_Back to labari_
…………Mi[]ewa Mamy tayi, kana ta masa sallama ta tafi gida, kaman yadda ta shaida masa, bayan ta tattara abubuwan da ya kamata a tafi dasu gida.......Fitan Mamy ba jimawa su Muhammad suka zo kaman yadda suka saba, wanda ke nuna da alamun sa[]ani sukayi da Mamy'n........
Hira suka tab'a, sai da dare yayi, kafin suka masa sallama bayan sun bar masa Muhammad (Babandi) kasan cewar yau kwanansa ne........
*_Washe gari....._*
Aiko washe gari kaman yadda suka tsammanta aka sallameshi, ya koma gida bayan an tabbatar da warkewa ciwukan jikinshi, haka ma karayar kafa da hannun, daga nan aka tabbatar da babu wata matsala kana daga bisani aka basu takardan sallama suka koma gida yana sumul garau tamkar wani abu bai tab'a faruwa dashi ba........
_(Allahu ka bawa marasa lafiya na gida da asibiti lafiya, ya Allah mu kuma da muke dashi ka k'ara mana lafiya mai anfani ba don halin mu ba.....)_
★★★
A bangaren Afrah kuwa, duniya ta mata sugar rayuwa ta mata zuma, ta ji dad'i taci abun da take so ta sha abunda take so, haka kuma ta kwana a inda take so, ta fita a Sanda take so haka kuma ta dawo a sanda take so, ba mafadi tamkar akuyar da bata da mai ita.......
_Waye ga kule ta mutu Fatima ta mutu ayi wasa......_*Ni dai nasan duk wanda ya rasa ma fad'i to yasa a ransa ya shiga suran da ba aya,*
Zuwa wannan lokacin kuma Fahad ya gama gama gane abunda Afrah take yi, ya so ya taka mata birki, sai dai wata Zuciyar ta gargadeshi da aikata hakan.......
Hakan yasa ya kyaleta tana cin albarakacin tantanin daya bi ta kai, a cewar sa........
*A BANGAREN SU SIMRAH*
BA TARE DA kyamkyami ko wani abu ba, ya gyara mata jikin ta, bayan ya mata allura ya samu tayi bacci.
Daga karshe dai a D'akinsa ta kwana, ba tare da Ammy ta nuna damuwar hakan ba.
Washe gari kuma, tun bayan tafiyar sa Salla, ta tashi itama, kana tayi side dinsu a yayin da Zuciyarta ke luguden yadda Ammy zata d'auki lamarin.
Da zuwan ta D'akin bata kalli Amra ba, da alama dai a D'akin Ammy.....
Sai dai da mamakin ta ganin ko maganan Ammy bata mata ba, haka tayi jinyar kwana biyu kaman yadda takeyi a ko wani lokaci na period d'inta kana ta warware taci gaba da attending lectures d'inta.......
*BAYAN SHEKARA UKU*
....Kamar yarda Mamy ta wajabtawa Simran yiwa Simrah Lesson kullum dare, hakan ne ya tabbata, domin kullum karfe 8pm zata tafi part dinshi karatu, ita ce ba zata dawo ba sai 10pm....
Shaƙuwa ce mai matuƙar yawa ta shiga tsakaninsu, wanda yasa ko motsi daya daga cikinsu yy to daya yasan mai yake nufi, suna matuƙar ji da juna, suna mutunta juna, basa son ganin ɓacin ran juna, kamar dai yarda Mamy ta yi maradi tare da Alƙintawa hakan ya faru, domin tana hango tsananin shaƙuwa da soyayya mai zafi wadda basu san sunawa juna ba, a cikin idanunsu,hakan kuma ba ƙaramin dadi yawa Mamyn ba.
dan dama ta jima sosai tana fatan su haɗa kansu, su zama tsintsiya madaurinki daya......cikin ƙanƙanin lokaci Simran ya fada wani mugun kogon soyayyarta, ko zama yy sai ya ringa ganinta,murmushinta marar yankewa yana barazanar dauke mishi numfashi daga cikin gangar jikinshi, taƙun tafiyarta, yana yin maganarta, mu'amularta, gaba daya sun zauba daram a cikin tunaninshi, bashi da damar zama shiru shi daya.
da ya zauna kuwa sai tunaninta ya Addabawa Rayuwarsa, wanda yasa ya fara ƙaurace mata, dan gani yake yawan kusantar juna da suke shine ya haddasa mishi shiga cikin wannan.....A ganinshi in ya nisanta kanshi da ita zai samu rangwame na abun da yake ji, amma kuma abun da bai sani ba, wannan shine ya ƙara gina tubalin tunaninta a cikin ranshi, sa boda tsananin tunani har rama yayi.
Yau din ta kasance Juma'ah wanda yasa gaba daya ma'aikata suka dawo da wuri domin shiryawa zuwa Sallar Juma'a......
Misalin 12pm ya kamshin turaren Giorgio Armani ya ƙarade gaba daya palon, a hankali ta daga kanta izuwa sama ta saman Steps ....
Gently cikin natsuwa da kamala ya fara saukowa daga Upstairs yana sanye da Farin Boyle mai manyan zane, ya sha hularshi Zanna da Takalmin Cover baƙi, yy wani fitinannan kyau, gashi sai baza kamshi yake......
Idanunshu ne suka sauka cikin na juna, karfaffiyar Ajiyar zuciya suka sauke a tare kuma zuciyarsu tayi wani bugu da yasa dukkansu suka daura hannuwansu saitin zuciyoyinsu , sakamakon bugawar da take.......
ita ce ta fara cire idanunta daga cikin nataa,tare da fesar da sanyayyen numfashi, a hankali ya fara saukowa daga steps din idanunshi a kanta, har ya ƙarasa saukowa ƙasa, ss ta mishi kyau shima, zama yy kan kujera, rusunar da kanta tayi Ba tare da ta ce masa komai ba.
A zahiri kwata-kwata ba ita yake kallo ba, sai dai a bad'ini kuwa, duk wani movements nata yana ankare dashi hakan ko ya takura ta sosai......
Domin itama tasan ba ita yake kallo ba, tunda gashi ya maida hankalin SA ga akan wayansa.
Sai dai tasan yana kallon ta ta hanyar jin idanunsa masu kaifi akanta tamkar razor blade sabo mai shegen k'arfi kiran kamfanin tiger.......
A k'alla ya d'auki ⁴0minutes a wajen yana zaune yana mata kallon k'asa-k'asa, wanda take jinsa har cikin jininta yana zagayawa.
Ganin lokaci ya ja ne yasa ya mik'e ba tare da yayi magana, haka itama,
Sai dai a cikin ransa yana jinjina miskilancin yarin yar.....
Fita yayi ya tafi masallaci kasan cewar lokaci yayi.
*Bangaren Afrah*
Da farko ta d'auka abun haka zai dore, sai dai daga baya sai taga Ashe abun ba haka ba. Domin kuwa daga manyan alhazawa sai ta dawo kanana, daga su kuwa ta sake dawowa down wanda karshe tana iya fita har ta dawo bata hadu da wanda ya nemeta ko da kuwa da ³0 minutes ne.
Wannan abu tun baya damunta har ya dawo yana tab'a ta sosai, hakan yasa kullum take fita ba tare da ta gaji ba, karshe sai ta buge da neman bokaye a cewarta ko Hannu aka SA mata.
Sai dai mutumin dake d'an iska ne, sai YACE mata ai an saka mata Hannu ne a akan sana'ar tatan, don haka zai mata aiki sai dai aljanu suna bukatar sprm d'in jikin ta.
Ba tare da wani tunani ba ta amince nan wannan mummunan kazamin da bai san Allah ya hau kanta.......
Fahad ya zuba mata ido, don zuwa yanzu ko nemanta baya yi, kawai tana cin albarakacin wannan fatan kaman yadda ya fad'a a shekarun baya.
Sai dai zuwa wannan lokacin ta fara kaishi mak'ura, hakan yasa yake ji a ransa lallai gab yake da yaci Ubanta, sai dai zai bari sai ya k'arasa mata daurin talalan da yayi niyya........