🤍Dr.TAHEER🤍
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
18
Yana zaune cikin mota suka fito...Layla ce karshen fitowa tana rikeda hanun hibba...ya sake kafeta da ido yana jin ciwon fitan da zatayi a haka...ba don umma da yaga namai kallon tuhuma ba...da bata isa ta fita da wnn kayan ba wlh...duk ranshi ya kara baci...tana isowa ta bude front seat ta shiga tareda dora hibba a kan laps dinta...Taheer yai ma motan key suka fita daga gidan...Saida suka hau kan titi snn ya kalli Nafisa ta mirror yace"ranki ya dade ina Muka nufa?..dariya tayi tace"ko inama bro ai Kaine Dan gari...duk inda kasan zamu samu kaya masu kyau"...bai sake mgn ba ya dauki hanyar store din da suke siyayya...tafiyan 15 mins ne ya kaisu wurin...bayan yayi parking duk suka bude motan suka fita...Layla ta Dan saci kallonshi...ganin fuskar nn a tamke ta fita daga motan da sauri...duk ya hade fuskan nn wlh tsoro yake bata...Taheer na ciki yana binsu da kallo har suka shiga ciki...ya kifa kanshi da starring motar Yana sauke numfashi...bai san wane irin kishi yake dashi a kan yarinyar nn ba.
Ganin sun dauki kusan 40 mins basu fitoba...sai ya bude motan ya fita...Kai tsaye ya shiga ciki...Nafisa ya fara cin karoda ta dau duk abinda takeso Al'ameen na tura kayan a trolley...gaban counter suka karasa...shima Taheer din ya karasa snn ya bada atm dinshi don a cire kudin a ciki...ya kalli Ramadhan dake tahowa hanunshi rikeda wasu kayan...yace"Mami ga wani mutum can ya tare Yaya ya hanata tahowa...wai Yana son mgn da ita"...tun kafin tayi mgn Taheer ya dubeshi da sauri yace"where is she?...da hannu Ramadhan ya nuna mai wurin da take...bai sake cewa komai ba ya nufi wurin da sassarfa...ranshi in yayi dubu to a bace yake...Nafisa ta bishi da kallo kawai snn ta maida hankali kan fito da kayan data siya din.
Taheer na Shan corner ya hangota tsaye da wani namiji...bai iya ganin face dinta cox ta juya baya amma he can clearly see yanda guy din ke Mata murmushi...ya karasa wurin da sauri...ba tareda yace komai ba kawai yasa hannu ya shiga janta daga wurin...guy din ya sha gabansu yana kallon Taheer din yace"don Allah please...mgn kawai zanyi da ita ba jimawa zatayi ba"...yana gama fadan haka yasa hannu ya kama dayan hanun Layla dake rikeda wayarta Yana kokarin ya jata kawai yaji saukan Mari a kuncinshi...ya saki hanun nata da sauri tareda dafe inda aka mareshin...Layla batasan lokacin da ta saki wayan nata a kasa ba...tareda sa duka hannayen nata ta toshe bakinta dasu...hawaye ya shiga bin kuncinta wani kan wani...Taheer na kallon guy din dake dafe da cheeks dinshi har yanxu...cikin muryar gargadi yace"don't you ever...kar ka kuskura ka sake ganinta kayi tunanin yi Mata mgn talkless of dora filthy hands dinka a jikinta"...Yana gama fadan haka ya kama hanun Layla ya shiga janta da mugun sauri...sai da ya bude mota ya turata ciki snn ya zagaya shima ya shiga...dama already su Nafisa na ciki...yaja motan da wani irin gudu suka fita daga wurin...Nafisa na tambaya meya faru...da kyar Layla na kuka ta fada Mata abunda ya faru...ta karasa da fadin"wlh ba laifina bane Mami...ki tambayi Ramadhan Ina cikin tsaiwa na yazo ya faramin mgn"...Nafisa da mamaki ya isheta tace"sai ki dinga kula daga yanxu...ba kowanne namiji ne zaka tsaya kana mgn dashi a wani wurin ba"...shidai Taheer yana jinsu...amma bazai iya bude baki ma yayi mgn ba...don haka yayi musu shiru...yanajin Nafisa nata Mata fada har suka karasa gida...bayan duk sun fito...Nafisa ta zagaya side din da yake...ta Mika mai atm dinshi tana murmushi tace"godia muke bro...Allah ya saka da alkhairi"...sai da yadan kakalo murmushi snn yace"bake nayiwa ba ai...'ya'yana nayiwa"..still dai tana dariyan tace"to 'ya'yan naka ma sun gode..Bari mu karasa ciki"...Kai kawai ya iya daga mata...ita Kuma ta juya ta nufi cikin gidan... Al'ameen da Ramadhan suka dauki kayan suka bi bayanta dashi.
A hankali Layla ta kalleshi tace"daddy don girman Allah kayi hakuri...wlh it's not my fault"...Saida ya watsa Mata wani kallo snn yace"ai it's my fault tunda ni nace kisaka wnn kayan ki fita"...Yana gama fadan haka ya bude motan ya fita...batada zabin daya wuce ta fitan itama...don haka ta bude motan ta nufi gidan tana rusa kuka.
A parlor ta taradda su Nafisa...sun baje kayan da suka siyo su ummi na kalla...umma ce ta fara lurada ita tace"ke meye haka...Zaki shigoma mutane kina kuka?...Layla batace komai ba kawai ta wuce dakinta...Nafisa ta basu labarin abinda ya faru...ummi tace"don kyautawa bata kyauta ba...amma meye zai ringa hanata kula samari ko ance mashi bazatayi aure bane...Nafisa na kallon ummin tace"ummi ai ba cewa akai bazata kula samari ba...amma at least a fara neman izini tukun...ba mutunchi bane ta tsaya kula saurayi a waje"...a fusace ummi tace"to idan bata kulasu a wajeba...taya zaayi har su samu number dinta ko Kuma su San gidansu...idan bata kula samari ba sanyata a gaba zamuyi muyita kalla ko kuwa shi Wanda yake hanata kulasun zai aureta ne"...Nafisa dai shiru tayi donta fuskanci ummi bazata fahimcesu ba...umma kuwa dama shiru tayi tana sake sake cikin ranta.
YOU ARE READING
🤍Dr.TAHEER🤍
General FictionDr.TAHEER labari ne mai cikeda soyayya mai tsuma zuciya...labarin wani matashin likita daya kamu da matsananciyar soyayyar yarinyar da ya raineta a hanunshi..yarinyan dake kiranshi da suna daddy kasancewarshi cousin brother din mahaifiyarta daya gir...