3

19 1 0
                                    

______Hanyar Kitchen d'in gidan ta nufa wanda ke cikin parlour'n.

Ba tare da b'ata lokaci ba ta fara had'a musu abincin da zasu ci cikin gaggawa, don yau ta tashi batajin dad'i sa boda rashin lafiyar da Amrah ke fama dashi, yanzu ma ji take tamkar ta dawo da zazzabin jikinta ko ta samu nutsuwa, don a duniya bata kaunar abu ya tab'a Amrah.

cikin k'ank'anin lokaci ta kammala had'a, joloff d'in Spaghetti, domin tasan idan bata gama da wuri ba shima wani bidirin ne mai zaman kansa da zai tashi a gidan ……….

      Bayan ta gama ne, ta sakana Abbansu  a cikin Warmer d'aya, sannan ta saka na Mummy da Afrah acikin warmer guda d'aya.


Kana  ta d'ibi nata ita da Amrah acikin plate, wacce jikinta ya d'au zafi, alamun zazzabi ya ta sake dawowa, duk da kuwa da safe ya sauk'a, tasan dawowarsa baya wuce kukan da tayi dazu da kuma rashin maganin da bata samu ba. Wanda ita naga San inda zata samo mata ba.………

…Dukkansu akan dining d'in ta ajiyesu kana ta nufi D'akin dake mallakinta ita da Amrah a cikin gidan,

Don Afrah a D'akin Mummy take kwana, saboda wai tana fara bazata had'a D'aki da bak'ak'en mutane ba. (Sai kace Mummy ce mai halitta.)


Shurun da taji, ya tabbatar mata da Afrah taci abinci, kuma abincin da aka dafa  ya mata, nan itama ta samu hankalinta ta kwanta, domin tasan idan baiyi mata ba, to lallai dole ta sake dafa wani,

Haka Afrah ke mata a wassu lokutan, sai ta takarkare tayi girki sai tace bai mata ba, wani abun take son ci, kuma dole a sata ta sake dafawa ko da kuwa tana halin ciwo ne.……


Nan ta kwanta a gefen Amrah tare da janta a jikinta, tana jin yadda jikinta yake tururin zazzabi mai zafi.

Ido ta tsurawa  Amrah'n dake kwance,

A zahiri  Amrah take kallo, sai dai kuma abunda take tunawa daban.



       _Kwata-kwata bata jin dad'in yadda rayuwar gidansu yake._

Dama Uwa nak'in abunda ta haifa ne? ko dai ita rayuwarta ya bam-bamta dana kowa?
Ita me laifnta? bayan bata halicci kanta ba.

Allah shi ya halicceta, kuma a haka yake son ganinta, amma duk laifin halittan fatar jikinta an d'ora mata ita kad'ai tamkar ita tayi kanta …….


Gashi har Yarinya k'arama wacce bata san me duniya take ciki ba, ta fara fuskantar  gararin rayuwar
da ita take fuskanta tun tashinta sabida kawai ta kasance  *BAK’AR FATA* shin me ne ne laifinsu don sun kasance bak'ak'e???? Su sukayi kansu ne? Ko dai su suke son hakan? Su Ya kamata su tuhumi Mummy akan haifansa gambiza da tayi……

Haka taci da tunanin yadda rayuwar gidansu ya wakana a shekarun baya zuwa yanzu, babu wani canji.

Amma zataci gaba da addu'a tasan Allah bai manta da ita ba.


Zata cingaba da addu'a har ubangiji Allah ya nuna mata karshen wannan zaman na gidansu.

Domin gidansu wani irin bahagon gida ne, mai rud'd'en lissafi.

***       ***       ***

  Washe gari, tun 5:30 ta tashi, as usually, shara tayi, ah tayi mopping,  kana ta d'aura musu breakfasts, tana gamawa tayi wanke-wanke, bayan tayi shara, kana  ta tada Amrah tayi mata wanka, kana ta bata abun karyawa taci, kad'an saboda rashin jin dad'in da batayi. sannan ta sanya mata uniform.

Tasan Amrah bata da lafiya, amma babu yadda zatayi dole taje school, don da barinta a gida gwara taje school d'in, at least suna tare Makaranta d'aya.



Amma idan ta zauna a gidan bata san batasan me za'a mata ba, domin babu mai tauyinsu a cikin Gidan.


Hatta Mahaifinyar data haifesu, k'yamansu takeyi, bata sonsu, bata shiga sabgarsu, ba ruwata dasu.

Mahaifinsu shine kad'ai mai bata hak'uri, wanda yakasance bashi da "Say"  a cikin Gidan, domin dashi da babu duk Uwar Ubansu d'aya,

Numfashi ta sauk'e, kana shafa  kan Amrah, a yayin da ita kuma ta tashi, kana ta shiga wanka, cikin saurin ganin lokaci ya k'arato.

Bayan gama saka Uniform d'inta, ba tare da tasawa cikinta komai  ba, taja hannun Amrah suka fita daga D'akin.

Sanin babu wanda ya tashi daga cikin Gidan, domin Afrah already tayi Candy tun last year. A yayin da ita kuma take ss 2. Kuma  bana take son zatayi Paper.


Haka ta isa cikin Makaranta ta, bayan takai Amrah class d'insu itama tayi nasu class d'in.

Maths shine First period, don haka ta zauna ta nutsu.

Tayi mugun k'ok'ari, ganin ta kawar da tunani daga cikin kwanyar kanta, saboda ta samu ta gane karatun, kwata-kwata bata son damuwar gidansu ya shafi karatunki, amma babu yadda ta iya.....✍️





*#Share fisabillah*


WATA UWARWhere stories live. Discover now