Jikin Sadiq, sai dai muce Alhamdulilah, ba laifi yana samun sauk'i dai-dai gwargwadon iko.....
Tabbas Mamy taga canji ainun a wajen d'an natan, yadda ma ya zama a yanzu ba haka yake tun farko ba.....
Mutum mai magana da wasa da dariya ga barkwanci, da faram-faram da jama'a ya zama haka? Shuru-shuru sai dai ya tsurawa waje d'aya ido yana kallo, a duk lokacin da ya tsurawa waje daya kallo, ita d'in Mahaifiya ce, hakan yasa take iya karantarsa, har take iya ganin zallan b'acin rai mai had'e da tak'aici akan kekkyawar fuskarsa....
Lallai akwai matsala ta ayya na ranta, sai dai bata san ta ina zata fara ba....
A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah buwayu gagara misali.... har Sadiq yayi sati takwas a cikin Asibitin, wato ⁴ months kenan da yin accident d'insa, zuwa wannan lokacin kuwa tuni karayar dake jikinsa su ka had'e, haka ma sauran ciwukan dayaji....
Sai dai har zuwa kawo wannan lokacin, babu wani canji na daga rashin maganan daya koya a bagtatan...
Yau ma kaman kullum, kishingide yake akan gadon asibitin, ya []urawa waje d'aya ido, a yayin da fuskarsa kuwa ta bayyana zallan b'acin ran, hakan yasa har Mamy ta shigo D'akin bai sani ba....
Ido ta kura masa ba tare da tace komai ba, sai dai ta tsaya ne tana nazartan fuskarsa da yanayinsa...
Numfashi ta sauk'e a boye, a ranta ta fara raya. "Nasan shi, nasan waye d'ana, don haka nasan ruwa baya tsami banza, lallai akwai abunda akayi masa kafin yayi accident d'innan, ko kuma abunne ya sashi cikin wannan halin, Allah dai shi ne masani, ta kai ayar maganar tana sauk'e numfashi....
Koma dai me ne ne dole ya koyi yadda zai yarda da kaddara mai kyau ko akasin haka, tunda ya kasance Musulmi, haka kuma mumini mai cikecikekken imani.....
Ai ita rayuwa ba haka take ba, komai ya sami bawa dole yayi hkr, musamman ma shi da yake mai ilimi dai dai gwargwado....
zama tayi a gefensa kana ta dafa kafadarsa... cikin sanyin murya ta fara fad'in
_" ita wannan rayuwa tamkar matakalar be ne haka take, kana hawa wannan kana sauk'a daga wancan, sai dai ka sani duk wanda zaka hau kafin ka sauk'a sai kayi hak'uri, if not kuma wallahi sai dai ka tsaka a step d'aya ba tare da kayi gaba ba, idan kayi wasa kuma komawa bayan ma zai iya gagaranka....._
_Ban damu dana san me ne ne ainihin abunda yake damunka ba, ko kuma sanin wanda ya maka abun ba...._
_Sai dai ka sani yarda da kaddara dole ne akan ko wani musulmi na gari muddin yana son ya zama nagartaccen bawa....._
_Ita rayuwar nan da kake gani komai zaka bi bi sai ka samu 'kalubale, haka kuma dole kayi hak'uri muddin wata nasara kake son cimmawa......_
_Ka kasance mai yafewa mutane akan laifin da suka aikata maka gudun tashi da Zunubai biyu, ga na gaba sannan ga zunubin ri[]e mutum a cikin Zuciya wanda kai ma kasan hakan haramun n... bazan saka ka yafewa Wanda ya maka laifin ba, domin kuwa ko da ka yafe baka da lada kaman yadda Anas ya rawaito cewa انما لصبرعند ا لصدمة الأولي>>
_( lallai shi hak'uri yana zuwa ne a mataki na farko....__Abunda hadisin nan yake hora bayi dashi shi ne, "da anyi maka laifi kawai ka yafe, da an zalunceka kawai ka yafe, tun lokacin da aka maka.... Sannan kuma ka yafe sabida Allah, ba don duniya, matsayi, so, ko wani abu ba...._
_Tun farko ya kamata ka yafewa wanda ya maka wannan abun, ba wai sai yanzu da nayi maka maganan ba..._
_Allah yana son bawa mai hak'uri da kuma saurin tafiya, domin idan bawa ya cika yafiya, Allah ya kany magana wanda zai sa mala'iku su ji ya kuma ambashi sunan wannan bawan sannan ya shaida musu da ya yafe wa wannan bawan, bayan ya fad'a musu abunda wannan bawan ya kasance yana aikatawa..... Ita tafiya tana da dad'i kuma tana da sauk'i muddin ka dora Zuciyarka akan hakan....._