Page 16

7 1 0
                                        

Yau Lawali ya zo wa mamarsa da daɗaɗɗan albishir a kan ya biya mata aikin hajji ta tashi su tafi wajen masu gyare-gyaren hoto da passeport. Yake faɗa mata har ma babansu yana can daga wajen aiki shi ma Hassan ya biya wa masa kuma har ya tafi da shi. Murnar wajen iyayen nasu ba a magana duk da Samaila ya taɓa zuwa amma sosai ya ji daɗin wannan biya masa hajjin da Hassan ya yi._
_Haka suka yi ta shirye-shiryen tafiya hajji babu kama hannun yaro. Ko da lokacin tafiya ya yi suka tafi can TOROƊI wajen dangi suka yi wa danginsu bankwana, su uku suka yi tafiyar har da Lawali wanda shi a wajen  aikinsu ne aka biya masa hajjin saboda kwazonsa, shi ne sai ya biya wa mamarsa da abin da yake da a hannunsa wanda yake tariya. A haka suka tafi hajji sai dai suka kwashe wata guda a can sannan suka dawo, kuma ta Toroɗi suka biya dayake a Niamey jirgi yake sauke su,shi ne suka tafi can don kar su ba wa mutane wahalar zuwa gaishe su shi ya sa suka biya can ɗin, suka ba mutane ƴar tsarabar da suka taho da ita.  Sosai mutane suka yi ta taya su murnar aikin hajjin da suka yi a lokacin da za su dawo ne suka taho da Hadiza wacce ta kasance ƴa a wurin yayan Samaila, zawara ce ita mijinta ya rasu ya bar ta da ƴaƴa biyar. Sun taho da ita ne don ta ringa taimaka masu da wasu ƴan ayukkan duk da dai ba su da matsala da matar Lawali da suke gida guda da ita, tana yi masu komai amma dai saboda su rage mata aiki suka taho da Hadiza har zuwa lokacin da za ta samu wani mijin ta yi aure tunda da karfinta yanzu ne ta yi wa ƴarta ta farin aure.

Bayan sun dawo da wasu watanni, sai zancen ya sauya soyayya ta shiga tsakanin Lawali da Hadiza duk da ya yi gudun hakan sosai saboda matarsa babu abin da ta rage masa da shi, amma sai da SO ya darsu a zuciyarsa game da ita saboda SO babu ruwansa da neman izini ko shawara,wani lokacin kyakyawan ɗabi'a ne suka sanya shi darsuwa ɗin,wanda abubuwan da Hadiza take yi wa iyayensa ne yake gani yana yabawa shi ne har sai da so ya shiga  zuciyarsa. Tun yana ɓoyewa har ya zo ya fara fada wa mahaifiyarsa abin da yake ji game da Hadiza,. Ita kanta abun ya ɗaure mata kai sai dai ba a jayayya da ikon Allah. Ta yi wa abun addu'a sannan ta faɗa wa mijinta shi ma dai fatan alkairi ya yi wa lamarin sannan da kansa ya faɗa wa Amina zancen auren da Lawali zai yi da Hadiza a kan ta yi haƙuri ta rungummi auren, wata kaddara ce ta rayuwa ta zo masu a hakan. Sosai kishi ya turkune Amina sai dai ta yi kokari sosai wajen ɓoye shi ta yi addu'ar fatan alkairi saboda kasancewarta mace ta kwarai mai biyayya. Sai a lokacin ne ake faɗa wa Hadiza ɗin amma ta nuna ba za ta taɓa auren Lawali ba saboda in har ta aure sa ta yi wa matarsa butulci na auren mijinta ita kam ba da ita wannan abun kunyar ba, tana zaune gidansu ta rasa sakayyar da za ta yi mata sai ta auren mijinta. Duk da tana da burin auren mutum irin Lawali amma ta ce sam ba za a yi wannan abun da ita ba, sai da Amina ɗin da kanta ta yi mata magana sannan ta amince sai ga shi nan da nan soyayya ta shiga tsakaninsu har aka saka ranar aure aka ɗaura aure amarya ta tare a gidan.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya suna zaman su cikin zaman lafiya sai dai babu mai haye wa wani don gudun tashin hankali tsakaninsu. A haka suka samu ciki kusan lokaci guda. Sosai Lawali yake ba su kulawar da ta dace. Sai dai babu wacce Lawali ya ga ɗan da ta haifa a cikin su don cikin Amina yana da wata bakwai ita kuma Hadiza nata  yana da wata takwas Lawali ya kamu da ciwon ciki mai tsanani wanda take bugu guda ya yi masa ya rasu. Wannan mutuwar ta girgiza mutane da dama sosai suka sha kuka. Sulaiman amininsa ya sha kuka gabadaya da iyalansa ya zo wajen ta'ziyar amininsa yana yi ta kuka kamar ƙaramin yaro wanda sai da aka wuni ya samu labarin mutuwar. Babu ɓata lokaci ya kamo hanya ya taho yana yi ta kuka,ko a hanya cikin mota kuka yake yi sai matarsa ce take ba shi haƙuri, faɗi yake shi da matan Lawali ne aka yi wa wannan mutuwar musamman in ya tuna yadda suka taso a tare suka gudanar da rayuwarsu kafin su fara aiki zama ya raba su. Wannan abun in ya tuna shi yake sanya shi kuka sosai. Haka aka cigaba da zaman makoki har zuwa lokacin da aka yi sadakar kwana uku sannan mutane suka fara ragewa aka bar sai ƴan gida kawai, Sulaiman da iyalensa kam nan gidan suke wuni har kusan sati da rasuwar. Sai dai aka fara kiransa wajen aiki ne sannan ya fara shirye-shiryen komawa bakin aikinsa amma har zuwa lokacin bai daina kukan rasuwar amininsa ba. Kafin ya tafi ya yi wa matansa alkawari in har sun haihu yana so daga sun yaye yaran da suka haifa ya ba su zai zamar musu uba kamar yadda Lawali zai yi. Duk da suna son kula da abin da za su haifa amma haka dai suka amsa da to don yi masa kara. Ya yi murnar  da yadda suka amshi bukatarsa sannan ya koma bakin aikinsa.

Lawali yana da wata ɗaya da kwana goma Hadiza ta haihu ƴan biyu duka maza, sosai suka yi murna da haihuwar. Sannan kuma sun sha kuka sosai saboda  tunawa da Lawali da suka yi, ga shi ya tafi ya bar iri har na ƴaƴa biyu amma bai gani ba, ga kuma cikin Amina da ba a san ko minene a ciki ba. Ranar suna ƴan biyu suka ci sunan Lawali da Sulaiman wanda Babansu ne ya yi wa yaran huɗuba da sunayen saboda yi wa Sulaiman kara da kuma tunawa da Lawali. Wannan sunayen da aka sanya masu sosai Sulaiman ya yi murna da hakan har yana ɗaukar yaran yana rungummewa saboda tsantsar ƙaunar da yake ji game da su kamar shi ne ya haife su, shi yake ya matsu a yaye su ko a ba shi su don ya yi alƙawarin kula da su har karshen rayuwarsa saboda ba wani yara ne da shi ba duka yara uku ne matarsa ta haifa haihuwar ta tsaya mata duk da ba tsufa ta yi ba amma yanzu karamar yarinyarta shekararta shida, shi kuma yana son yara sosai musamman yaran amininsa wanda yake ji tamkar nasa.
Dayake lokacin hutu ne yana nan garin wajen hutu har Amina ta haihu mace wanda tserewa tsananinsu da Hadiza kwana ashirin da bakwai ne. Ita kuma ranar suna aka sanya mata suna Maryam. A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har hutun Sulaiman ya ƙare ya koma bakin aikinsa inda ya bar wa iyalen amininsa kayan abinci sosai wanda ya san za su jima ba su ƙare masu ba.

Kafin ya tafi sai da ya rubutu sunan Lalla Hafsat a wata makarantar gwamnati wanda ya so ya biya mata ta kuɗi don dai an hana shi a cewar Amina gara dai makarantar gwamnati saboda tsaro da halin rayuwa, bai yi musu ba duk da bai so ba amma ya rubuto ta sannan ya tafi kuma ya bar wa yayannunta kayan makaranta da duk wani abun amfanin yara ƴan makaranta, sosai suka yi masu godiya wannan hidimar da yake yi masu wadda ko wani ɗan'uwanka na jini albarkar abin da zai yi kenan.

LALLA HAFSATOù les histoires vivent. Découvrez maintenant