2

172 3 0
                                    

*AUREN DOLE*
👰👰👰👰👰👰

*NA*
*RABI'ATU BASHIR(Ummu Maher)*🍇
_______________

*🖊️⚔️ALKALAMI YAFI TAKOBI WRITER'S ASSOCIATION🖊️⚔️*
____*(A.Y.T.W.A)*__

'Kungiyar da ta kasance ta Marubuta Masu Fasaha Da Sanin Ya kamata.

*Bismillahir-Rahmanir- Rahim*
_________________

*Page🟨2*

'Malam Hamisu Dan Borno Shine Cikakken Sunan Mahaifin 'Indo.Mahaifin "Indo Matanshi Hudu' Uwargida Itace  Surbajo Mahaifiyar Indo, Tanada Yaya Goma "Indo ce Kawai Mace,Sai Falmata Itace Ta biyu Ita Yar 'Uwar Malam Hamisu ce Sunkasance 'Yan Maiduguri Borno State.

"Sai Habiba Ita Yar Adamawace Yayanta Tara,Duk Mata "Sai Halima Mai "Yaya Shidda Ita Ma yar Adamawa ce.

" Malam Hamisu Mahaifin Indo Shine Ya karbi Abubakar Alokacinda Mahaifinshi Yarasu.Wanda Yakasance Amininshi Sosai.Abubakar tunda Yataso Saida Yayi Shekara Goma Sha Biyar Sannan Aka Haifi 'Indo Yanansonta Tun tana Karama,Alokacin Kuma Yayi Saukar Alqur'Ani Mai girma.

"Sanda Yakai Shekara Ashirin'Alokacin Indo Shekararta Biyar Kuma 'Alokacin Wani Abokin "Malam Harisu Maisuna Jabbama Yayi Sha'awar Hada Yarsa Da Abubakar.

" Malam Hamisu Yasan Asalin Jabbama Mutunne Mai Hakuri Da dattaku Sosai.Gashi Da Kyauta 'Shiyyasa Ma Da Ya Tuntubi  "Malam Harisu Da Maganar Ya Yadda Akancewa Zai Kebe Da Abubakar Din Yaji Ta Bakishi.Haka Kuwa Akayi Sanda Ya nemeshi Da Maganar Ya Amince Batareda Yace Komai Ba Saboda Yanajin Kunyar Malam, Dan ko Kashi Yau Malam Yace Zai Hadashi Dashi Baijin Komai Don 'Yafi Karfin Haka Awajenshi.Babu Bata lokaci akayi Aure.Ta tare.

" Malam Abubakar Shima Yazama Babban Mutun 'Inda Haryanzu "Indo Tana cikin Ranshi. Ya Kara Aure Don Uwargidanshi Tazo Masa Da Cewa Kawarta Hadiza Batada Miji Kuma Dan Allah Ya Aureta. Ta Nada kirki Don Alokacinda Tahaifi "Mustafa Shine Danta Nafari.Ita ke zuwa ta taya ta Aiki da komai.Shiyyasa Take Ganin Mutuncinta'Malam Da farko Bai Aminceba Daga Baya "Ya Saboda Ya Matar Tashi Ta shiga Damuwa.Bayan Anyi Aurensu Ta Haifi Danta Namiji Hakilu,Nanfa Hadiza Tazage Tana Yiwa Kawar Tata Rashin Mutunci Tawa Uwa Da Uba.

" Ita Kuwa duk Abinda Zatayi Mata Bata Taba Kallonta Da Abinba.Hasalima Saidai Tayi Murmushi'Ana Hakane "Indo Ta Zama Budurwa Ayanzu Tanada Shekara Shadaya Daidai. "Malam Kuwa  Yana ta Jiran "Indo Tagirma Dan Yanzu Har mafarkinta Yakeyi. Yana Sunbatu Uwargidanshi Kuwa Kuwa Kullum Yakanyi Mafarkinta Adakinta,Yanacewa Wayyo "Indo Kisoni Inbaki Soniba Zan mutu Abindai Yakai Malam Kamar Zaiyi Hauka.Hadiza Kuwa " Tace Saidai Yamutu don Wallahi Babu Abinda Yashafeni.Uwargida Kuwa Hankalinta Yatashi Sosai Matuka,Babu Bata Lokaci Tafadawa "Malam Hamisu halinda Mijinta Yake ciki.Babu Bata lokaci yazo don ganin jikin Nashi Yadda Yake.Ko da yazo Kuwa Alokacin Yana sunbatu 'Yana cewa Wayyo Allah Na "Indo ina sonki kisoni Dan Allah,Malam Cikin Dattaku "Yace Abubakar Meyayi Zafi hakane Malam Ya tsugunna Yaringa Yimishi Addu'O'i Amma kamar Ana turaashi.
" Malam zuwa Yanzu Yagane me "Abubakar Yake nufi Wato Yada de Yana son " Indo Yarshi Ya jin jina kai  Bayan yaga yadda Abubakar yasamu bacci.
'Bayan ya Isa Gida yasamu Surbajo Uwargidanshi Da maganar,Surbajo Tayi Murna Sosai "Ta kai Amma fa Naji Dadi Yaro Mai Hankali Gashi Yakama Sa na'arsa Mai Kyau Ga Almajiranshi Yanzufa Malam Haryafika Almajirai Malam "Yace To Yanzu Dai Kinga "Indo shekararta Sha dayane da Rabi,Amma za,a iya Auren Daga baya Saita Tare Alokacin Tamara Kwari.

" Malam Hamisu Kuwa Yasamu "Indo Da maganar Nanfa "Indo Babu ko Kunya Ta Fulani Tace Bata sonshi Ita "Sani takeso almajirin Malam.

Share&Comment
Ummu Maher

AUREN DOLEWhere stories live. Discover now