shi, ɗakin Hadiza aka bar wa Saratu da Hafsat da shi. Duk da a lokacin ma ana yi ta shirye-shiryen auren Saratu wacce har ta gama karatunta na likita don shi ta karanta bayan gama sakandari ɗinta.

Zawarawa masu kuɗi ƴan kasuwa da ƴan siyasa suna yi ta dakon son Amina da Hadiza saboda kasancewarsu fulani kuma ba su yada kansu ba suna kama jikinsu sosai duk da girma ya fara kama su, amma babu wacce take kula wani daga cikinsu don ita Amina ta ce babu wani auren da za ta yi, gara ta yi zamanta a haka har zuwa lokacin da za ta tafi inda ba a dawowa. Ita ma Hadiza ta ce babu auren da za ta yi shi yasa duk masu neman aurensu suka janye ba don ransu ya so ba sai don ba su ba su haɗin kai ba duk da akwai waɗanda ma suka ce sun amince za su dinga iske su har gidajensu amma a banza. Haka suka cigaba da zamansu sai ƴan sana'o'i da suke yi a cikin gida na kankara da zobo wanda suke samun kasuwa sosai. Wannan kenan

Suna ɗan taɓa hira da Sulaiman da yaransu ta talho da yake cikin gidansu, sama-sama suke gaisawa da ƴaƴansu waɗanda suke kiransu da Tanti don har kwanan gobe ba su san waɗanda suke haife su ba in aka cire uwar rikonsu wacce ita ce mahaifiya a gare su, kuma duk ɗaukar ƴan uku suke wa junansu. Wani lokacin Maryam har cewa take yi da mamarta "Mama me ya sa ni ba a sanya min Hassana ba sai su Hassan?" Dayake ba a kiransu da sunayensu na zane ko a takardar haihuwar da aka sauya masu Hassan da Hussaini ne, amma wancan ta farkon ita ce mai Lawali da Sulaiman. Sai dai mamarta ta yi murmushi ta ce mata "Saboda kina daban da su, kuma ke ta musamman ce, sannan kuma kina autata shi yasa na sanya maki wannan daɗaɗɗan sunan mai ɗadi da ma'ana sosai. Kuma kin ga su maza ne." Ita kuma Maryam sai ta yi ta jin daɗin wannan kirarin da aka yi mata na auta don tana jin daɗin hakan sosai a ranta, musamman mamarsu mace ta gari wacce ba ta da kyashi ko hassada balle ta nuna launiyar fata tsakaninsu da nata yaran don ba ita ce ta haife su ba. Ga shi kuma har yanzu ba ta sake haihuwa ba su ne autanninta ƴan uku.

      💞💞💝💞💝💞💝💞💞

A ɓangaren gidan Abubakar kuwa rayuwa tana tafiya yadda ake so, sai dai matsalar Asma'u kullum ƙarawa gaba take yi. Ibrahim ya fara girma wanda dole ta sanya ta daina dukansa. Bayan Ibrahim ya gama sakandari ya fara jami'a, sannan yana yawon zuwa gidan abokin babansa Hassan saboda yanzu yana da ƴancin yin komai don ya zama saurayi ba a dukansa sai dai baƙar magana da habaici wanda inda sabo ya saba da su tun tasowarsa, babbar ƙawarsa ita ce ƙanwarsa Farida wacce har kwanan gobe uwarta take hanata kula sa. Wani lokacin ma da sata zai ja Farida ya tafi da ita, ranar sai dai ta yi wa Farida ɗan banzan duka wanda ya tsorata Ibrahim har ya daina tafiya da ita. In ya tafi su yi hirarsu da mamarsa Saudat wacce wani lokacin in tana ba shi labarin rayuwarsu da Hajara mahaifiyarsa sai sun yi hawaye musamman shi da bai san mamarsa ba ya mance ta.
Haka zalika in ana wani shagali yana zuwa gidan saboda abokinsa ɗan gidan Saudat wanda suka taso tare a zamanin baya yana gayyatarsa, kuma in ya tafi yana jin daɗin tafiyar saboda yana haɗuwa da dangi sosai kama daga yara har manya.

Ibrahim  yana aji biyu a jami'a ya ajiye karatun jami'a ya tafi aikin soja don shi ne burinsa na rayuwa. A lokacin da ya tafi Farida tana aji biyar a firamari. A wannan lokacin tuni Farida ta gama fahimtar irin kiyayyar da mahaifiyarta Asma'u take yi wa yayanta Ibrahim. Ta gama gane ba mahaifiyarta ba ce ta haife sa, sai dai ba ta san waccece mahaifiyar Ibrahim ɗin sai dai ya faɗa mata ta rasu ko shi bai santa ba. Sannan ba ta san wani dangi na mahaifinta ba in aka cire kakanninta da suka rasu amma bayan su ba ta san wani ba, sai dai tana jin labarin uncle ɗinta da yake ƙasar waje amma ba ta san shi ba,don ba ta hirar da mamarta sai dai babanta. Akwai wani hutu Abubakar ya so Farida ta tafi garin da ƴar'uwarsa take aure amma ƙememe Asma'u ta hana a cewarta yarinyarta islamiya za ta yi ba za ta tura ta hutu ba kuma ba wani damuwa ta yi da zuwan nata islamiya ba amma yanzu don yana son ta tafi ziyara shi ne ta hana. Sosai Abubakar ya ji zafin abun nan har ma rigima suka yi sosai da ita, ta hana danginsa shigowa gidansa sannan kuma ta hana ƴaƴanta ziyarar danginsa wanda zafin abun da ya ji shi ne ya tunzura shi har ma ya daina yi wa Farida zancen wani nasa dayake yarinya ce nan da nan ta mance.

         💝💞💝💞💝💞💞

Lokaci yana tafiya shirye-shirye auren Saratu ya kankama wanda ake yi ta gadan-gadan ita da Ikilima ƴar gidan Hadiza wacce ita ma ta fidda mijin aure. Ranar auren ne wani babban al'amari ya faru da gidan Hassan inda matarsa da ƴaƴansa duk suna gidan biki shi ma ya dawo gida ne zai ɗaukar wani abu, ashe an ɗauke wuta ba su kashe kayan kallo ba. Yana zuwa gidan aka maido wuta da ƙarfi wanda ya hadassa gobara mai tsanani wacce ta sanya Hassan ta ƙone sosai, sannan babu abin da suka fita da shi daga gidan komai kone shi ma don yana da rabon kwana gaba ne. Amma an fi shekara ana jinyarsa kuma yadda ƴan'uwansa suke yi masa jinya haka Abubakar yake wuni a asibiti ma da jikin yana tsanani tare da shi ma ake kwana a asibitin. Sannan kuma gidansa ya mallakawa Hassan inda suka tare a can kuma ana jinyarsa a asibiti. A lokacin ne aka sake sanin juna tsakanin Abubakar da Malam Siraji mahaifin Nura wanda shi ma yana zuwa dubiya lokaci zuwa lokaci. Wannan abun da Abubakar ya yi wa Hassan shi ya sa yake da ƙima sosai a idanunsa wanda yake jinsa tamkar Sani da suka fito ciki ɗaya. Ba zai taɓa manta alkairi ba shiyasa duk wani abu na taimakawa shu ma yana yi wa Abubakar shi ba don ya biya shi ba sai don kyautatawa.

💞💝💞💝💞💝💞💞

Yuni, 15th 2009

Duk wani ɗalibi da ya zana jarabawar fita daga kwaleji yana cikin fargabar jiran sakamakon saboda kowa yana da labarin gobe ne za a fitar da sakamako. A wannan lokacin in ka ga Hafsat sai ka zata rashin lafiya ne ta yi don wata irin rama ce ta yi ta ban mamaki, duk sun rame su uku ɗin don sosai suka yi karatu irin waɗanda ba su taɓa yi ba. Duk wanda ya shigo gidan su Nura zai gan su samansu allo suna exercise su uku, ko kuma suna hanyar makaranta. A ranar kusan dukkan su babu wanda ya yi bacci saboda tunani da fargaba duk da suna karatu amma dai fargaba ta hana su sakewa. Washegari aka fitar sa sakamako kuma duk sun samu. An yi murna an yi shagali sannan suka fara shirye-shirye wata jarabawa ta shida wata babbar makaranta inda a can suke sa ran ƙarasa sakansari ɗinsu.

LALLA HAFSATOù les histoires vivent. Découvrez maintenant