41&42

171 4 0
                                    


*💋 _AUREN'DOLE_ 💋*
👰👰👰👰👰👰

  *_Written_ by*✍️
*Rabee'atu .B. Abdullahi*
(Ummu Mahe)🍇🍇🍇💋💋💋💋

Y'ar Mutan Nigeria🇳🇬🇳🇬🇳🇬💚🤍💚

   *Page🟨41&42*

_____"Ina shiga gidan'Muka gaisa da Mijin Aunty Sadiya'Na zauna muna ta hira da Surayya'Tace kinsan Allah"Dijer gaskiya baki da wayo idan kinason kija hankalin mijinki ya soki'yaji dake to ga wata hanyar da Zan lissafomiki matuk'ar kina haka to Wallahi kin gama dashi.


1_Na farko iya magana
2_Shagwab'a
3_Biyayya
4_Iya girki
5_Tsafta
6_Kula dakai'dashi kanshi mijin  da kula da danginshi da dukiyarshi.
7_Hak'uri
8_Juriya
9_kula da addini

10_Kwalliya

"Surayya tace kinga wad'annan abubuwan su " Aunty Sadiya ta ke fad'amun don haka saiki dage wajen kwato naki mijin'Harme akayi wata farar fatar,Banza dame sukafi mu Hausa Fulani'To idan zaki farka ki farka'Naji Ana fad'in hakan abayana"Aunty Sadiya ce abayana tsaye da k'aton cikinta kamar zai fashe'Bansan sanda na k'el k'ele da dariya ba'Tace ke kinji mun wulak'anci"Dijer ni kikewa dariya ko'to ai dad'in abun kowa ma zaiyi sai muga yadda mutun zaiyi idan yagani ajikinshi"Ta rankwashi 'Surayya tace har ke munafuka da kika k'i futo da Mijin Aure'kinganta nan kullum'sai tsirfa sai Iyayi'Wallahi ki cigaba'AUREN'DOLE'Zan miki.


       "Surayya tace haba Aunty nace miki fa ni duk basuyimunba harda fa'Wannan baturen fuska kamar ta kwai,Ni duk basuyimun ba'Tace mun Allah" Dijer wannan Hafiz'd'in da na gaya miki,Komai d'inshi yayi Amman d'an isakane lamba d'aya'Da yazo fa sai kiji yana cemun wai irinmune matan da akeso'yan duma_duma,sai kiga ya hau tab'amun hannu na ni kuma nan zankarta mai rashin mutunci murabu baran baran.



       "Aunty Sadiya tace to Allah ya kawo Nagari, muka amsa da Amin muka cigaba da hirarmu,Cen Nace Aunty Sadiya bari intafi'Yaya Bashir sun kusa da wowa Tace to Ina zuwa.

Ta shiga d'akinta ta debomin wasu sleeping dress'Y'an ubansu da wasu skin tight,Sunyi kyau sai Body hok,Da har da Hularsu sunkai guda biyar kowanne da Hularsu'Kafin Inyi Magana'Surayya ma ta ajjemun irinsu masu kyau matuk'a da turaruka masu dad'i.


Na kalli " Aunty Sadiya,da "Surayya Nayi musu godiya suka bani shawarwari,Kala Kala Kama daga yadda Zan sanya kaya da yadda'idan naga" Bashir zanyi kwarkwasa da kissa da yadda zanyi da jikina inyi ta juyashi kamar maci jiya.

Ina zuwa gida na baje su akan gadona insaka wannan insaka wannan,daga k'arshe dai duk na linkesu kamar yadda suke na fito don d'ora girki,Abun yana bani mamaki wani lokacin sai nayi kwanaki bangs"Zahra ba sannan sai'inga kuma ta dawo,Abun yana bani mamaki Matuk'a.


Ina gamawa na jera akan dining bayan na jera,na k'ara gyara wajen,Sannan na zuba nawa naci bayan nagama na wanke kwanon da naci na kife sannan na koma d'akina,Na tsalo wanka kamar Zan Canza fatata'Bayan nagama wankan na gyara kaina da man wanke Kai,Nayi relaxer'Yayi kyau bayan nafito na k'ara gyarashi,sai k'amshi ya keyi gwani ban sha'awa gashi fa ya d'au k'el_K'eli gwanin sha'awa,Na shafa lotion mai dad'in k'amshi Nan danan fa jikina ya hau silb'i kamar Auduga,Hannuwana kuwa sai wani shek'i yakeyi ga laushi.


Na d'auko wani short nicker da wata Riga snglet'sai na d'ora Y'ar falmaran akai'Wow na fad'i Ina k'ara fara'ata ganin kyaun da nayi,Na d'auko nayi parking d'in gashina da Jan rebom'tunda kayan ma akwai ja'da fari ajiki.

Nan fa d'auko turarena na wajen Momi na saka,Sannan na kuma k'ara na wajen su'Aunty sadiya,Ai kafun kace me d'akin ya hau wani irin k'amshi kamar me,Na saka warwaro Na Red da Ring shima Red Wow fad'in irin had'uwar da nayi ba'ah magana gashi nayi wani irin fresh,gani y'ar  Baby ta Dani y'ar k'arama sai iyayi .


Ina fitowa daga d'akina nafito da Qur'anina Ina karantawa sai naji an bud'e k'ofa da Sauri Na tashi zanshiga d'akina,Sai na tuno da Nasihar dasu Aunty Sadiya sukayimun,Sai na maze na tashi Nayi mishi sannu da zuwa,Wani Irin kallo ya Bini dashi Wanda na tabbatar shi kanshi baisan yanayi ba ni kuwa cikin salon da suka koyamun nafara tafiyata Ina murgud'e murgud'e Ina karairaya,Y'ar k'aramace ni Amman Inada halitta mai ban mamaki.


Na had'amai abincinshi na mik'amai na sunkuyo'Ai wani Abu ya gani bansanda yace Wow ba'Ni kuwa dariya kawai nakeyi ciki ciki,Ya muk'omin k'afarshi wai na cire mishi safarsa mamaki ne shimfid'e a fuskata yayimun Alamun da Incire mishi,Ina cire mishi yana wani Jan numfashi Ina gamawa ya k'ara ruk'o hannuna wai naci gaba,ni kuma nagane wayanshi Dana tsugunna babu KO kunya zai shaga yayi ta kallona.

Bayan mungama cin abincin,na kwashe kayan naje na d'auraye kayan Sannan na dawo na gyara wajen'Yana zaune da laptop dinshi yana ta danne danne,Na cigaba da Aikina inayi Ina rausaya kamar wata macijiya,Shi kuwa fad'Bashir fad'i yakeyi azuciyarshi Anya kuwa wannan"Dijer ce kuwa Dijer d'in da yasani y'ar k'auye wadda bata iya dressing ba anya kuwa itace.

********************

Da daddare kuwa na fesa wankana da wata sleeping dress mai d'an Karen kyau,Farace k'al Amman mai kwanciyace ajiki,tana da wandonta aciki doguwa ce Amman ta fi guiwa da kad'an Wani murmushi nayi na gyara gashina sai k'amshi ya keyi na k'ara duban kaina acikin madubi,Masha"Allah na fad'i.


Ina fitowa na hangoshi yana ta Aiki da laptop gashi gefanshi duk wasu ta kaddune'Maze zanwuce Sai Naji Yace"Dijer ki had'amun coffee ki kawo mun d'akina.



Hmmm🤔😄?Wayyo Allah na "Bashir wato'Anfad'a  tarko KO,to wai in Ankai coffen🥃Mezai faru😄😄😄😂😂to Nice first din Comment,Allah duk Wanda yakaranta Baiyi Comment Bazaiji me zai faru ba......





*Ummu Maher ce*

*Vote*
*Share*
And
*Comment*✍️
[11/10 12:02] Rabiatu.b.Abdull(ummMaher: 👰👰👰👰👰👰

AUREN DOLEWhere stories live. Discover now