🤍Dr.TAHEER🤍
Written by Maman Ashraf ✨
Wattpad@ummuashraf22
52
A takaice dai Saida Layla ta kwashi tsawon awanni tana labour amma haihuwa yaqi zuwa...zuwa yanxu karfinta ya gama karewa kaff don tun tana samu tana pushing har ta kasa yi Kuma...Taheer da har yanxu ke tareda ita duk yayi zuru zuru shima sai kace shi yake nakudan...doc Afiya har yanxu na tareda ita...su ummi ma suna waje tun suna sa rai zaa fito ace musu ta haihu har suka fara tunanin Allah yasa lfy...Saida Taheer ya fito da kyar ya samu ya lallabasu ya kaisu office dinshi don dare yayi sosae...har zuwa yanxu Kuma ko Nafeesa basu Kira sun fada Mata ba...ummi tace gara idan an sauka lfy sai a Kira duk Wanda ya kamata...shi Kuma Taheer bayan ya gama dasu ya sake komawa labour room...aikam kmr jira ake ya shigo ciwo ya sake dawowa gadan gadan...ya kama hannunta ya rikeshi cikin nashi...doc Afiya Kuma ta shiga kokarin taimaka mata...a takaice dai sai asuba snn suka samu Kai ya fito..shima Saida doc Afiya ta Mata episiotomy('Kari)snn aka samu ya fito...Layla ta saki wani wawan ajiyan zuciya don relieve sosae taji ta samu just by fitowan kan...doc Afiya ta taimaka tareda karasa ciro babyn...Saida ta yanke cord snn ta nade babyn a zani ta mikawa nurse dake tareda su...tayi withdrawing oxytocin tayi mata snn ta fara yi dinke mata wurin data Kara din..sai yanxu Layla ta samu bakin kuka..ta ringa kwalla musu ihu kmr ba itane take cewa zata mutu ba jiya..shiko Taheer idanunshi na rufe ruf don ba son ganin dinkin yakeba..yana kuma rikeda hanunta har yanxu..har aka gama dinkin nn Layla bata dena kuka tana kurma masu uban ihu ba...daga nn Saida ta tabbata ta fitar Mata da jinim da yayi saura a jikinta snn tayi Mata parking tareda hada mata ruwa ta shiga wanka...ita Kuma ta shiga gyara wurin...Taheer kam tunda yaga an fito da baby lfy ya lumshe ido yana maimaita"Alhamdulillah"cikin zuciyarshi...yana rikeda Layla dukda yanda yakejin zuciyarshi na fisgarshi kan yaje yaga babynshi amma baije inda takeba Saida ta shiga wanka...ya karasa inda nurse din dake rikeda babyn nashi take...ya Mika hannunshi kawai tareda amsan babyn da har an gama shiryawa an Sanya mai Kaya...ya lumshe ido tareda hugging babyn a kirjinshi...cikin ranshi yanayin duk addu'a dayazo bakinshi...yanajin yanda son babyn ke ratsa ko wace kafa ta jikinshi...wato haka iyaye keji a kan 'ya'yansu...ya dago face din babyn yayi addu'a tareda tofa mai snn ya dubi nurse daketa kallonshi tana smiling yace Mata"me aka Haifa"...tana fara'a tace dashi"it's a girl"...Taheer ya sake lumshe ido yana Kara godia ga Allah daya cika mashi burinshi...ya bashi 'ya macen da yake matukar so...a hankali ya sake maida idonshi kan babyn sai ya kasa gane dawa take kama...tanadai da haske sosae Wanda ko baa fada mai ba yasan wnn hasken Layla ne tunda tafishi fari nesa ba kusa ba...a hankali yayi kissing goshinta murya can kasa yace"I love you"...
Inshort dai Saida Taheer ya bata lokaci sosae yana kallon babaynshi yana Kuma surutu shi kadai snn ya tuna dasu ummi...ya mikama nurse babyn da sauri snn ya fita zuwa office dinshi...su ummi na ganin ya shigo suka shiga tambaya ko ta haihu...Saida ya sakar musu kayataccen murmushi kafin yace"ta sauka lfy Ummus..an samu baby girl"...lokaci daya suka shiga fadin"Alhamdulillah"a tare kowacce face dinta daukeda tsantsar murna..shi sai ya kasa gane ma Wanda yafi wani murna a cikinsu..Bayan doc Afiya ta taimaka Mata tayi wanka ta gyara jikinta tsaf snn ta kaita zuwa post natal..nurse ta biyota da babynta...suna shiga ta hau gado ta kwanta ko babyn nata bata tambaya ba bacci me nauyi yayi gaba da ita...nurse na kokarin kwantar da babyn daketa tsala kuka a cradle dake cikin dakin suka shigo gaba dayansu kowa daukeda farij ciki...dama suna zuwa labour room da sukaga basu nn Taheer yace suzo post natal yasan dole can zaa kaita...tsakanin ummi da Umma har rige rigen daukan baby sukeyi...karshe dai ummi ta dauka tana fadin"ai nice babba sbd haka ni zan fara ganinta"...tana gama fadin haka tasa hannu tareda yin Bismillah ta amsa babyn da har yanxu bata bar kuka ba...ta kua mata ido tana kallo sai taga tamkar Taheer dinta lokacinda aka haifeshi...face dinta irin na Taheer ne sak sai fari Kuma data dauko na Layla...a hankali ummi tayi addu'a tareda tofa Mata a fuska...ta mikama umma tana fadin"Allah ya rayaki ya maki Albarka..Allah Kuma yasa ba halin kukan Layla Zaki dauko ba..don naga tunda Muka shigo dakin nn bakinki baiyi shiru ba"...umma na dariya itama ta karbi babyn...kallon nata itama takeyi tana kuma ganin kamrta da Taheer din kmr yanda ummi ma ta gani...tayi Mata addu'a itama ta shafa mata tana cewa"Allah ya maki Albarka..Allah ya raya mana"...da sauri Taheer dake kallonsu with so much love yace Ameen...doc Afiya tayi sallama dasu zata tafi Taheer yasa hannu cikin aljihunshi ya debo kudin da shi kanshi baisan adadinsu ba..ya Mika Mata su fuska daukeda murmushi yace"accept this little gift of mine plss..na gode sosae da taimako na da kikayi Allah ya saka da alkhairi"..doc Afiya na murmushi ta amsa kudin tareda yin godia snn suka fita daga dakin..ya rage daga ummi.. umma..sai Taheer da Kuma Layla dake bacci...Taheer ya matso jikin umma a hankali tareda rungumeta yana cewa"Umma am a father now..she's my daughter umma I can't believe this..Allah na gode maka ya Allah..Allah Alhamdulillah"...da sauri ummi tazo inda suke tareda amsan babyn dake hannun umma tace"kaidai zanga randa zaka nutsu wlh..dubi yanda kazo ka wani rungumeta ga yarinya Kuma a hanunta ko so kake ka yar daita Oho"...sudai basu tanka Mata ba..shikam Taheer cikin ranshi yace"ai yanda nakejin son yarinyar nn ummi ko kuda bazan iya bari ya sauka jikinta ba balle Kuma ni in yar daita kasa da kaina"...ita kuwa umma shafa bayanshi ta shigayi tana tayashi farin ciki...ita kuwa ummi kan daya daga cikin plastic chairs dake dakin ta zauna ta Dora yarinyan kan laps dinta snn ta dauko wayanta ta shiga neman layin Nafee.. ringing din farko Nafeesa ta daga kmr dama jiran Kiran take...hankali a tashe tace"Ummi haihuwan yazo koh"...Saida ummi ta saki dariya kafin tace"ai an rigama an sauka Nafee..kin ganni rikeda babyn a hannuna"...Nafeesa ta saki wani Hamdala..muryanta cikeda murna tace"dn Allah da gaske ummi..yaushe ta haihu..meta haifa...ya akai baku kirani ba ummi"...ummi na cigaba da dariya tace"duk wnn tambayoyin haka Nafee da wanne zan fara...tun daren jiya ake abu guda wlh amma sai asubahin nn ta haihu..an samu mace"...Nafee tace"MashaAllah ummi..Allah yaraya yayi Albarka..Ina Laylan take"...Saida ummi ta dubi inda Laylan ke bacci kasadan snn tace"she's sleeping..tunda ta haihun ma inaga ko babyn bata ganiba.. amma dai lfynta Lou"... Nafee ta sake cewa"To Alhamdulillah tunda she's fine..Allah ya Kara Mata lfy ya raya mana baby..Nima Ina nn zuwa ummi ko yau na samu available flight zan taho InshaAllah"...ummi tace"to shknn Allah ya kaimu"...daga nn sukayi sallama...ummi ta maida dubanta ga Umma da Taheer da har yanxu bai bar jikinta ba.. bai Kuma dena sambatun da yake ba..kawai he's happy yau shine da 'ya ta kanshi..jininshi...ba abinda zaiyima Allah daya wuce godia..he's forever grateful...
YOU ARE READING
🤍Dr.TAHEER🤍
General FictionDr.TAHEER labari ne mai cikeda soyayya mai tsuma zuciya...labarin wani matashin likita daya kamu da matsananciyar soyayyar yarinyar da ya raineta a hanunshi..yarinyan dake kiranshi da suna daddy kasancewarshi cousin brother din mahaifiyarta daya gir...