8

19 1 0
                                    

______Baki ta tab'e kana taci gaba da kallonta, don ta samu ta kore wannan b'acin ran da Yusuf ya dura mata yanzu, lallai ta yarda duk duniya bata da makiyi kaman Yusuf.......


Tunda abunnan ya faru magana irin haka, ko maganan abunda zata haifa bai sake had'a Hauwa'u da Yusuf ba......


........Haka taci gaba da kula da cikinta, tare da taimakon Yusuf, har watanni haihuwar sukayi.


Ranar wata Laraba da daddare ta tashi da nak'uda, ba tare da b'ata lokaci ba ya sungumeta sukayi Asibiti.


Bata d'auki lokaci mai tsayi ba, cikin ikon Allah da buwayarsa Allah ya sauk'eta lafiya.....


Inda ta samu 'Ya mace haka kuma mai haske, irin na Uwarta, kaman yadda take buri kuma take muradi.


Zo kaga murna wajen Hauwa'u,  bakinta yak'i rufuwa  sa bo da sanin abunda ta haifa...,


A ranar aka sallamesu bayan likitoci sun tabbatar da lafiyarta dana abunda ta haifa.


Bayan sun dawo gidansu ne Yusuf yayi waya da gida ya sanar dasu maganan haihuwa.


Nan ko dangi da abokan arziki suka fara tayasu murna samun karuwa.

Washe gari aka turawa Hauwa'u babbar mata mai kula da ita da Jaririyarta.


Babba ce mai suna Laraba, wacce aka turo mata ita dangin Mahaifiyarta (Hansai)


Ana gobe suna Innayi da Hansai shirya sukaje Bauchi don ganin Yarinya.

Ranar suna Yarinya taci sunan Hafsa suna ce mata (Afrah) anyiwa Mahaifiyarta mai suna.


Haka aka ci gaba da rainon Afrah, bayan gama arba'in Laraba ta tattara ta koma, aka bar Afrah dai Mahaifiyarta sai kawarta dake zuwa gidan jefi-jefi Maman twins.


Inda Hauwa'u taci gaba da kula da Afrah, wacce takeson Yarinyar tamkar zata had'iyeta ta sake tufo da ita, don So, don jinta take har cikin ranta....


Afrah tana da shekara uku, Allah ya sake bawa Hauwa'u wacce Afrah ke kira da (Mummy) wani cikin kuma a karo na biyu.

Tayi farin ciki da samun cikin, sa bo da ita bata k'i ashe tayi ta ajiye 'Ya'ya mata farare irinta ba, ko ma ta cika gidan dasu, bai dameta ba indai mata ne kuma farare......


.....Don haka ta d'auki son duniya shima ta d'aurawa cikin, sai dai son da take masa, bai kai wanda tayiwa na Afrah ba, don wannan tamkar an cire mata son, shi d'in ma tana sonsa, sai dai bai kai Rabin na Afrah ba......

Abba dai ido ya zuba mata, domin tun akan acikin Afrah yayi sanyi akan lamarinta, ya kjma d'auki alk'awarin bazai sake mata magana akan ciki ba......


A cewarsa bazai sake magana ba akan abunda ya shafi wannan b'agaren ba, domin baya son irin haka yana shiga tsakaninsu tunda ba sabawa sukayi ba, ya kuma.


Sai dai bai fasa kula da ta ita da cikin jikinta ba, haka ma Afrah, kasan cewar  cikin yana mugun bata wahala, don kullum a kwance take kaman ruwa......

Bata ci bata sha, babu abunda yake zama acikinta, domin komai taci sai ta amayar.

Mummy bata samu sauk'in ba, sai da cikinta yayi wata biyar, daga haka kuma komai ya koma normal, taci gaba da zuwa aikinta wanda abokin Yusuf ya nema mata, mijin Maman twins.

Haka rayuwa yaci gaba da tafiya, cikin Mummy yana cika wata tara da sati biyu, a daren ranar ta tashi da ciwon baya da mara.

Cikin tashin hankali ya debeta yayi asibiti da ita, bayan ya kai Afrah mak'obtansu.

WATA UWARWhere stories live. Discover now