chapter eight

1.6K 83 3
                                    

🤍Dr.TAHEER🤍

Written by Maman Ashraf✨

Wattpad@ummuashraf22

08

Ranan Thursday Layla na zaune sai sharan hawaye take sakamakon kalaban da ummi ke Mata...Sam bata son a taba Mata kai.
Saura befi hudu su gamaba Taheer ya shigo parlon...ya kalli Layla dake ta aikin kuka snn ya kalli ummi data daure fuska tana cigaba da kalaban....yanason yin mgn amma yasan ummi fada zata haushi dashi don haka yayi shiru kawai ya zauna yana kallonsu....kasa hakura yai da ganin yadda Layla ke kukan yace"ummi sannu da aiki...ko Zaki kawo in karasa Mata"...banza tayi dashi batace komai ba....Saida ya sake maimaitawa snn ta dago tana hararanshi tace"in baka ka karasa salon ka kyaleta ta gudu koh...to baka isaba....kullum Kai kake lalata yarinyan nn duk wani abun daya kamata bazaka barta tayi ba....ynxu wnn kan nata kusan watanshi hudu ba kitso sai kace ba mace ba....to na dena Bari wlh... daga yanxu every two two weeks zan dinga tsefe kan da kaina snn inyi Mata wani....idan bata saba da kitson ba haka zaayi Mata aure taje tanayi a gidan miji....to ba zaayi haka daniba...tunda ta fara mgn shiru yayi kawai Yana kallonta....Saida ta gama kalaban tsaf snn ta mike tana karkade jikinta ta wuce daki abinta....da gudu Layla ta fada jikinshi tana cigaba da kukanta tace"daddy don girman Allah ka tsefe min wlh kaina har ya fara ciwo"....ya rungumeta sosae a jikin nashi ya shiga shafa dogon gashin nata yace" shushh ya isa to dena kukan....kinsan ummi bazata Bari a tsefe ba....so kiyi hakuri bazai dade yana miki ciwonba...kafin tayi mgn wayanshi ya fara ringing...."Alhajin Dutse"shine sunan dake kan screen din wayan nashi(N.B Alhajin Dutse shine kakan Layla,shine ya haifi mahaifinta snn Kuma yayan kakanta Wanda ya haifi mamanta)....ya dan janyeta a jikinshi snn yayi picking..."Assalamu alaykum"...aka fada daga daya bangaren... Taheer ya amsa tareda gaisheshi...mutumin yace"Alhamdulillah Taheer ya mahaifiyar taka....tana nn lfy alhaji...."MashaAllah dama wani mgn ne ya taso shine nace let me call you anytime ka samu chance sai kazo muyi mgnr....da sauri Taheer yace alright zanzo gobe InshaAllah...mutumin yace no ba sauri ake ba Taheer....u can take ur time duk ka sama dama sai kazo....da sauri Taheer yace....ba damuwa sir....zan taho gobe in Allah ya kaimu....alhajin yace"shknn Allah ya kaimu goben...ka gaida amaryar tawa...Taheer ya amsa da zataji InshaAllah snn ya ajiye wayan....da sauri layla dake jin me sukace tace "daddy kaje Dani plss....nadade banje Dutse ba daddy don Allah zan bika"....mikewa yai yace"alright idan an samu tickets biyu sai muje...let me talk to ummi first...yana shiga ya fadama ummi yanda sukayi snn ya tafi clinic...ya Kira wani friend dinshi dake airport yace yanason tickets biyu zuwa kano gobe....cikin saa Kuma an samu zasu sauka a kano daga nn sai su karasa Dutse a mota.

Washegari....

Taheer na zaune parlo shida ummi ya gama shirinshi tsaf...Layla ta fito daga dakinta itama ta gama shiryawa hanunta rikeda Arabian gown dinta da zata Sanya gobe...sai pant da bra dinta data Dora kan rigan.....ta karaso parlon tasa hannu ta dauko Dan jakan da Taheer yasa kayanshi a ciki ta shiga sa natan a ciki itama...ummi daketa kallonta da mamaki taja tsaki tace"kedai zanga ranarda Zaki nutsu kisan kin girma Layla...ynzu breziern ne kika dakkoshi haka gagal gagal ko Dan sakayawa babu??..Layla na cigaba dasa kayanta a jakan tace"to ai naga ba kowa a parlon dagake sai daddy fa....ai ba kunyanku nakeji ba...ummi ta girgiza Kai kawai tace"Allah ya kyauta...Taheer dake nan zaune yana jinsu murmushi kawai yai don baisan me zaice ba....suna gamawa driver yayi dropping nasu a airport suka shiga jirgi zuwa Birnin dabo.

Bayan isansu kano gidan umma suka sauka...saida sukaci abinci suka Dan huta snn driver dinta ya daukesu zuwa jigawa....basu saukaba sai around 4 na yamma....bayan driver yayi parking suka nufi entrance din gidan....wata mai aiki ce ta bude musu kofa bayan Danna door bell da sukayi....tayi musu iso zuwa central parlor snn ta tafi Kira musu matar gidan....bayan mintina kadai sai gata ta sauko daga sama....dattijuwar Mata ta karaso parlon da fara'arta suka gaisa da Taheer....snn ta kalli Layla tace to tsohuwa da fatan dai ba zama kika zoyi gidana ba....Layla na murmushi tace"ay idan baki wasaba har mijin kima sai na kwace kafin na bar gidan....matar ta zaro ido tace"lallai Layla kinyi baki yanxu....ya ummin taki...ummi na nn lfy tace a gaisheki...tace Ina amsawa bari ayi muku mgn da alhajin....ta mike xuwa sashen maigidan nata....bayan minti kaman biyu ta fito tace musu bismillah muje....sukabi bayanta har zuwa part din....yana zaune kan daya daga cikin royal chairs din dake parlon....dattijo ne wanda kallo daya zakamai kagano yanada tarin ilmi....bayan sun zauna Taheer har kasa ya durkusa ya gaidashi hakama Layla da yaketa faman tsokanarta wai bata ajiye komai ba sai tsayi....hajiya ta mike tacema Layla"to tashi muje 'yar nema ki barsu suyi mgnrsu...ba musu Layla ta mike suka fita tare....alhaji na kallon Taheer yace"yanzu ka fara huta gajiya Taheer....in anjima sai muyi mgn....shidai Taheer ba haka yaso ba....kmr yace baya tareda gajiya Kuma yai shiru....alhaji ya daga waya ya Kira wani....bayan few minutes wani saurayi ya shigo dakin....kyakykyawa dashi ya risina ya gaida Taheer snn alhaji yace"yawwa Usman ka kaishi masaukinshi snn ka tabbatar ka Kai mai duk abinda yake bukata...Usman ya amsa snn ya dauki jakan dake gefen Taheer ya fita....a hankali Taheer ke binshi a baya baisan dalilinda yasa jikinshi yai sanyi hakaba....ya kagu yaji wani mgn ne zasuyi....boys quarter Usman ya kaishi....Saida ya tabbatar ya mai duk wani abu daya kamata snn ya mai sallama ya tafi....Taheer kwanciya kawai yayi yana tunani sai can ya dauko waya ya sanar ma ummi sun sauka snn ya Kira umma itama ya fada Mata ya sake komawa ya kwanta.

🤍Dr.TAHEER🤍Where stories live. Discover now