*AUREN DOLE*👰👰👰👰👰👰
*NA*
*RABI'ATU BASHIR(Ummu Maher)*🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇,,,,,,,
✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*🖊️⚔️A'LK'ALAMI YAFI TAKOBI WRITER'S ASSOCIATION⚔️🖊️*📚📖
✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__*((A.Y.T.W.A))*🖊️🔍📖
*_K'ungiyar_ da _ta_ _kasance_ _ta_ marubuta masu _fasaha_ da _Sanin_ _ya_ _kamata_*.
_______
*Bismillahir_Rahmanir_Rahim*
______________
*Page🟩23&🟪24*
"Haris yayi saurin d'ago idonshi akan k'anin nashi" Bashir ya nufo inda "Haris yake ya zauna kusa dashi yad'ago idonshi Wanda yayi jawur" ya kalli "Haris yakasa magana sai " Haris d'inne yayi saurin cewa haba"Bashir sabida me zaka shigomin d'aki babu sallama me yayi zafi haka?
"Ola lekon ya tashi ya basu waje don su gana da d'an uwanshi" Bashir yace Bros Ina cikin matsala sosai bros "Kana da Sanin cewa 'Hajiyarmu tayi min " AUREN DOLE"
"Kuma wai y'ar k'auye gashi ni kuma Nayi Auren soyayyah da" Zahrata"Kuma yanzu tace dole saina saki'Matata 'zahrah'.
"Haris kuwa idanunshi ne sukayi jawur alamun ranshi yayi matuk'ar tashi'Don shi " Haris mutunne mai hak'uri idan Abu ya b'atamai rai to gaskiya abun yayi tsanani,"Haris ya d'ago Rinannun idanunshi ya kalli k'annin nashi dasu."Wai yau 'Dijanshi ce aka Aurawa k'anninshi 'Bashir har yake fad'in abinda yakeso akan ta,Lallai 'Bashir ya ci darajar d'an uwanshi da sai ya koya mishi Hankali don yadda yakejin " Dijaa wallahi gani yakeyi indai babu 'Dijaa to tamkar babu shine don yadda yake k'aunar "Dijanshi Amma babu yadda zaiyi k'addara ta Riga fata.zai rungumi k'addara ya zauna da matarshi Wacce akayi mishi " AUREN DOLE"Da i'ta wato "Kaltume.
" Yana cikin wannan tunanin zucine ya jiyo muryar"Bashir yana cewa don Allah Bros kashiga maganar nan Don Allah.
Haris ya dafa k'annin nashi "Yace Bashir Kai ka Riga da ka b'atawa iyayenmu Rai adalilin Auren da kayi babu Wanda yasani to Amma Babu komai zamuyi magana dasu," Bashir yace Nagode Bros shiyyasa Nake sonka."Hajiya kuwa Zaune ta ke tana karanta " Alqur'ani maigirma ta tsinkayo Sallamar y'ay'an Nata Ta D'aga kanta ta kallesu ta re dajin k'ara sonsu. Suka shigo Zauna suna zama zasu gaida "Hajir wayarta tayi " Ringing"Ta d'auka tareda cewa W/kslm "Malam daman yanzu nake shirin kirawoka.
" Malam muntaho yanzu 'Hajiya mutuniyarki fa Tana ta yimana Rigima,K'anwarki ke Rarrashinta fur-Tak'i yin shiru."Hajiya Tace to Bata Wayar "Malam ya mik'awa " Dijaa wayar'Hajiya tasaka wayarta"A hands free ta ke Zazzak'ar muryarta ta cika Wayar Tace "Hajiya kinga " Malam yace wai i'dan Zamu dawo bazai taho Dani ba.
'Haris kuwa wani irin Abu yataho yasa yamai a wuyanshi ya rasa yadda zaiyi da Rayuwarshi,Sai yanzu ya San ya tafka Babbar asara ta Rashin Sanar da soyayyarshi da baiyiba Yayi Zurfin ciki gashi yanzu yanaji yana gani tafi k'arfinshi, ya Runtse Idonshi ya na mai furzar da huci A fili."Hajiya ta juyo da kallonta wajenda " Haris yake ya Rame sosai duk da girman jikinshi mai siffan k'arfafa Amma kana kallonshi kasan yana cikin damuwa sosai kuma ta San halinshi da zurfin ciki sosai.'Hajiya Tace Haba son meyake damunkane gaba d'aya ka sauya haba Dan Allah meyake damun Kane eye?
"Haris yayi shiru ya kasa Cewa komai,Ta ke ya ji k'arfin hali Ya zo mai saka makon kiran sunan Allah da ya ringa Kira acikin zuciyarshi.
" Haris ya taso daga inda yake ya matso kusa da"Hajiya 'Yace Hajiya abinda yake damuna ba komai bane illah "Damuwar d'an uwana" Hajiya don Allah kiyafewa"Bashir matuk'ar kika yafemai to "Dady ma nasan zai yafemai tunda kin fishi d'aukar zafi." Hajiya ta kalli "Haris Ta ce son na yafemai d'an uwanka bayajin magana ta akanme na Auramai yarinyar da nake ganin y'ar mutunci wadda zaiji dad'in AUREN ta wadda batada wayewar da zata bijiremai'Yarinyar da sonda nake Mata kamar ni na haifeta haba ya bazanji ciwo ba,Saiya rasa Kuma wadda zai Aura sai " Baturiya"Ha Kuma bada sanin muba tunda shi ya d'auko k'arfi KO ganinshi yakeyi damu kamar sa'anninshi KO to Wallahi kaci Darajar d'an uwanka na yafema Saidai tunda kabi jiremin to dolene Nima kafarantamin'na Auren "Dijaa d'iyar mutunci da mutuntawa.
" Bashir kuwa tunda ta Fara magana yayi shiru batare da yayi ganaba ya sunkuyar da kanshi.Yana tunanin yadda zai zauna da Matar da baya sonta Kuma y'ar k'auye.
*** *** ***
Sai Dare sannan su"Dijaa suka i'so birnin kano,Tunda ga k'ofar gidan "Malam yake ta kallon i'Kon Allah don tunda yake bai tab'a ganin gida mai kyau kamar haka ba.Bai tsinke Al'amarin ba saida suka shiga gidan maigadi ya wangale musu gidan " Malam kuwa abinma sai ya Ringa bashi tsoro yayi galala yana kallon i'kon Allah saboda kyau da tsaruwar gidan."K'anwar Hajiya ta tashi "Dijaa daga baccin da ta keyi tana 'Dariya Ta ce Amarya mai Rigima munzo ko 'Inna Uwargida Ta ce lallai kam wannan Amarya da Rigima Ta ke y'an uwan " Indo Mahaifiyar "Dijaa kuwa sukace Lallai kam Amarya mai Rigima tayi da ce Amarya mai goshi.
" Ba'ah b'ata lokaci ba suka Shiga da "Dijaa gidan tareda gyaran mata lifayar da a ka sa mata." Hajiya kuwa najin tsayuwar motarsu"Dijaa ta sake kallon"Bashir da ke kusa da "Haris suna hirarsu ta y'an uwantaka,Sukayi" Hajiyarsu na cewa "Bashir ka nitsu kajini kada kasake " Kayiwa mutanannan wani Abu kanajina KO ya kalleta"Yace to "Hajiya zanyi yadda kikace'Yasha shaddarsa da kakkiya mai kyau shima " Haris haka yayi kyau da shadda skye Blue wadda ta dace da Clour d'in jikinshi chocolet colour shidaman"Haris ba fari bane shi.
*** *** ***
Suka shigo gidan su"Haris sukayi sallama Aka umarci'Dijaa ta shiga da k'afar dama.Bayan sun shigo"Haris da Ango 'Bashir suka shigo gaisheda surukan nasu'Bayan sun gaisane 'Hajiya ta rik'e "Dijaa da kanta ta kaita d'akin da yazama d'akin Dijaa ne da Angon Nata" Bashir da ya had'u sosai komai nasu yana cikin b'angaren masu d'akin"Bashir Dana"Dijaa yana kusada juna sai babban parlonsu da kitchen da band'aki sai Kuma wasu d'akunan manya gidan dai masha'Allah b'angaren nasu dai yayi kyau sosai."Hajiya ta saka aka kawo wasu"Malam abinci sukaci suka sha.Bayan sun gaman"Malam suka k'ara gaisawa da "BASHIR inda " Haris yayi musu sallama ya tafi gidanshi cike da tashin hankali Allah ne kawai yakaishi gida.
*Ummu Maher ce*.✍️
*Vote*
*Share*
and
*Comment*🗳️📩💌
[10/10 22:42] Rabiatu.b.Abdull(ummMaher: 👰👰👰👰👰👰