_____Lectures d'in 8 take dashi, hakan yasa tun 7:30 ta gama shiri, sa bo da sanin halin lecturer d'in da tayi……
Ammy tayiwa sallama da niyyar tafiya… Hannu ta d'aga mata alamun ta tsaya, dakatawa tayi daga mik'ewar da zatayi……
nan ko ta dauk'i wayanta dake gefenta, yan danne-danne tayi, kana ta kara a kunnenta………
Ringing biyu ana uku aka d'aga, "lafiya kalau," a ummaki na?? Dan shuru kad'an kana ta ce "ok please zo ka sauk'e min Simra a skull yanzu, kar tayi letti, ok please kayi sauri, tana gama fad'a ta sauk'e wayar daga kunneta, kana ta maida kallonta kan Simra,
"Ki jira kad'an Yayanku zai zo ya sauk'eki,"
Idan tace taji dadi maganan to lallai ta tabbata cikekkiyar mak'aryaciya, sai dai kasan cewar musu ba dabi'anta bane tun tana yarinya, haka kuma bazata so farawa a yanzu ba, a yanzu ma akan Ammy ba, hakan yasa ta ce " to Ammy, tana mai lank'wasa yan yatsunta, a yayin da kanta yake kasa……
Tayi zaman …15… minutes bai zo ba, hakan yasa ta ce wa Ammy tana zuwa, ta tashi ta shiga D'akin dake mallakinsu don shiga toilet, sa bo da period d'in da take, kasan cewar tana da yawan shiga toilet idan tana wannan halin,,,,,, hakan yasa direct ta nufi toilet d'in dake cikin D'akin don gyara jikinta……"Ki fita yana jiranki a mota cewar Ammy, wacce take gayawa Simra, da fitowarta kenan,,,,,, kai kawai ta jinjina mata, kasan cewar ta mara son magana wato (miskila),
"Na tafi Ammy,"
"To Allah ya bada sa'a ayi karatu lafiya." Da
"toh," ta kawai ta masa a yayin da take tafiya………
Cikin sauri sa bo da lettin da take ganin tayi, gashi tasan lecturer'n bashi da mutunci ko kad'an, don zai iya hanata shiga Lt d'in idan ya riga ta shiga, kasancewar dabi'arsa ne haka,,,,,,,
Tafiya take a hankali cikin shirinta, na atanfa kiran chiganvy kalan jaa mai ratsin coffe brown da fari, an mata d'inkin fitted gown wanda ya amshi jikinta ya zauna mata d'amas, hijab ne a jikinta coffe brown, wanda ya dace da kekkywar fuskarta……
..…tafiya take cikin taku da kuma zallan nutsuwan da Allah ubangiji ya d'iga mata……
kanta na kan tsintsiyar hannunta data d'aurawa agogo tana kallon time.....
★★★
Ido ya tsura mata ganin yadda take tafiya kaman wacce k'wai ya fashe wa a ciki, tsaki yaja a karo na ba adadi……… Sunkuyawar da tayi shi ya hana shi samun k'arewa fuskar ta kallo.
"Wato duk yadda kake sauri muddin da mace kake tafiya to sai kaga nakasu a lamuranka, jibi yadda take tafiya kaman wacce bata da Jini," yayi kwafa daga lokacin daya kai ayar tunanin da yake rayawa a cikin Zuciyarsa……
"Ina kwana,
"ya tsinkayi siririyar muryanta, jinjina kansa kawai yayi, ba tare da yace komai ba sbd shi bud'e baki da sunan magana a wassu lokutan yakan bashi wahala ainun….…
Tana gama dai-dai ta zamanta, ya figi motan yayi reverse, mai gadi ya bud'e masa get, ya cilla hancin motan a kan kwanceccen ti-tin dake malale a K'ofar gidan da kin fita, direct hanyar da zai sada su da A.T.B.U sukayi, cikin speed d'in da ya k'arawa motan.....
***
Acikin motan babu mai magana, sai sautin karatun dake tashi a hankali, a haka har suka shiga cikin makantar......