13&14&15

81 3 0
                                    


*AUREN DOLE*

👰👰👰👰👰👰

*NA*

*RABI'ATU BASHIR(Ummu Maher*🍇🍇🍇🍇🍇🍇
____________,,,,,,,,

✍✍✍✍✍✍

*🖊️⚔️AL'K'ALAMI YAFI TAKOBI WRITER'S ASSOCIATION⚔️🖊️*📚📖

__*((A.Y.T.W.A))*__📚

✍✍✍✍✍✍
______________,,,,,

_,K'ungiyar da ta kasance ta Marubuta Masu fasaha da sanin Ya kamata.

*Wannan Shafin Nakune Masoyana Baki d'aya*

*Special gift to My📩*

*👱🏻‍♀️Nabeela Dikko*
*(y'ar mutan dikkawa*)

*Allah ya k'ara Mana basira Da zak'in Hannu Amin*
_______,,,,_______

*Bismillahir_Rahmanir_Rahim*

*Page🟨13🟩14&🟪15*

________➡️"Bashir dake tsaye ai sai yaji jiri na Neman d'aukarshi'Zahrah tayi saurin mik'ewa ta ruk'o maaoyin Nata tana tambayarshi me yafaru kawai sai ya zauna zaman y'an bori dab'as.

"Zahrah ta tashi ta d'auko wayar tashi'gashin kanta ya Rufe mata Ido tayi saurin gyarashi ta d'auko mai Wayar   tasaka Hands free'
" Hajiya kuwa dataji shirun yayi yawa sai tace"Bashir kanajina'Kuma munyi Magana da Mahaifinta Yace idan kadawo muxo Tare  dakai Don banason a d'auki lokaci Sam,Nafison ayi dawuri ka koma da Matarka.

"Hajiya tacigaba da cewa kuma kasan meye'Yarinyar tanada، Hankali da nitsuwa kenanda kunya'Ga Addini'gata Yarinya k'ara shagal don bazata Wuce Sha Ukuba Amma kafin ta tare zata zauna Wajena tak'ara kwari." Hajiya tasake Cewa My Son kanajina Kuwa naji kayi shiru.

"Bashir kuwa Yayi 'Zahrah inkiya da takashe Wayar takashe tana Wani zare ido'Fuskarta harta b"aci don ganin masoyin Nata cikin tashin hankali'a a ta ke kuma wani kishi ya bigi zuciyarta sosai jin Muryar mace maizak'in sauraro haka.

" Zahrah kuwa ganin har yanzu"Bashir baiyi Magana ba ta zauna  "tad'ago fuskarshi 'Tace Bash sunanda take fad'amai kenan 'Tace haba Bash ya akayi meya faru,KO wani abune yafaru,Kuma sannan wacece Wannan wadda takiraka awaya.Cikin yaren France take maganar'Bashir tambayar ce tayi mishi yawa 'yace  Ta b'allo mai magani  yasha sai barci.

" Zahrah ta Lillib'e da bedsheet me kyau'ta tsiramai gwala gwalan idanunta kamar na mayu tana kallonshi cike da shaukin so,Tana cewa azuciyarta indai kuwa "Macece takirawoshi to ta b'allo wa kanta jaraba don zata iya komai akan " Bash d'inta.toh Wannan kenan!kome zai faru idan yatashi? kubiyoni don jin abin da zaifaru.

"Hajiya kuwa tabi wayardake hannunta da ido tana mamakin abinda yasa " Bash yakashe Mata Waya.Afili tace KO lafiya oho?

"Shikuwa Haris cike yake da farincikin da bai tab'a tsintar kanshiba, ya Danna hancin motarshi cikin gate d'in dake manne a jikin dank'areren gidanshi Wanda " Sojoji sukayi mishi k'awanya.

"Ola lekon ne yafito dasauri ya bud'ewa Megidannashi murfin mota yafito fuskarshi shimfid'e da k'aya taccen Mur mushi'Sosai. Haris Yace haba Ola'bana fad'amaka kada ka k'are bud'emin Murfin Motaba.Haba nima abarni in ringa excersice ko.Ola' yayi   dariya Yace Sorry Oga.Ola'kuwa yana mamakin Ogannashi yaga yana cikin farinciki shima sai ya tsinci kanshi cikin farinciki.

" Wayar ola'ce tayi ringing Wanda ke mak'ale  agefen Aljihunshi nakakin "Soja" Ya d'aga yana cewa 'Hellow madam Mrs Ola' Yayi wata dariya data dawo da"Haris daga hayyacinshi.
Haris kuwa yanajin yadda"Ola'yake Magana da matarshi Wacce sukayi "Auren soyayya" Bashi da akayiwa "Auren dole" Ba ata ke yaji wani irin haushi azuciyarshi"Haris yayi wata dariya"Yace babu komai na kusa "Auren Soyayya" Haris ya shafa gyemunshi yana murmushi mai k'ayatarwa.

"Haris kuwa yanashiga gidanshi ya wuce d'akinshi "A Alokacin 'Kaltume tana fallow ta zube kayan 'Mata'A gabanta Tana ta d'irka,Shikuwa " Haris baisan tana yiba ya shige cikin d'akinshi KO cire kayan"Sojanshi baiyiba ya haye kan gadonshi Yayi Ruf da ciki yana tunanin Masoyiyarshi"Dija.

"Malam Abubakar zaune A'Babbar kujerarshi Ya Tara matanshi duka'Yayi gyaran Murya'Yace Daman bakomaine yasaka nataraku ananba sai " Neman Auren Y"ata 'Dijaa'.

"Aiba " Inna Uwargida da"Raheela ba har'Indo saida ta d'aga kanta ta kalli "Malam fuskarta tana zubarda hawaye don ayanzu tayi Nada mar abinda taringa yiwa" Malam Abubakar da Y'arta tilo "Dijaa Wani son y'arta tane yak'ara shiga zuciyar" Indo tana mai Nadama da zubda kwalla sosai.

"Mlm kuwa ya kula da yadda" Indo ta firgita da jin za'ah Aurar da y'arta ta.Indo kuwa azuciyarta tana cewa yanzu da na kula da Y'ata da Mlm baitara min Kishiyoyinaba da tuni munyi Maganar mu kad'ai.

"Malam yadawo dasu daga tunanin da Suka Lula.Yace daku nake fa kunyi shiru KO Baku ji abinda na fad'aba.

" Sukayi Saurin cewa Munji Allah yasa ayi damu"Inji Inna Uwar'gida.Tana mamakin Aurarda "Dijaa da gaggawa haka. Bayan suntashi Duka matan Mlm yayi saura.Indo ce kawai Awaken" Mlm ya kalleta  cikin sakin fuska yace"Indo Amarya lafiya tayi k'asa dakanta tanamai tsiyayar hawayenta ak'asa."Indo Tace Mlm yayi saurin d'ago kanshi yaji me "Indo zatace don yaga yau tayi wani lakwas babu Rashin kunyarnan. Ya kalleta yaga yadda tayimai Wani Kyau'Yarintarta yasake fitowa sosai.Mlm yashafa gyemunshi yayi wani Murmushi yana juya idonshi sosai kamar wani tsohon Maye.

" Indo ta taso daga inda ta ke ta matso kusada Mlm Sosai,Tarik'e gefen takalminshi cikin kukanta Mai ratsa zuciya."Tace Mlm don Allah don Annabi Mlm Yayi saurin Amsawa da cewa;(S.A.W) yana maishafawa harzuwa gyemunshi.

"Indo Tace Mlm Kayafemin kuskurenda nadad'e inayi'Maka Na tuba kayafemin.Mlm kuwa cike da farinciki da k'aunar Matarshi" Indo ya dago dakanta yana Mai gogemata hawayenta.Nandai Mlm da"Indo suka d'inke sunamai cike da kewar junansu.
Toh Wannan kenan"



***    ***   ***

"Bashir kuwa yana tashi daga baccinshi Yaga " Zahrah agefanshi tana yimai Sannu'Ya tashi Yayi Brush yayi wanka""Zahrah tafita domin shi"Bashir yana kare mutuncin kanshi Da addininshi don baiyar"Zahrah tana d'akin yana wankaba.Bayan sungama cin abincinne yake cemata tafad'awa iyayenta ad'auramusu Aure'Take tanbayarshi me yafaru kuma.Yace shidai yafad'amata idan zaitafi"Nijeria 🇳🇬"K'asarshi ta gado yanason ad'aura musu Aure.


*No comment No typing*


✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

🧡❤️🤍💙💛

*Ummu Maher ce.*

💚💜🖤🤎💗

✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

AUREN DOLEWhere stories live. Discover now