chapter eleven

1.5K 90 16
                                    

🤍Dr.TAHEER🤍

Written by Maman Ashraf ✨

Wattpad@ummuashraf22

11

Wannan Daren ma kmr wancan Sam Taheer bai samu bacci ba sai dayai sallahn asubah...hakan yasa bai tashi da wuri ba sai after 10....bayan yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya as always ya nufi part din ummi...tana zaune parlor tana kallon wani program ya zauna kusada ita bayan sun gaisa tace"ya ciwon kan naka"....yace "to da sauki zaace ummi nasan stress ne idan na samu hutu zai Dena...tace"ya kamata dai ka samu kayi hutun gsky"...yace InshaAllah..baby bata tashi bane?Ummi tace "kmr dai bata tashin ba don tunda na fito banji duriyarta ba...ya mike Yana fadin bari in duba mgn nake sonyi da ita...tana tsaye gaban press dinta tana neman kayanda zata saka ya shigo dakin..ta juyo da murmushi a fuskarta tace"good morning Daddy"Yana murmushin shima ya amsa Mata"morning..zo muyi wata mgn"ba musu ta dawo gefen gado ta zauna tareda maida hankalinta gareshi...Saida ya kauda kanshi snn ya fara mgn"Usman ne dama yace Yana sonki and he wants to marry you"Layla ta zare ido da mamaki tace ban gane he wants to marry me ba daddy..wane Usman din ma kke mgn in the first place?ya kamo hannayenta ya rike snn a hankali yace"dama mgnr daya kaimu Dutse knn...Alhaji ya fadamin Usman yace Yana sonki Kuma suna son hada aurenki dashi amma sai da amincewarki...idan bakiso ba Wanda zai maki dole"Layla tayi shiru na tsawon lokaci tana tunani kafi tace"daddy to Kai yanxu zakamin aure ne?bakace sai na gama school zakamin aure ba"Taheer ya lumshe ido ya bude snn yace"haka na fada baby Amma bazan iya musu da Alhaji ba...kinga a ka'ida Yana da right din da zai badake ga duk Wanda yakeso amma sbd karamci irin nashi sai baiyi hakan ba..ya kirani ya sanar dani snn yace a tambayeki..amsanki kawai muke sonji kina sonshi ko baki sonshi??Saida tadan tabe baki snn tace"am not used to loving u know..ban taba son kowa ba apart from you sai su ummi so ban San ya so din yakeba..amma daddy Kai ka amince ne..I mean kanason in aureshi?Taheer yai shiru kawai Yana kallonta ji yake inama zai iya fitowa ya sanar da ita shima yana sonta..inama zai iya nuna Mata babu Wanda ya Dace da ya aureta face shi...tunanin hakan yasa zuciyarshi ta sake karyewa da kyar ya daga Mata Kai alaman ya amince...sai ta saki murmushi tace"Nima na amince daddy..ban San ko Ina sonshi ba amma na amince sbd Kai..nasan InshaAllah with time zanyi developing feelings for him"ya Dan kakalo murmushi snn yace "alright bari inje in kirashi sai in sanar dasu kinyi accepting..bai jira cewarta ba ya fita a dakin da sauri..baibi takan breakfast din bama ya wuce abinshi.

Yana shiga daki ya Kira alhaji ya sanar dashi ta amince..alhaji ya nuna farin cikinsa sosae snn yace zai sanar da Usman ta amince ko a waya sai su fara mgn da ita kafin ya samu lokaci sai yazo Abuja su sake fahimtan juna.

A bangaren Taheer kuma ya yanke ma kanshi hukunci zai fara yin baya baya da Layla..a tunaninshi hakan ne kadai zai saukaka mai abinda yakeji gameda ita... snn kuma bazai iya jure yana kallonta tana waya da wani a mtsayin Wanda zata aura ba...so it's better ya rage shiga harkanta kawai...kazantar da baka gani ba akace tsafta ce.
Wannan kenan

Kwanaki nata tafiya yayinda shakuwa me karfi ke shiga tsakanin Layla da Usman...dukda bai taba zuwa Abuja ba amma kasancewarshi mai raha da son mutane cikin lokaci qarami Layla ta fara sabawa dashi snn ga uwa uba soyayyan da yake gwada mata...duk da har yanxu bawai zatace ta fara sonshi bane but tanajin dadin kasancewa tare dashi.
Saidai wani abu dake damunta shine canji data gani tattare da daddynta..Sam bata San laifinda ta aikata mai girma haka da har zaisa daddy ya fita harkanta gaba daya..he no longer cares about her kmr yanda yakeyi a baya...abun ba karamin damunta yake ba kuma ta rasa wanda zata fadawa...ko mgnr aurenshi da anty Samira a bakin ummi taji tasan da Dane da bakinshi zai fada Mata tunda yasan tanaso yai auren...gaba daya she's confused bata San laifinda ta aikata ba...kodai don tayi accepting Usman ne??ta tambayi kanta sai Kuma wata zuciyar tace ba haka bane ay Saida ya nuna amincewarshi snn itama tayi amma why daddy zai juya Mata baya haka?

🤍Dr.TAHEER🤍Where stories live. Discover now