14

11 0 0
                                    

.......Anty Safiya dai tuni suka maida ita yar kallo a wajen, ta rasa wani irin magana sukeyi haka wanda ta kasa ganewa....


Sai dai bata zurfafa ba, ta kama bakinta tayi k’um dashi, don babu ruwanta da abunda ba'a sa ka ta ba, amma koma me ne ne. zata sani wata rana. (Niko nace idan sun so ba.)


Haka su Maman Twins suka tattara suka tafi, bayan dogon kashedi da kuma togaciyan da Maman  tayi wa Mummy akan Baby.

Hannun SIMRAH ta rike har bakin motanta, kafin ta sake hannun kana ta kalleta, sannan ta ce "kiyi hak’uri kinji Mamana, komai zai wuce kaman ba'ayi ba, insha Allah ya kusan zuwa karshe (wani karshe kuma a shekara goma.) "Amma gaya min idan kawai abunda yake damunki, Mummy tanayi miki wani abu?
Maman Twins ta kai karshen ayar magana tana kafeta da ido....



"Ba komai Maman Tw........
"Shiiiiii Maman Twins ta katseta tana mai cewa " "Ammy" na gaya miki zaki na cewa, no more Maman Twins, sai kuma idan ki na son ce wa Maman SIMRAH, ta k'arasa maganar cikin tsigar wasa.

Dariya sukayi dukkansu, kana ta k'ara ce wa "Ki daina boye min abu kinji, idan kinada damuwa ki fad'a min kai tsaye kar kiji komai kinji Daughter?


"To Ammy insha Allah,  haka Maman  Twins d'in ta bar gidan tana daga mata Hannu, tamkar bata son barin SIMRAH....


Haka rayuwar gidan yaci gaba da tafiya, kullum sai Maman Twins tazo gidansu SIMRAH, da yamma kuma ta koma....


Ranar suna yarin ya taci suna Aisha (Amrah) wacce Abba yayiwa had'uba da hakan, kana ya rubuta a cikin paper ya  bawa SIMRAH ta kawowa Mummy. A yayin da Maman Twins ta za6awa mata nickname, wato (Amrah) kaman yadda ta zabawa Simra.

Kallo ta k'arewa paper'n kana ta tab'e tare da  ce wa "Hmm to ni kuma ina ruwana. Ai sai ku jira Uwarta, idan tazo.... (Akwai wata Uwarta ne, bayan ke)

Aiko ba'a jima ba sai ga Maman Twins da manya-manyan kuloli shak’e da abinci, haka aka zuzzubawa makobta da abokan arziki.

Komai Maman Twins itace tayi tamkar ita ce mai jego,


Haka taron suna ta watse lafiya, sai fatan Allah ya raya mana Khadijatul-Kubrah.


Haka rayuwar gidan yaci gaba da lafiya, babu abun da ya canja, kullum Amrah tana hannun SIMRAH, don babu abunda yake had'ata da yarin yar daga bada no-no shi ke nan, wanka kuma sai Anty Safiya ta shigo take yiwa Baby'n.


Maman Twins  tana zuwa dubasu lokaci zuwa lokaci, haka ma kullum cikin tambayan SIMRAH take ko tana da damuwa , sai dai kullum amsan d'aya ne, "babu komai, har ta tagaji ta daina.


Bayan shekara d'aya, Mummy ta yaye Amrah kaman yadda ya yaye SIMRAH a shekara d'aya.


Haka kuma daga wannan ranar komai na Amrah ya k'arasa dawowa wajen SIMRAH, tuni Amrah ta zama bata da Uwar da ta wuce SIMRAH don itace komai nata...


Kullum suna shiga D'akin Abbansu, inda zai saka su a gaba yayi ya hawaye,  ko kuma ya dora hannayensa a kan kayukansu yayi musu addu'a.

Tun Amrah bata fahimtar komai har ta fara fahimta,


Haka kuma Mummy bata rugewa SIMRAH komai ba, na daga cikin wahalan da take bata, Amrah tana giram itama abunda ya shafi SIMRAH yana neman shafanta.......✍️





Back to labari.



Manage please

[

WATA UWARWhere stories live. Discover now