Page 8

4 0 0
                                    

A duk lokacin da ruwan sama ya sauka a gari kowa ya san yadda mutane suke son wannan yanayin mai cike da ni'ima, in har mutum ya fito waje zai ji daɗin fitar saboda wani ni'ima da take tattare da lokacin, musamman ga masoya suna jin daɗin wannan yanayin sosai wannan lokacin ma bayan an yi ruwan sama gari ya yi luf-luf gwanin ban sha'awa, a wani harabar wani gida mata da miji ne waɗanda daga ka kalle su za ka gane cewa waɗan nan masoyan sun gina rayuwarsu cikin so da ƙaunar juna, za ka fahimci zallar soyayya a tattare da su saboda yadda suke matukar son junansu kuma ko a gaban waye babu ruwansu da mutum nuna soyayyarsu suke yi. Suna zaune saman lilo mai matukar kyau da tsari, sai ka ce gidan Turawa ne saboda tsarinsa ya yi kama da nasu, daga ɗaya ɓangaren ga shuke-shuke nan na noman rani, salat tumatir, cabagge, albasa da sauran kayan marmani, dayan wani ɓangaren kuma wata ƴar karamar piscine ce mai kyau cikin gidan, sannan ga kuma itatuwan mangoro, gwaba, lemo, gwanda, da banana, dayake babban gida ne sai shuke-shuken suka yi wa gidan kyau sosai kuma suka yi tsari._
_A can tsakar gidan ga lilo kala kusan uku, yayinda yara biyu mace da namiji masu kimanin shekara biyar suke wasa  saman lilon ɗan sululu sun sha kyau gwanin ban sha'awa cikin kayansu na shan iska, kallo ɗaya za a yi wa yaran a fahimci ƴan biyu ne saboda tsantsar kamaninsu duk da ba jinsunsu ɗaya. Su kuma mata da mijin suna zaune suna hira kasancewar mijin bai aiki yau yana gida yana hutawa haɗe da ba wa iyalensa kulawa. Suna hira cike da so da kauna haɗe da musayar kalaman soyayya masu daɗin faɗa da kuma matukar tasiri a zukatansu, ba za a taɓa cewa su suka ajiye waɗan can yaran ba saboda kullum ba su tsufa kuma soyayyarsu kara linkuwa take yi a zukantan juna, matar ce ta yi magana tana cewa._

_"My jann!"_
_"Na'am my angel." Cewar Ibrahim yana kallon kwayar idanta masu matuƙar birge sa, sai ta ce da shi_
_"Ya kamata ka kai mu gidan Anna." Cewar matar wacce ba kowa ba ce face *Lalla Hafsat*_
_"Ya kamata dai mu je gidan Anna." Cewar Ibrahim yana kallonta. _
_"Na zata ba za ka tafi ba shi yasa na ce ka kai mu ai." In ji Lalla tana kallonsa._
_"Ya kamata ki daina tunanin ba zan je ba, saboda kin san matuƙar ina gida ban tafi aiki ba to babu abin da zai sanya ni barin ki tafiya wani waje ba tare da ni ba, saboda ke ce mahaɗin rayuwata uwar gidana kuma amaryarta, ina sonki ina matuƙar ƙaunarki ina fatan Allah Ya bar mu tare da ke har karshen rayuwarmu." Ibrahim ya faɗi haka yana shirin sauka daga saman lilo ɗin yana kallon Lalla da son jin abin da za ta ce masa_
_"Ko da rana ɗaya ba ni son in yi nesa da kai ni ma, da ace wajen aikinku za su ɗauki ni aiki da tuni na je neman aiki can saboda mu dinga tafiya tare muna dawowa tare da kai mahaɗin rayuwata, ina son...."

"Kon! kon! kon!" ƙarar bugun kofar dakin Ibrahim da Farid yake bugu da iya karfin da Allah Ya hore masa saboda ya tsani wannan mutumin duk da yana yayansa da suke uba guda, ga shi babansu  ne ya aiko sa kiransa ba zancen ya ce bai zuwa, shi yasa yana zuwa ya fara bugun kofar ba ji ba gani kuma da gayya yake yin haka don ya ɓata wa Ibrahim ɗin rai saboda in har yana baccin rana aka tashe shi ciwon kai yake yi, shi kuma abin da yake so kenan saboda ya ji haushin aiko sa da aka yi.

Cikin haushi Ibrahim ya tashi daga baccin da yake yi mai matuƙar daɗi saboda mafarkin masoyiyarsa da yake yi, ga shi wani ya zo ya katse masa baccinsa da mafarkinsa, ko ba a faɗa ba ya san wanene wannan da ɗanyan aikin, cikin fushi ya tashi ya fito yana buɗe kofar haɗe da kallon Farid da yake famar jijjiga kofar, daman ya san za a rina shi ne ɗin, kallon ammma ka raina min hankali Ibrahim ya yi masa sannan ya ce da shi
"Wani abu sai wanda bai waye! Me ya kawo ka ɗakina?"
"Sannu ɗan duniya wanda ya waye! tsiyar me zan nema a ɗakinka ba don an aiko ni kiranka ba?" Cewar Farid cikin fushi da fusata.
"In ban da kauyanci haka ake tayar da mutum daga bacci? Wallahi ka yi na ɗaya in har ka sake kuskuren aikata na biyu sai na yi mugun ɓata maka rai." In ji Ibrahim cike da taikacin katse masa baccinsa da Farid ya yi lokacin da yake mafarkin Lalla ɗinsa. Sai Farid ya ce
"Bisimillah ni da kai shege ka fasa a gidan nan."
"Na san me yake damunka yaro." Ibrahim ya yi maganar yana rufe dakinsa da ƙarfi, haɗe da komawa saman gado a cewarsa bari ya kwanta baccin ko zai ƙara mafarkin da yake yi saboda yana son jin Lalla ta ida maganar da ta fara yi masa a bacci. Sai dai ina! Duk rufe idon da yake yi amma shiru babu baccin da ya zo masa sai ma ciwon kai da ya zo masa na tashinsa da aka yi, sai jin ƙarar wayarsa ya yi tana neman agaji, bayan ya daga kiran sai ya ji muryar mahaifinsa yana cewa
"Soja har yanzu baccin kake yi?"
" A a babanmu ga ni nan tafe." Sai ya kashe wayar yana duba kiran da aka yi masa ya fi goma, mamaki ya kama sa na tunanin yaushe aka yi waɗan nan kiran bai ji ko ɗaya ba saboda wayar ba a silince take ba,lallai mafarki ya yi masa daɗi da har bai ji kiran wayar da aka yi masa fiye da goma ba. Sai ya fara tunanin ko dai wani abu ya faru a gidansu, ai da sauri ya faɗa toilet sharp-sharp ya yi wanka ya fito ko mai bai tsaya shafawa ba ya sanya doguwar riga ya fita zuwa baban falon gidan. Yana shiga da sallama a bakinsa ya iske su zaune suna cin abincin rana, gaishe da su ya yi sannan Farida ta gaishe sa ya amsa mata yana cewa
"Babanmu kowa lafiya dai ko?"
"Kowa lafiya ƙalau, kai ne dai Farida ta ce min ba ka da lafiya, abinci ma ka daina ci, shi ne ta ce na yi maka faɗa ko za ka koma cin abincin, shi yasa na aika kiranka, na kira wayarka ba ka daga ba." Cewar Alhaji Abubakar ya yi maganar tsakaninsa da Allah kuma ba da wata manufa ba ya yi ba ko kuma don ya ɓata wa Hajiya Sabira rai, don shi har yanzu tausayin Ibrahim yake yi na rashin samun uwar riko ta kwarai balle har ta ji damuwarsa da farincikinsa, da a ce mahaifiyarsa tana da rai da ita za ta matsa masa har sai ta ji abin da yake damunta, amma bai samu hakan ba sai dai kanwarsa ce take iya bakin ƙoƙorinta na ganin ta kula shi yadda ya dace.
Ibrahim kallon Farida yake yi yana mamakinta, lallai ma shi za ta yi wa haka don ya faɗa mata sirrinsa? Kar da a ce har zancen Lalla ta faɗa wa babansu? Kamar ta san yana kallonta sai ta ƙi daga kai ta kalle sa balle ma ya ce mata wani abu, sai cewa ya yi
"Babanmu wasa ne Farida take yi, ni Kullum ina cin abinci."
"Kai dai yanzu zauna mu ci tare da kai, Farida cika masa wannan filet ɗin, kai kuma ka tabbatar ka ba ni filet ɗin nan Kwango, ka ji dai na faɗa maka." Cewar Alhaji Abubakar.
"Ikon Allah! Shi Ibrahim ɗin ne ake matsa wa har sai ya ci abinci, ai shi ba yaro ba ne balle a yi masa faɗa ya san daidai ya san ba daidai ba." Hajiya Sabira ta faɗa tana tashi daga table ɗin don abun ya fara ba ta haushi a cewarta na fifita Ibrahim da Alhaji Abubakar yake yi fiye da sauran ƴaƴansa, wai har da wani cewa sai ya cinye abinci sai ka ce yaron goyo, lallai don ya samu dauri gindi daga wajensa ne shi yasa yake yin abin da ya ga daman yi, ita kuma wannan abun yana bakanta mata rai sosai wallahi, da tana da yadda za ta yi da tuni ta yi saboda ta gaji da wannan masifar ta Ibrahim, duk lokacin da zaizo hutu gidan ƴar kulawar da ake ba yaranta kanana sai ka ga ana ba shi ita, yanzu kuma ga shi wai Farida ce ta yi masa maganar rashin cin abincinsa, wai haɗa ma a yi masa fada sai ka ce yaron goye, ita ba don ta yi wa Farida baki ta zo daga baya tana nadama ba da tuni ta yi mata baki in har ba ta fita harkar Ibrahim ba.

Babu wanda ya ce kala a cikin su sai kowa ya yi shiru suna cin abincinsu, shi kam Ibrahim abubuwa da yawa ne suka sha masa kai, ga mafarkin da ya yi yanzu, ga tsanar da Lalla ta yi masa, ga kuma masifar Mama, sannan kuma ga abincin da aka ce dole sai ya cinye, kuma ya san ba zai iya ba saboda tunanin da ya yi masa yawa wanda shi ne musabbabin abin da ya hana shi cin abincin, ya san kuma don ya kwanta da tunanin zuwa gidan kawu ne shi ya sa ya yi mafarkin Lalla har sun yi aure sub haihu da ita ga kuma soyayyar da suke zubawa ita shi. Haka dai babu yadda ya iya haka ya fara cin abinci don ba zai iya yi wa babansu musu ba, amma jin abinci yake yi kamar magani don ba daɗinsa yake ji ba duk da kasancewarsa dambu abin da yake so amma yau kam sam jinsa yake yi kamar magani. Bayan ya ci wanda ya ishe duk kowa ya watse daga wajen cin abincin wasu sun yi ɗaki wasu kuma suna falo zaune, sai ya matsa kusan Farida yana cewa ta ara masa wayarta saboda bai fito da wayarsa ba, bayan ta mika masa wayar sai ya yi mata wani rubutu a cikin message, sannan ya tashi ya fita haɗe da cewa
"Kar ki buɗe ki bari har in fita don yanzu nake son a yi komai fa, in so samu ne ma da yamma fa."
Ya ida maganar yana fita daga falon,Samira sa Farid da suke zaune suka bi shi da kallo kowa da abin da yake sakawa a ransa.

Wani ihu Farida ta buga bayan ta gama karanta abin da Ibrahim ya rubuta mata a waya sai ta tashi ta ruga da gudu sai cikin dakin babansu tana cewa
"Babanmu Albishirinku !" Sam ba ta cikin hayyacinta saboda daɗin abin da Ibrahim ɗin ya ce mata ki mahaifiyarta da take zaune tare da shi ba ta kula ba da ita ma ta kawo masa zancen haɗin da take so a yi na Samira da Ibrahim, shi kuma ya ce ba zai yi wa Ibrahim dole ba saboda yanzu auren soyayya ma ana yinsa da yawa bai zuwa ko'ina don haka gara ya tambayesa in har ya amince to zai aura masa Samira in kuma bai yarda ba to sai dai ta yi haƙuri saboda shi ma ya san tana son Ibrahim ɗin. Shi ne sai rigima ta ɓarke tsakaninsu tana faɗa an nuna mata ba ita ce ta haifi Ibrahim ba tin da ta haɗa sa aure da ƴarta an hana. Kuma sai ga Farida ta shigo ɗakin tana faɗin albishir, duk kallonta suka yi suna sauraren abin da za ta ce , sai wayar ta mika wa Babansu bayan ya karanta sosai ya ji daɗin wannan labarin sannan ya ce ta tafi zai neme ta. Ba ta yi musu ba ta fita zuwa ɗakinta tana tsalle ita ɗaya. Kiran wayarsa ta yi tana cewa komai yana tafiya daidai ka yi ta addu'a da izinin Allah za a dace.

             💞💞💞💞💞💞💞💞

Da dare zuwa ƙarfe takwas bayan sallar isha'i a cikin harabar gidan su Hafsat, ita da Nura ne suke zance ksancewar gidan su Lalla ba shi da yawaitar mutane da yawa, shi yasa kullum in dai za ta yi hirarta da Nura suke yi cikin gidansu sai dai in har ba ya zo zance ba ne wani abu daban ya kawo shi. Ya zo ne suna tsara yadda za a yi ya turo magabantasa saboda jarabawar da ya yi bai samu ba,ci gaba zai yi da karatunsa na digirgir wato Doctorant saboda bai samu wancan ba, kuma ita babu yadda bai yi da ita ba a kan su tafi tare ita ma ta yi amma ta ƙi a cewarta gara su yi aurensu saboda ta fi matsuwa da shi saboda yadda samari suke sha mata kai daga kowanne ɓangare. Bai yi mata musu ba ya amince don shi ma yana son auren, shi ne ya zo suna zancen yadda zai kai kuɗi da kuma lokacin auren saboda duk yana da kuɗinsa Kasancewar yana koyarwa a secondry school can Niamey inda suka master ɗinsu ita da shi kuma ya tara kuɗin aure yana son har ya gama siyen kayan akwati sai a fara maganar aurensu. Sun yanke shawarar nan da wata uku in ya samu kuɗinsa zai kawo kuɗin ita kuma za ta fara neman aiki can Niamey ɗin su ga yadda za ta kasance. Daga su ci gaba da hirarsu har zuwa ƙarfe tara da rabi, bayan sun yi sallama ne ta shiga cikin gida sai ta iske mamansu zaune ta yi zungum kamar wacce aka aiko wa da sakon mutuwa saboda fuskarta kaɗai za ka kalla ka fuskanci tana cikin damuwa sosai. Cikin tashi hankali ta isa gare ta tana cewa
"Mamata lafiya? Me yake faruwa?"

Littafin kuɗi ne, in kina son cigaban labarin ki tuntuɓi wannan lambar +22784506476, an yi arha an hana bashi nera 200 kacal ne



Real Nana Aisha 🥰

LALLA HAFSATOù les histoires vivent. Découvrez maintenant