🤍Dr.TAHEER🤍
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
45
Taheer na ganin tafiyansu ya tada motanshi shima snn ya bar gidan...Kai tsaye gidanshi ya koma...yayi wanka ya shirya snn ya tafi clinic...har yanxu Kuma bai denajin zuciyarshi a dagule ba..aikin kirki ma kasawa yayi a clinci din tsabar bacin ran da yake ciki.
Su Ummi kuwa tafiyan almost 6 hours ne ya kaisu Kano..umma tace ko zasu tsaya a kanon su kwana zuwa gobe Thursday su kama hanyan Dutse amma ummi tace gara su hada tafiyansu lokaci guda...haka suka dauki hanyar Dutse duk ba Wanda bai gajiba a cikinsu...sallah kadai suke tsayawa suyi..abinci kuwa dama da kayansu suka taho..duk wanda yace yanajin yunwa zaa zuba a bashi yaci...Layla Kam ko abincin ma bata iya ci sosae ba..ta damu sosae akan bacin ran data gani shimfide kan fuskan Taheer..bata San meyasa ba amma ko kadan bata so taga yayi fushi da ita...gaba daya neman sukuninta takeyi ta rasa duk yake irin wnn fushin da ita.
Sai waje karfe 4 suka shiga garin Dutse sbd yanayin hanya da bata da kyau sosae...suna isa family house din su Awwal aka tarbesu sosae..aka kaisu masaukin da aka tanadar musu su kadai...cikin lokaci kankani Kuma aka cika gabansu da kayan ci da sha iri iri..gaba dayansu a gajiye suke sbd zama wuri daya..don haka kowa saida ya dan watsa ruwa snn suka zauna cin abincin dukda ba wai suna tareda yunwa bane tunda sunci abinci a mota...Saida suka gama snn suka shiga gidan aka fara gaisawa da mutane..duk inda suka shiga sai an nuna Layla ana cewa itace marigayi Usman zai aura Kuma sai Allah baiyi ba...gaba daya Layla sai suka tuno mata da Ya Usman dinta..ta tuna yanda yake sonta sosae...dukda baza tace yakai Taheer sonta ba amma shima tanada tabbacin son da yake mata mai girma ne...lokaci daya jikinta ya Kara yin sanyi.. memories dinta da Usman din suka shiga dawo Mata..ga Kuma Taheer da taketa expecting kiranshi tun dazu amma bai kiraba...abun sai ya hadu ya Mata yawa..don haka ta samu ta sulale daga cikin mutane tareda komawa masaukinsu ta kwanta ita kadai..kawai sai ta fara hawayen da bata San takamaiman dalilinsu ba...meyasa daddy zaiyi mata haka ne..?
Abuja...
Yinin yau gaba daya Taheer yayishi ne cikin damuwa da rashin walwala...ko abincin kirki ya kasa sama cikinshi har yanxu...haka yayita zama a clinic har dare snn ya tafi gida.. Yana so ya kira yaji sun sauka lfy snn yanaso itama yaji muryanta amma he's upset with her...don me zata dauko wnn kayan ta sa hadda su mayafi snn ta kama hanya ta tafi inda yasan dole maza zasu kalleta...
Ya gama duk Shirin da yakeyi before kwanciya snn ya hau kan gadon ya kwanta..sai ya rungumi pillow yana sakejin takaicin rabashi da matarshi da akayi kawai sbd biki...the more yana tunani the more zuciyarshi ke Kara lalacewa...a karshe dai gani yai bazai iya jurewa ba sai ya dauko wayanshi ya shiga dialing number dinta..ko su ummin bazai kiraba don suma sun bata mishi rai...Layla dake kwance daki tun dazu taji wayanta ya fara vibrating...ta daukota da sauri don tana expecting kiran nashi...tana ganin shine me Kiran kuwa tayi picking don karma ya katse bata daga ba...Taheer da yaji tayi picking call din sai ya sake tamke fuska kmr tana gabanshi ya Kuma ki yin mgn...a hankali cikin voice dinta dake nuna alamun tasha kuka tace"daddy are you upset"...Taheer banza yayi mata don yana ganin tambayan nata akwai rainin hankali a ciki...ta sake cewa"am sorry idan nayi maka wani abun"...tun bata karasa mgnr ba yace mata"don't sorry me okay..karki kuskura ki bani hakuri"...Layla ta dafa goshi tanajin yanda yakeso ya caja mata kai tace"daddy laifin me nayi Kuma"...a fusace yace"oh tambayana ma kike..bakisan laifinda kikai ba right..wa ya baki izinin yafa mayafi ki kama hanya kije har Dutse dashi"...shiru Layla tayi a zuciyarta tana yanxu wnn fushin duk na mayafi ne..a fili Kuma tace mai"to am sorry..bazan karaba"...Taheer yai shiru kmr bazai sake mgn ba..sai Kuma yace"Ina su ummi"...tace"suna cikin gidan"...yace"ke kina Ina"..."Ni Ina daki tun dazu..na gaji ne shine nazo na kwanta"...a takaice yace Mata"to sai da safe".. ta amsa mai da toh snn sukai hanging call din...Layla ta ajiye wayan tana mamakin wnn fushin nashi duk don tasa mayafi ne..
YOU ARE READING
🤍Dr.TAHEER🤍
General FictionDr.TAHEER labari ne mai cikeda soyayya mai tsuma zuciya...labarin wani matashin likita daya kamu da matsananciyar soyayyar yarinyar da ya raineta a hanunshi..yarinyan dake kiranshi da suna daddy kasancewarshi cousin brother din mahaifiyarta daya gir...