🤍Dr.TAHEER🤍
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
15
Kamar yanda Alh Adam Jakada(uncle din Taheer)yai alqawari yau ya dira garin Abuja...da safiyar gobe Kuma shi da wani friend dinshi dake nn Abuja...sai old friend din mahaifin Taheer din InshaAllah zasuje nema ma Taheer auren Sameera kmr yanda ummi ta bukata.
Daren yau Yana zaune part din mahaifin Taheer...inda a nan ne yake sauka duk yazo Abuja...ummi da Taheer na zaune cikin parlorn suma... Alh Adam na kallon Taheer yace"for the last time ina tambayanka watanni nawa kakeso a sanya maka bikin?...Taheer dake zaune kan carpet idanunshi a kasa yace"kmr nan da shekara ko zuwa da rabi haka"...a tare ummi da Uncle din nashi suka kalli Taheer din..."Kai bakada hanakali ne...are you mad...ya zakace a sa maka biki shekara daya da rabi...what's your problem?...a hankali Taheer da har yanxu kanshi ke kasa yace"ai ana sawa uncle..har shekara biyu ma ana saw...bai karasa ba uncle din ya katse da fadin"you are not serious...Kai me kake jira da zakace a Sanya maka shekara...akwai abunda baka gama bane?..ka shiga hankalinka Dani wlh...idan bakai auren yanxu ba sai yaushe knn zakayi...you are not getting any younger so in zaka dena wnn mafarkin ma ka dena...ummi dake gefe ta tabe baki snn tace"ai na fada maka dama Alh...indai Taheer ne 6ata mana rai da lokaci kawai zaiyi...ni inta nawa nema nanda wata biyu nakeso ayi bikin...ay shi ya kawota yace zai aureta ba dole akayi mai ba"...cikeda gamsuwa uncle ya girgiza kai snn yace "shikenan...tashi ka tafi"ba musu Taheer ya mike ya fita daga dakin...ummi ta bishi da harara😹
The following day Alh Adam sukaje neman aure gidansu Sameera...an Kuma sa biki next two months kmr dai yanda sukayi da ummi...farin ciki a wurin ummi baya misaltuwa...sai Kiran family and friends take a waya tana sanar dasu ansa bikin Taheer wata biyu...duk wanda ta kira yakan tayata murna snn yayi addu'ar fatan alkhairi.
Ta ko wane bangare murnan sa wnn biki ake...umma ma da taji ba karamin farin ciki ta samu kanta ciki ba... finally Taheer zaiyi aure..Allah ya basu zaman lfy...Nafeesa ma da labarin ya risketa ji tayi tamkar tayi tsuntsu tazo Abuja don farin ciki...haka Layla ma baa barta a baya ba...she's super happy daddy zaiyi aure...shknn shima daddy zai haifa 'da ko 'ya and she can boldly call him/her"kanina ko kanwata"Bangaren Taheer kuwa baiji dadin sa bikin watanni biyu ba Sam...har ga Allah yaso a sa ko 6 months ne idan ma bazaa sa shekara ba...tun daga lokacin kuma ya zama wani iri...gaba daya baida walwala sosae...Kuma sai karewa yake kmr kudin guzuri...duk ummi na lura dashi amma taki kulashi...ko me zaiyi sai anyi auren nn Bi'iznillahi...Allah ya gani shi ya fara kawota a matsayin wadda zai aura so ba auren dole zaa mai ba.
Suna zaune dinning Layla na kokarin serving dinshi...for the 5th time wayanshi ya sake daukan ruri...a fusace yai picking yana cewa"for God sake menene haka Sameera...idan kika Kira kikaga banyi picking ba Ina wani abun ne and in naga missed call zan kiraki...why kiketa jera min Kira haka sai kace mara aikin yi"... Sameera ta Dan goge hawayen daya zubo mata snn a hankali tace"am sorry"...ba tareda ya sake cewa komai ba yai hanging wayar tareda Jan tsaki...ummi dake zaune parlor tanajin duk abunda ke faruwa ta karaso dinning din tana mai mugun kallo tace"wato bakada kirki ko Taheer...matar taka kake ma wnn ihun kawai sbd ta damu da kai ta kiraka a waya...you are trying to become stubborn koh...to kaci gaba Allah ya baka sa'a...and let me remind you..in har kan mgnr auren nn kake haka...to wallahi kaji na rantse ba fashi...sai anyi auren nn...idan yaso in an daukota an kowa maka sai kayi gunduwa gunduwa da ita tunda baka shirya yin auren ba..shahsasha kawai"...Layla ta dan rausaya Kai tace"Kai ummi...yanxu da girmanshi zakina mai fada irin haka"...tun bata karasa ba itama ummi tace"kinci ubanki kema...komai girman nashi ai bashi ya haifeni ba...nice nan na haifeshi...sbd haka ki kama kanki kema tun kafin in hadaku keda uban naki incicci ubanku wlh...shashasha kema mara kunya..duk sai nayi maganinku wlh...tana gama fadanta ta wuce abinta...Layla ta bita da kallo tana turo baki kafin ta maida kallonta ga Taheer daya dafe Kai da hanunshi...ta dawo kusa dashi tareda kamo hanun nashi ta rike cikin sigan lallashi tace"kayi hakuri daddy pls"..a hankali shima ya dago yana kokarin yin murmushi ya daga Mata Kai snn ya mike kawai ya bar dinning din...direct part dinshi ya wuce ya wulla kanshi kan gado yana sauke numfashi.
YOU ARE READING
🤍Dr.TAHEER🤍
General FictionDr.TAHEER labari ne mai cikeda soyayya mai tsuma zuciya...labarin wani matashin likita daya kamu da matsananciyar soyayyar yarinyar da ya raineta a hanunshi..yarinyan dake kiranshi da suna daddy kasancewarshi cousin brother din mahaifiyarta daya gir...