*AUREN DOLE*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*NA*
*RABI'ATU BASHIR(Ummu Maher)*🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
_______,,,,,✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*🖊️⚔️AL'K'ALAMI YAFI TAKOBI WRITER'S ASSOCIATION⚔️🖊️*📚📖
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
___*((A.Y.T.W.A.))*🖊️🔍📖*K'ungiyar da ta kasance ta marubuta masu fasaha da Sanin ya kamata.*
______,,,,,
*😄🥰 Wannan ma shafin na kune Reals*😘
(Nabeeha Aminu)🧕🏻
&
(Nabeela Dikko)🧕🏻
*Allah ya bar zumunci Amin*
______,,,,,*__Bismillahir_Rahmanir_ _Raheem*
_______________*Page🟧18&⬜19&🟩20*
*** *** ***
"Hajiyarsu Haris kuwa a hargitse tayo kan d'an Nata tana kiran sunanshi tana girgizashi da k'arfi,Amma abinda tagani ne ya sata yin wani ihu tareda salati da k'arfi jinine ke zuba ta hancin " Haris da bakinshi da gudu ta fito parlonta tana Neman taimakon gaggawa,Dadynsu Haris ta hango da K'anninshi suna hira, ta nufo inda suke a hargitse tana nuna musu d'akin da hannunta bakinta yana kakkarwa idonta na zubar da hawaye mai zafi.Da gudu suka isa d'akin don ganin menene ai suma tuni hankulansu suka tashi sukayi gaggawar d'agashi suka fito dashi daga d'akin"Dadynsu Haris kuwa yana ta kwala wa mai gadi kira yana cemishi ya bud'e musu gate.
"Sun iso hospital d'in su K'anninshi" Bashir inda adaidai Alokacin"Bashir yadawo da Matarsa "Zahrah Saidai ya ajiyeta a hotel d'in da suka sauka kafin yazo ya gabatar musu da matar tashi Uwargidanshi.motarsu Dady na sauka shima ya shigo asibitin dayake ya Dade baishigo asibitin tunda suka mayar dasu Kaduna.
" Dady kuwa da k'anninshi da sauri suka fito da"Haris Wanda a yanzu baisan inda kansa yakeba saboda halin da yake ciki,"Bashir kuwa bai hangosu ba daga farko saida ya fito daga cikin motar sannan ya hangosu da gudu ya iso inda suke rik'e da"Haris suna kiciniyar fito da shi daga cikin motar yana zuwa yace Dady lafiya mai yafaru da "Haris lafiya shima hankalinshi ya tashi sosai da ganin d'an uwan nashi " Dady yace wa Bashir ba lokacin tambaya bane kaidai yi sauri mu shigar dashi, Da sauri suka kamashi suka shiga dashi"Bashir ya kirawo likitocin Abokanshi da saurin suka d'auko gadon marasa lafiya suka shiga dashi aka rufo k'ofar"Inda su Dady suka tsaya abakin k'ofar d'akin suna kukan zuci.
"Dady da k'anninshi kuwa sai kallon " Hajiyarsu Haris sukeyi cike da tausayinta don sunsan duk cikin y'ay'anta tafi son "Haris shiyyasa sukejin tausayinta sosai fiye da Kansu.
" Likitoci kuwa sun duk'ufa wajen bawa"Haris taimako inda yanzu sun gano matsalarshi kuma numfashinsa yadawo normal.Saida sukayi awa d'aya sannan suka fito hard a "Bashir Wanda yayi mamakin abinda ke damun d'an uwan nashi wayo cutar tunani. suna fitowa su Dady sukayo wajensu " Bashir suna tambayarshi'Yace wa
su Dady su ta ho office.sukayi yadda yace Bayan sun shiga suka zauna har Hajiyarsu "Haris yace daman abinda yasa nace muzo nan don infad'a muku abinda yake damun d'an uwa nane,Ba komaine yake damunshiba sai cutar tunani akwai abinda yake damunshi Wanda yazama dole abashi shi sabida azauna lafiya Wanda anayimai abinda yake damunshi zaizama tarihi.Dadynsu Haris da Hajiya bak'aramin Mamaki abin yabasu ba tome yake damunshi sukayi ta tunani a zuciyoyinsu.Nasamar d'annasu abinda yake so har yajazamai wannan matsala.
" Bayan sunfito daga Office d'in "Hajiyarsu Haris ta kirawo Wayar" Kaltume don tasanar da'ita halinda mijinta yake ciki.itama "Kaltume bak'aramin tashin hankali tashigaba don tana matuk'ar son Mijin Nata sosai." Bashir yace musu nanda awa d'aya zai farka suka ce toh cike da alhinin abin don sunasan Sanin abinda yake damun d'an nasu.
*** *** ***
Bayan awa d'aya "Haris yatashi yaji jikinshi yayi mai nauyi sosai,yana tashi Kaltume yafara gani kusa dashi yabita da kallo ya kalli inda Hajiyarsu take tana sallah,ya hango Dadynsu da k'aninshi 'Kaltume tacewa su Dady yatashi suka matso sunayimai Sannu.Hajiya ma ta idar da sallah tataso tana yimai Sannu.Dady yace ak'irawo likita Momi tafita don kirawo likitan.
" Bashir kuwa ya na Office da abokinshi ' doctor Faisal yana ce mishi Faisal kaga ga d'an uwana babu lafiya yanzu Yaya zanyi gashi nataho da Zahrah and'auramana Aure da ita,Gashi Hajiya tayimin AUREN DOLE, Yanzu Yaya zanyi Faisal ni narasa ma yadda zanyi wallahi abin yayiwa kwakwalwata yawa.
"Faisal yafashi Yace kayi Hak'uri abokina su " Hajiya zasu fahimceka.Bashir ya juya zai d'auki lapcort d'inshi idonshi yashiga cikin Na "Hajiyarsu cikin tsananin firgici,Ya Fara fad'in Allahumma Ajirni fi musibati Wa aklufni Khairan minha.
*Kuyi hak'uri Nayi tyiping kad'an Ina busyne*🙏🏻
*Ummu Maher ce*.✍️
*Vote*
*Share*
and*Comments*
[