……… Da maganan Zee, kwana biyu aka k'ara, ana washe garin zasu koma Asibiti Bauchi, don mata aikin ta, rai yayi halinsa, ta ce ga garinku nan.....
Mama taji mutuwar Zee fiye da tunanin mai karatu, jí irin wanda baki bazai iya fad'a ba.
Sai dai tuni ta dauki alhakin mutuwar ta ta dorashi akan Baba, don a cewar ta shi ne ummul kab'isin faruwar komai.
A cewar ta daya rike samartakansa tun lokacin daya zama cikekken mukallaf da duk hakan bai faru ba, hakan yasa bayan rasuwa Zee da kwana goma sha uku, zuwa wannan lokacin kuma mutane duk sun watse hatta na jinin ma sun tafi, hakan yasa ta je dakin sa, don surfa masa bala'in dake cin ranta.
Baba wanda zuwa wannan lokacin ya fara saduda da akan lamurin duniyan,
Musamman idan ya tuna da daa, Allah ya azurtashi da lafiyayyun yara har k'waya uku, biyu maza d'aya mace, amma a kwana a tashi babu ko d'aya, numfashi ya sauk'e a lokacin daya kalli Mama kana ya ce........
"Asma'u lafiya,?
"Ita ce ta kawo hakan, Alhaji na gaji, dama jira nake gidannan a watse na zo nace maka ka bani takarda ta, domin na gaji da ibtila'in dake samuna a dalilin zaman gidannan.
"Wallahi na gaji bazan iyaba, yara uku na haifa amma yau babu ko d'aya.
Tunda na kai munzalin balaga ko hannuna wani DA namiji bai taba rike wa ba, Har sai da aka kawo maka ni, amma dalilin ka, har Jika shege sai dana a wannan bayan nawan, ba kuma d'aya ba, ba biyu, bar maganan cikin da aka zubar duk kuma Yaya na ne.
Fahad saboda halinka d'aya d'auka na iskanci, har ma ninkawa domin d'an na gada yafi d'an na koya,
har nema sai da yayi, don Allah ya tak'aita min wahala ne nayi ihu kaji da abunda ya faru da Mama a cikin littafin Sadeey na *HAIHUWATA* shi ne zai faru dani, daga haka ka sallamawa duniya shi, yanzu ko halin da yake ma bamu sani ba.Shi kuma Mubarak tamkar ba musulmi jinin Hausa_Fulani ba, tamkar d'an Arna ri[]e adda da wuk'a, neman mata, ZINA har da fyade, fashi da makami, shaye-shaye, kwace. duk wannan d'ana ne mai yin wadannan mugayen abubuwan da ko guda d'aya bawa yaeyi wallahi Allah bazai ga da kyau ba, amma ni nawa d'an duka yakeyi, har ma da wanda ban sani ba. Yayansa ya nemeni sai kuma ya nemi kanwarsa, tamkar gidan dabbobi wallahi haka rayuwar gidannan take.
Sai Zainab mace kaman ni, daya kama ta ita ce zata ji6ance ni ta bani hak'uri idan Mahaifinta da yayunta suka dura min bak'in ciki, ta share min hawaye na a yayin da bakin ciki yasa suka zubo min. Wai ita ce Mubarka zai nema har da cikin da sukayi ta zubar wa, bayan yayan shegu k'waya uku da Fahad ya tafi barmin. Chaiiii innanillahi wa inna ilaihi raji'un, hasbunallahu wa ni'imal wakil....
"Hajiya Asma'u dan Allah kayi hak'uri.
"Ya isa Alhaji! Ka sani an dad'e ana ruwa kasa tana shanyewa, wallahi wannan karon zan magance matsalan gidannan da kaina,!!! duk da kuwa Mubarak dana ne na ciki na,!! amma wallahi sai ya girbi abunda ya shuka ta hanyar kai shi k'ara kotu, kuma ni ce zan zama lawyer d'in kai na! Ko don na kwatowa Yaron da aka kashe baiji ba bai gani ba hakki!!!
Tana gama fad'an hakan tayi waje duk da kiran da Baba yake kwala mata akan ta saurareshi.
Bayan kwana biyu Barrister Asma'u ta shigar da k'ara, a zaman farko kuwa ta bada shaidan video'n data saka Zee mai-mai ta maganganun ta. aciki.
A wannan zaman ne kuma kotu ta yenkewa Mubarak Garba Abdullahi D'an_Buram hukuncin daurin rai da rai tare da horo mai tsanani.
Mama Zuciyar ta ta riga da ta bushe, ta k'enkeshe, bata jin ko d'ar akan abunda ta aikata.
A yayin da Baba kuma ya k'asa tawakkali yayi ta kuka musamman inda aka zo wucewa dashi dom kai shi gidan yari.
Yadd yake ta kuka yana neman yafiyar ta da kuma bata hak'uri akan ta janye karan ya mata alk'awarin zai tuba.
Sai dai bai san bakin Alk'alami ya riga ya bushe ba.
Haka kuma ta dawo ta fuskanci kula da Baba, wanda hawan Jini ya masa bugu daya ya kada shi, gefensa daya yayi shanye wato yayi paralysis.
Itan ma don Allah yayi ta mai dakekkiyar Zuciya ne, da tuni itan ma hawan Jinin ya kada ita.
Mutane da dama sun nuna mata kuskuren ta na kai d'an ta kotu a yenke masa hukunci, sai dai hakan bai dame ta, domin da Zuciya d'aya tayi kuma tayi masa wannan gatan ne don yin masa shirin rayuwar barzahu daya fi komai tsayi da wuya musamman a wajen wad'anda basu aikata dai dai ba.....
Bayan wata takwas,
Abubuwa da sun faru, ciki har da rasuwar Baba a watanni biyar da suka wuce,
Haka kuma Mama ta je har gidansu Ahmad ta nemi gafaran ahlinshi tare da basu hakuri da kuma basu llabarin inda Mubarak d'in yake, bayan jin su Muhammad (Babandi) sunce su basu yafe ba, kuma Allah ya so shi sun tuba, da Sai sun d'auki ba.
Haka ta dawo gida jikinta a sanyaye.....
*Bayan shekara uku*
A shekaru ukunn nan abubawa da yawa sun faru ciki har da rasuwar Daddy wato (Mahaifin su Ahmad) dogon jinyan daya yi na tsawon watanni tara da sati uku.
Haka ma Mubarak, Allah ya am shi abunshi bayan zazzabin dare d'ayan daya daukeshi,
Haka kuma kafin ya rasu, sai da ko ina aka tabbatar da nutsuwa da kuma tubanshi, don har saukan da bai sauk'e a gidansu ba yayi a cikin dogon gidan jihad gombe.....
..Rayuwar gidan Mamy Alhamdulilah, suna zaune kalau da su Muhammad (Babandi), Abdullahi (Shaho) Bilal
(Oxle)
Tiger
Daya Musulunta ya koma (Sulaiman)
Bubaldu ( dama shi *Abubakar* ne) labar-bar (Musa).....Dukkasnu sun nutsu, sun dawo mutanen kirki yaran arziki, haka kuma tare suke zaune da Mamy a gidansu Sadiq d'in, kasancewar su dama marayu ne ba mai Uwa da Uba......
Sai yan Uwa da zumuncin yanzu ya zama sai a hankali.......
Haka ma rayuwar gidan Mama, babu abunda ya dame ta yanzu, domin ubangiji ya dora mata dangana, Fahad ma ta nemeshi har ta gaji daga sai ta yada komai ta fawwalawa Allah. Kana ta je kauyensu kuma ta d'auko yarinya da Maman ta rasu, itama ta samu ya gabanta mai rage mata kewa, Uwa Uba kuma lada da kuma falalan Rik[]e maraya.....
Back to labari........
[2/24