Page 6

11 3 0
                                    


             Shafin kyauta na shida

Bayan kwana biyu da yamma Lalla tana waya ita da Nura cike da jin daɗi, haɗe da musayar kalaman soyayya masu matuƙar tasiri a zukatansu. Sai take jin alamar ana kiranta ga wayar ba ta dago wayar ba balle ta duba don ba ganin komai ake yi ba saboda ba a gyara wayar ba har yanzu.  Kawai ta basar ne saboda koma dai wanene ba katse kira za ta yi ba tunda dai tana hira da mahaɗin rayuwarta. Sai da Nura ɗin ne yake cewa
"My baby kamar ana kiranki a waya fa?"
"Ko ma dai wanene ba katse kiran Ruhina zan yi ba saboda shi, don kiran ba mai muhimmanci ba ne saboda ba daga gida ba ne ko kai." in ji Lalla.
"Kuma fa haka ne fa gimbiyata." Cewar Nura.
"Yes sadaukina ashe ka gane." In ji Lalla.
"Ni kuwa na gane ƴan'matana." Cewar Nura. Haka suka ci gaba da hirarsu har sai da suka shafe fiye da awa guda suna waya sannan Nura ya yi mata sallama saboda ya ce zai tafi gidan mota ya siyo tikita don gobe da safe zai yi asubanci ya dawo gida kasancewar yau da safe ya zana jarabawar da ya zo yi.

Tana sauke wayar daga kunnenta sai ga wani kira, ta zata ma Nura ne ya sake kiranta ko ya yi mantuwa bai faɗa mata wani abu ba, sai ta ɗaga kiran cikin muryar shagwaɓa tana cewa
"My Nur ka yi mantuwa halan?"

Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya Ibrahim ya sauke jin muryarta kaɗai da ya yi saboda yana cike da kewarta tun shekaranjiya rabonsa da ita da ya sauke su a gida, ya so ƙwarai ya ji muryarta amma babu damar hakan saboda ba shi da lambarta, shi ne ya samu Farida da maganar ta ce masa ta san yadda za a yi, ya ba ta awa guda za ta nemo masa lambarta amma dai ya fara ba ta lambar Fati sannan, bai yi mata musu ba ya ba ta lambar Fati sannan ya tsaya jiran tsammani. Ai kuwa take ta kira wayar Fati bayan sun gaisa ta gabatar mata da kanta suka sha hira sosai sai da za su sallama ne sannan ta buƙaci lambar Lalla don ita ma tana son ta kira ta a fara zumunci, ba ta kawo komai a rai ba ta ce mata za ta turo mata ta message. Babu ɓata lokaci bayan sun gama wayar Fati ta tura mata, sai ta yi masa forward ɗin lambar. Shi ne ya fara kiranta amma kuma ya ji tana waya wacce bai san lokacin gama ta ba saboda awa guda ce da wani abu suka yi amma gani yake yi sun fi shekara suna yi saboda yadda zuciyarsa take tafarfasa, wani irin kishi ne ya ziyarce sa lokaci guda wanda bai taɓa sanin yana da shi ba sai wannan lokacin, lallai soyayyar Lalla ba ƙaramin kamu ta yi masa ba a lokaci guda cikin abin da bai wuce kwana biyu ba, gaskiya ya yarda *Soyayyar gaskiya*(Littafin Real Nana Aisha) ce yake yi mata, lallai sai ya yi da gaske wajen kutsa kansa cikin rayuwarta don da alama wannan saurayin nata ya jima suna soyayya da shi, sannan ya san ba kowa ba ne zai kira ta su yi daɗewa haka kamar shi tunda ga shi yanzu tana ɗaga kiransa ta kira sa da sunansa.
"My heart lafiya ka yi shiru kuwa, ko ba ka gaji da jin muryata ba ne?" Ta katse masa zancen zucin da yake yi ta hanyar ƙara magana don ita duk a tunaninta ya dawo ne ya tsokaneta don sun saba duk da haka a cikin soyayyarsu ba su wani ɓoye-ɓoye.
Sai da ya tattaro jarumta saboda ta riga da ta gama da shi, don muryarta wani yanayi take sanya shi mai wiyar fassarawa, sosai yake jin daɗinta fiye da tunanin mai karatu sai ya ce
"Tabbas ban gaji da jin muryarki ba don tana tattare da wani sirri wanda ba kowanne mutum ne ya san da shi ba, sai ɗaiɗaiku a cikin..."
"Ya Salam! Wanene kai?" Sai ta yi saurin ciro wayar daga kunnanta don ta ga wanda yake kiranta saboda ko kaɗan wannan ba ta yi kama da muryar Nura ɗinta ba, sai dai kash! Ta manta da wayar ba a ganin komai, sai ta  danna wa wayar lasifika don sosai ta ji tsoron jin muryar wani ba ta Nuranta ba.
"Tauraruwa lafiya kike dai ko?" Shi ne abin da ta ji an ce cikin wayar.
" Da wa nake magana?" In ji Lalla.
"Mijinki ne to be in sha Allah." Aka faɗa a ɗaya ɓangaren.
"In ma mafarki kake yi tun wuri ka farka,wanene kai? Ko ka faɗa min wannene kai ko kuma in kashe wayata." Cewar Lalla a ɗan fusace kamar za ta yi faɗa sai dai ba wani faɗa ta iya ba kawai burga ce irin tata wai don ya faɗa mata ko shi wanene, sai ya ce
"Ba sai kin yi wahalar tambaya ba, ni ne nan wanda kika yi wa sata kuma kika tsere, sannan kuma uban ƴaƴanki masu zuwa"
"Gaskiya ka yi ɓatan lamba Malam." Lalla ta ce hakan tana kashe wayarta don ita ba ta jin za ta iya waya da wani yanzu ba, ta fi ma tunanin ɓatan lamba ne ya yi don ba ta da wani saurayi face Nura ba ta cikina masu takarcen samari ɗin nan, sai kawai ta ajiye wayar haɗe da tashi ta yi wanka don a gajiye take sosai, dayake jiya sun yi dinner kuma sun jima ba su yi bacci ba, shi ne yau ta sha bacci sosai kuma wayar da ba ta samu damar yi ba da Nura ba ce jiya da dare ita ce suka yi yanzu da yamma saboda yau da safe bai samu damar kiranta ba yana jarabawa.
Kuma yanzu ma gidan amarya za su tafi ita da Fati saboda an ce sai sun je yi wa abokan ango girki, kuma sun yi zamansu gida har ƙarfe biyar ta yi masu ba su shirya ba abin da ake tafiya tun da azahar. Ta tashi ta wuce kuryar ɗakinta ta ƙara jin ƙarar wayarta saboda ba a fasa kiran ba, kira yake yi ba ji ba gani don burinsa ta ɗaga wayar, ita kuma ta yi banza da wayar ba ta dawo ba don ta san ba Nura ba ne kuma ba Fati ba ce, sai kawai ta yi gaba a cewarta tana da aikin yi gabanta. Cikin abin da ba zai wuce minti talatin ba ta shirya sannan ta ɗauki wayoyinta ta saka a jaka sannan ta leka ɗakin mamarta tana cewa
"Maman za mu tafi gidan amarya wajen girki."
Hajiya Amina mahaifiyar Hafsat ta ce
"Ikon Allah! Ki dai ce kun tafi cin abinci amarya, amma masu girki ai sun gama yi yanzu fa karfe shida ta kusa yi."
"Wallahi mama ni dai na gaji sosai, in bn da abun angayen ma, yaushe rabon duniya da wani zancen a yi masu girki amma don su ba mu wahala ne suka ce sai mu zo."  In ji Lalla Hafsat tana yamutsa fuska.
"Ko ma dai minene ai ku na gida ne,ya kamata ku je da wuri, ba ruwana ai ku da..."
"Assalamu alaikum masu gida." Sallamar da Fati ce ta rafka ita ta hana mama damar ƙarasa maganarta tana amsa sallamar, sai Fati ta gaishe da mama sannan ta kalli Lalla haɗe da cewa "Na zata ai ba ki shirya ba."
"Na isa in ƙi shiryawa in sha azalzala wajen besty." In ji Lalla.
Fati ta yi murmushi haɗe da cewa
"Mama mun tafi wajen girki, sai mun dawo."
Hajiya Amina ta ce
"Ai ke ce girki ɗin! Yau ku da ɗiyata kam, na san sai kun sha ƙorafi "
"Ashe dai mama ma ta san halin ƴarta amarya, kin ga besty mu tafi." Cewar Fati tana murmushi.
"Allah Ya kiyaye hanya yarana, a kula da kyau don Allah kar ku yi dare kun ga adedeta sahu wahala take yi daga zaria zuwa Ali ɗan tsoho in dare ya yi, kar ku wuce sallar isha'i don Allah." In ji Hajiya Amina saboda ta san suna iya tsayawa har sai abokan ango sun zo sun zuba masu abinci, kuma ga shi nesa suke kar su yi dare kuma unguwar tasu sai a hankali in dare ya yi.
"In sha Allah mamata ba za mu yi dare ba, sai mun dawo." Hafsat ta ce suna yin gaba zuwa ƙofar gida.

💝💝💝💝💝💝💝💝💝💝

Tun lokacin ya sake kiranta ba ta ɗaga ba wayar ba, ya ji babu abin da yake son gani sama da ita saboda ƴar maganar da ta yi masa ta yi tasiri a zuciyarsa, kuma yana son ya zo ya kawo mata waya da ya siye mata sabuwa kalar wacce ta lalace, tun da ya ce zai gyara mata ta ƙi shi ne ya siyo mata kalarta saboda ya ga wayar tana da kyau, ya so ya siyo mata babbar waya sai dai kawai ya yanke shawarar har zuwa gaba in komai ya daidaita don bai son ya fara nuna mata yana da kuɗi ko kuma ya siye ta saboda kuɗi, ya fi son ta so shi tsakani da Allah kamar yadda yake sonta.
Shi ne ya tashi nan da nan ya shirya ya taho gidansu don kawai ya ganta ko zai ji daɗi a ransa, yana faka motarsa kofar gidansu sai ya fito don neman yaron da zai aika ya kira masa ita.

Fitowar Ibrahim daga mota ta yi daidai da fitowar su Hafsat daga cikin gidansu. Wata faduwar gaba ta ziyarci zuciyar Lalla, wani ras gabanta ya faɗi sai da ta razana ta fara kwakwanton anya wannan mutum ne kuwa? Ko dai shi ne ya kira ta yanzu? Kai wannan akwai jaraba wallahi, na tsani jaraba ko ma me ya kawo shi gidanmu ne a daidai wannan lokacin, ai kuwa in bai yi da gaske ba zan koya masa hankali don na tsani shishigi da shiga abin da bai shafi mutum ba, kar ya je ya ja mani zargi a wajen Nura, saboda yana nan tafe gobe ya ɗauka na fara cin amanar soyayyarmu har na fara kula wani daga tafiyarsa ta kwana biyu kacal.

Sai ta yi kamar ba ta gan shi ba ta wuce gaba abun ta har ma tana shirin wuce sa, sai da Fati ta taɓo ta tana cewa
"Ba ki ga mun yi bako ba ne? Ko ba ki gane sa ba ne?"
"Ban kula da shi ba" Cewar Lalla cikin halin ko in kula, don ta fara jin haushin wannan mutumin kwana biyu da fara haɗuwa da shi amma har ya fara sanya mata ciwon kai, ina dalili ina ɗan mafari? Gaskiya ta yi kuskuren sake neman wayarta saboda nacin da ya fara yi mata tun yanzu. Dawowa da baya ta yi ta a gaishe sa ba yabo ba fallasa kamar an yi mata dole saboda ta fara jin haushinsa, sannan ta ce da Fati da take yi hira da Ibrahim kamar wacce suka jima da sanin juna ita da shi.
"Besty kar fa dare ya yi mana."
"Ku shiga mota in sauke ku" Cewar Ibrahim yana yi mata kallon ƙasa-ƙasa.

Wani kallon an ya ka san da wa kake magana Hafsat ta watsa wa Ibrahim saboda ganin shishiginsa yana fara yin yawa, kuma yana son shiga rayuwarsu, ita ina ma za ta yi kuskuren shiga motarsa a cikin unguwarsu? Ko ranar ma da ya kai su ɗaukar amarya don yana dare ne kuma ba cikin unguwarsu ba shiyasa ta shiga, shi ne yau ma zai fara cewa ta sake shiga? Har abada ba za ta dake kuskuren shiga motarsa ba saboda ganin da ya yi ran nan ta shiga shi ne yake son yau ma ta ƙara shiga motar, ba da ita ba wallahi ran nan ta shiga amma yau kam sai in Fati za ta shiga ita daya amma ba da ita ba. Sai ta ce da Fati
"In kin gama hirar ki iske ni bakin hanya, in kuma na samu adedeta sahu ki iske ni can". Ta ida maganar tana yin gaba abun ta, duk da kallo suka bi ta daga Ibrahim har Fati, suna mamakinta na wannan dizgawar da ta yi masa saboda ya ce zai taimaka ya rage musu hanya.. kodayake ita Fati ta gane abin da ya sa ta ƙi shiga motarsa saboda mutanen unguwarsu kar wani ya ganta ya fada wa Nura saboda ta san yadda suke kishin juna da shi, ko kuma a gan su tsaye a yi zaton wajenta ya zo tun da yana ƙofar gidansu.


200 kacal yake ki tuntuɓe wannan lambar domin ƙarin bayani +22784506476

Real Nana Aisha 🥰

LALLA HAFSATOù les histoires vivent. Découvrez maintenant