Wani kallon tuhuma Fati ta yi wa Nura tana mamakin ƙarfin hali irin nasa. Mamaki maganarsa ta ba ta duk da ta jima tana zargin da son Hafsat a zuciyarsa amma ya ce babu. Sai dai tun ba a je ko'ina ba har ya fara nuna son nata a fili. Lallai dole ne ta yi wani abu a kai kafin wani ya yi masa kwace har zuciyarsa ta buga.
Sake magana ta yi don ta ƙara gazgata zarginta gare sa ta yadda za ta ɓullowa lamarin tana mai cewa
"Ji min mutum da katsalanda! Kai ne Lalla Hafsat ɗin ne?"
Shi kam Nura ko a jikinsa don hakan da ya yi gani yake shi ne kawai mafita a gare sa na yadda zai kare ƙanwarsa daga faɗawa tarkon samarin makaranta a cewarsa. Abun da bai sani ba kishi ne yake ɗawainiya da shi da soyayyarta wacce ta yi masa mumunan kamu, wacce bai san ranar da ya kamu da ita balle ranar da ya fara kishinta ba.Jin abin da Fati ta ce masa ne ya sanya shi kallonta haɗe da cewa
"Ni da ita duk ɗaya ne! Ga ta nan ki tambaye ta. Don na amsa tambayarta ai ban yi laifi ba"
Ya idasa maganar yana kallon Hafsat wacce take kallon dramar Fati da Nura, don daman sun saba wasa ita shi wani lokacin. Murmushi ta yi tana cewa
"Maganarka gaskiya ce ƙanena."Saurin kallonta Fati ta yi tana mamakin furucin Hafsat, wannan al'amari nasu yana ba ta mamaki. Kar dai wasa suke yi mata da hankali suna soyewarsu a ɓoye ba tare da ta sani ba. Sai suke yi mata zancen ba soyayya suke yi ba. Amma in ba haka ba ta ya Hafsat za ta ce haka? Duk da ta sha goya masa baya in suna rigimarsu ta wasa amma na yau ya sha bamban da na kullum. Kawai sai ta basar da wannan tunanin da yake ranta sannan ta ce
"Ai shikenan! Allah Ya ba da zaman lafiya!"
Saurin kallonta suka yi suna mamakin addu'arta wacce sam ba su fahimce ta ba, balle ma har su amsa da amin. Babu wanda ya ce da ita kala a cikinsu, sai da ta sake magana sannan ne Nura ya tanka mata inda take cewa.
"Ya ban ji kun amsa da amin ba?"
"Addu'ar ce ba mu fahimta ba." Ita ce amsar da Nura ya ba ta.
"Ah to gane min hanya." Cewar Hafsat.
"Ba zu fahimta ba yanzu. Kawai ku ce amin a wuce wajen."
A haka suka ƙarasa gida suna tafe suna hirarsu kamar yadda suka saba.
💝💞💝💞
Ya karanta wannan sakon da aka turo masa mintuna goma sha biyar da suka wuce, ya fi a kirga amma bai fahimci komai dangane da sakon ba saboda abubuwan da sakon yake kunshe da su suna barazar tarwatsa masa ƙwaƙwalwarsa da tuninsa har ma da zuciyarsa wacce yake jin bugunta da sauri-sauri. Mamaki ya kama shi sosai na abin da aka rubuto masa.
Yau sam bai fahimtar French saboda da shi aka rubuto masa sakon. Gani yake da a ce da Hausa ne aka yi masa da zai fi fahimtar abin da aka rubuta. Gani yake yi wannan farasancin ya yi masa tsauri. Gani yake wannan farasancin ba irin na ƴan Nijar ba ne. Da a ce nasu da tuni ya fahimci wani abu a cikinsa.
Ya sake buɗe wayar yana karantawa ya fi sau adadi, amma ƙwaƙwalwarsa ta cushe, tunaninsa ya tsaya cak, bugun zuciyarsa ya tsananta fiye da yadda ya fara da farko. Sake buɗe sakon ya yi yana karantawa, ganin zai ɓata wa kansa lokaci akan abin da ba zai fahimta ba sai kawai ya yi kiran lambar wacce ta rubuto masa sakon.
Bugu uku ta ɗaga don ta san za a rina sai ya kira ta saboda abin da ta rubuta masa ɗin don ta san da sanin sai ya kira ɗin shiyasa ma ba ta yi nesa da wayarta ɗin ba, ko da ya kira sai ta ɗaga.
" Ban fahimci komai game da sakonki ba Fati." Shi ne abin da ya ce mata a farkon fara maganarsa.
"Daman na san ba za ka fahimci komai ba Nura."
Cewar Fati daga ɗaya ɓangaren kasancewar ita ce ta rubuto masa sakon yana son Hafsat bai sani ba ko kuma suna soyayya da Hafsat ne sun ɓoye mata."Ban gane ba." In ji Nura.
"Daman na san ba za ka gane ba." Fati ta ce tana dariya a ɓoye.
"Ya kamata mu ajje wasa gefe mu yi magana ta fahimtar juna don Allah." Cewar Nura don sosai abin da ta ce masa ya ba shi mamaki.
"Okay Nura!
Maganar gaskiya ce na faɗa maka a cikin sakon. Duk abin da na ce maka ina da tabbacinsa don ni na jima da fara sanin sirrin so shi ne dalilin da ya sa na fahimci halin da kuke ciki. Kana son besty son da ba ka san ranar da ya shiga zuciyarka ba. Kana kishinta kishi mai tsanani don haka ya kamata tun kafin a yi maka tufkar hanci ka yi wani abu a kan soyayyar da kake yi mata. In kuma har ka bari Hafsat ta fara kula wani namiji to ina mai tabbatar maka da za a iske ka zuciyarka ta buga. Soyayyar da take tafe da shakuwa tana da matuƙar daɗi in har an dace, sannan kuma tana matuƙar bayar da wahala lokacin da aka rabu ko kuma aka yi nesa da juna."
Ƙasa cewa komai Nura ya yi don shi sam bai san da wani abu wai shi so ba. Bai taɓa soyayya ba balle ma ya san so. Amma ita Fati ina ta san wannan jawabin da take yi masa? Wa ya koya mata wannan abun? Yarinyar da ba ta wuce shekara sha bakwai ba. Mamaki yake ina ta san waɗannan maganganu da shi bai sani ba game da soyayya?
Kasa magana ya yi saboda bai san abin da zai ce mata ba sai faman saurarenta yake yi kawai. Amma wani irin bugu yake jin zuciyarsa tana yi masa wanda bai taɓa jin irinsa ba tun da yake, sosai zuciyarsa take bugawa da sauri da sauri.
Ganin da Fati ta yi bai ce da ita kala ba sai ta ce da shi
"Ka nemi malaman soyayya su fahimtar da kai. Ina yi maku fatan alƙairi"

VOUS LISEZ
LALLA HAFSAT
Storie d'amoresoyayya, son zuciya, son maso wani, kaddara, tsaka mai wiya, dss