Page 1

46 5 0
                                    

🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼

🇦SSOCIATION🤝🏻


  Littafi na farko 📝

       Safi na ɗaya

Tafe suke saman mashin sai hira suke cike da nishadi, daga ka ga yanayinsu zai tabbatar maka da masoya ne, saboda yadda fuskarsu take cike da annuri kuma ga yanayin yadda suke tafiya sannu a hankali, duk wanda ya zo sai ya wuce su musamman hanyar da suka biyo, ba ta da mutane sosai shi ya sa ma suka samu damar yin hirarsu ba tare da wani hayaniya ba, a gaban mashin ɗin tsakanin saurayin da yake tukin mashin ɗin da kuma hannun mashin ɗin ƙaramar akwati ce ta matafiya. Suna tafe suna hira har suka kai inda za su tafi wato gidan bus , suna isa kuwa motar da za ta tafi daga Maraɗi zuwa Zandar har ta kusa tashi saboda har an fara kiran masu tafiya, dayake balaguro ne zai yi shi saurayin shi ne ta rakko shi inda zai shiga mota, don a cewarta ba za ta yarda wani ya kawo shi ba ita da kanta za ta rakko mahaɗin rayuwarta.
Cike da so da ƙauna budurwar ta kalli saurayin ta ce da shi " Yanzu nan tafiya za ka yi ka bar ni my lovely."
Shi ma cikin nashi salon ya ce da ita
"Ta yaya zan tafi in bar mahaɗin rayuwata? Ke ma kin san ba zan taɓa tafiya in bar ki ba, sai dai mu yi nesa da idanu amma kusancinmu ga zuciya kullum daɗa ƙaruwa yake don haka kin bar zancen zan tafi in bar ki"
Hafsat ta ce
"Na san kullum ƙara kusanci muke a zuciya, amma ba ni so ko rana ɗaya a ce mun yi nesa da juna da kai my Nour"
Ya ce
"Sorry my Hafsat kin san ba don zan zana jarabawa ba, da babu abin da zai sa in yi nesa da gida, in sha Allah jibi muna gamawa zan dawo gida kar ki wani damu kin ji tawan? Don haka ki yi min addu'ar nasara my weetheart"
Hafsat ta ce
"Addu'a wannan ta zama dole in yi maka ita rabin raina, fatana Allah Ya kai ka cikin aminci da lafiya, Ya kuma ba ka sa'ar jarabawa haɗe da sakamako mai kyau, sannan Ya maido ka cikin danginka lafiya"
Murmushi Nura ya yi haɗe da cewa
"Godiya nake gimbiyata, Allah Ya bar min ke ƴar uwata kuma mahaɗin rayuwata"
Hafsat ta yamutsa fuska haɗe da cewa
"Amin amin, amma me na ji ka ce? Kamar godiya na ji kana min kuma ka san babu godiya tsakaninmu"
Nura ya ce
"Godiya ta zama dole in yi maki ita Lallata"
"Ni da kai duk ɗaya ne hubbyna don haka bani bukatar godiya" cewar Hafsat, yana shirin cewa wani abu sai suka ji muryar mai kiran sunaye yana cewa
"Nura Siraj"
Saurin kallon shi suka yi a tare sannan kuma suka kalli junnansu, sai da aka sake kiransa don ana zaton bai kusa sai a lokacin ne ya amsa kiran yana cewa
"Na'am, ina zuwa"
Akwatin ya sauke daga saman mashin dinsa sannan ya sake kallon ta yana cewa
"Hubby ki saki fuskarki mana, so kike in tafi in bar ki cikin damuwa? Sannan kin san damuwarki damuwata ce don haka ki taimake ni ki sakar min kyakyawar fuskarki"
Feena ta ce
"Ko ɗaya ba zan so haka ba nawan, mu je na rakka ka shiga mota"
Bai yi musu ba suka yi gaba a tare wajen bus ɗin, ya shiga ciki yana waiwayen ta ita ma shi ɗin take kallo cike da so da kuma shaukin begensa, tana tsinkayensa ta madubi ta ga ya zauna, sai a lokacin ne ta dawo wajen mashin ɗin ta yi zaune saman sa tana jiran ta ga tashin bus din. Jakarta ta buɗe don ta ɗauki wayarta don tun suna saman hanya take jin ƙararta ita kuma a lokacin ba ta buƙatar wani kira don ta san da wiya in kiran mai muhimmanci ne tun da ba daga gidansu ne ba saboda ƴan gidansu duk ta san kalar tashin sautin kiransu, tana buɗe jakar sai ta ci karo da sakon da ta biyo masa da shi, sai a lokacin ta tuna ta yi mantuwa ba ta ba shi ba, wata chocolate ce ta siye mashi kuma sai ta manta, ko jakar ba ta gama rufewa ba cikin sauri ta yi wajen bus ɗin har tana yada ɗayar wayarta karama wajen ciro ledar daga cikin jaka, ba ta kula ma da ta yada wayar ba don cikin sauri take kuma ita dai burinta shi ne ta ba muradinta chocolate ɗin, tana isa wajen bus ɗin ta ce da mai kiran sunaye 
"Don Allah ina son in ba wanda na rakko sako, na manta ban ba shi ba sai yanzu da na buɗe jakata ne na kula da haka"
Ya ce da ita
"Babu damuwa amma kar ki jima don mota ta kusa tashi"
"Ba zan jima in sha Allah, na gode sosai" cewar Hafsat, tana shiga cikin bus din, nan da nan idanuwanta suka hango shi zaune a kujera kusa da wani namiji ya duke kansa ƙasa, ta yi sauri isa wajensa tana cewa da shi
"Ji mana samari! minti biyu" ta yi maganar da murmushi a fuskarta, cikin sauri ya dago fuskarsa saboda ya ji muryar sanyin idaniyarsa, shi ma murmushin ya sakar mata haɗe da cewa
"Kin fi ƙarfin a ba ki mintin biyu gimbiya saboda ya yi maki kaɗan"
Cikin shaukin so da kaunar sa ta langaɓar da kai, kamar su kaɗai ne a wajen tana cewa
"Godiya nake ɗan'uwana, dama ka yi mantuwa ne a cikin jakata shi ne na biyo ka da ita, Allah Ya sa ma motar ba ta tashi ba, da ba zan ji daɗi ba"
Kallon ta ya yi yana murmushi don shi ya ɗauka ma zolayarsa ce take yi, don bai san da wata ajiya ba a cikin jakarta ba, sai da ya ga tana miko masa wani leda mai kyau irin ta Alimentation, sai a sannan ya ce da ita
" Me kuma na manta acikin jakarki ƴan matana?"
Ta ce da shi
" Ni ma na buɗe jakar ne na ga kayanka ciki" ta ida maganar tana mika masa ledar, da murmushi a fuskarsa ya amsa yana cewa da ita
" Na g..." Bai ida maganar ba ta wurga masa wani kallo mai kama da hararen wasa, ko kuma wanda masoya za su kira da kallon ƙauna, sai ya yi murmushi haɗe da saurin cewa
" Ba fa cewa zan yi na gode ba, cewa ne zan yi na ji daɗin da kika tuna min da mantuwata"
"Taɓ lallai ma ni za ka yi wa wayo? Na fa girme ka." Ta ida maganar tana masa gwalo haɗe da saurin yin gaba don fita daga motar saboda ta ji ana sanarwar za a tada motar. Shi kuma ya bi ta da kallo yana cewa
"Za ki sani yarinya, zan kama ki in na dawo sai kin faɗa min wanda kika girma"
Gaba ta yi tana murmushi don kullum ita da shi haka suke yi saboda ba da wani abu ne ya girme ta ba duka bai wuce shekara ɗaya zuwa da rabi, kullum haka suke kamar abokai ita da shi, su zolayi juna kamar ba saurayi da budurwa ba, don hatta girmansu ɗaya ita da shi don dai shi namiji ne, ita kuma mace kuma ba ta da wani jikin girma.
Tana nan zaune har bus ta tashi sannan ita ma ta tuka mashin ɗin ta yi gaba, duk ba ta kula ba da ta yada waya ba kasancewar hankakinta yana ga masoyinta kuma ba ta sake buɗe jakarta ba, kuma wayar tana nan yashe inda ta yada ta don inda ta ajiye mashin ɗin babu mutane da yawa, shiyasa har ta tafi wajensa ta dawo babu wanda ya kula da wayar.

LALLA HAFSATOù les histoires vivent. Découvrez maintenant