34

10 0 0
                                    

*Waye Sadiq???*

•––––––•Alhaji Isma'il Madu shi ne asalin sunan Mahaifinsa, haifeffen  jihar Gombe ne, wanda ke zaune *Shongo Housing Estate*......

         Yana zaune da Matarsa d'aya, Hajiya Asma'u (Mamy) sai yaransu biyu Duka maza Abubakar shi ne babba sai Ahmad.....

          Alhaji Isma'il mutum ne mai sanyin hali da sanin ya kamata, haka yake zaune da mutanen anguwa lami lafiya......

      Haka ma Hajiya Asma'u wato (wato) Mamy, mace ce mai mutunci da kirki.....

Hakan yasa yaransu biyu tashi cikin tarbiya da tsawatarwa....

    Sadiq shine wanda ya d'auko halin iyayensa, a yayin da Ahmad kuma yayi daban, don shi d'in ya kasance irin fitinannun yaran nan ne da basa jin magana ko kad'an......

      Tun tashin Ahmad iyayensu suke damuwa da halin Yaron, sbd shi yaro ne da ba'a tank'warashi, idan yasa kansa a gabar to babu mahalukin da zai juya shi, Alhaji Isma'il (Daddy) yana shiga cikin tashin hankali matsananci idan ya yaga halin Ahmad, haka idan ya duba gobensa.....

      Hakan yasa bai gushe ba wajen ro[]on Allah akan shirya masa shi.... 

    A yayin da Sadiq kuma yake mai sanyin hali, ga dariya da wasa da mutane......


       Haka suke zaune gidan, cike da soyayyar junansu tamkar zasu hadiyi juna.....

       Ahmad ba wai rashin tarbiya ba ne yake damunsa, illa haka yayi SA....


      A lokacin da yaran suka girma, ta kai sunyi nisa a matakin karatu, sai abunda Daddy yake gudu ya faru, wato akan Ahmad,

      Sai ya fara biyewa abokan banza, hakan yasa halayensa suka juye daga miskili zuwa k'angarerre.... Kwata-kwata sai ya dawo baya jin maganan kowa, duk da a lokacin yana  *ss³* ne, a yayin da Sadiq kuma yake ⁴00 Level a jami'an Kashere, inda yake karanta Business_Administration burin Mahaifinsa ne, kasan cewar Alhaji Isma'il Madu, cikekken an kasuwa ne....


      Tsakanin Sadiq da Ahmad akwai ratan shekara *⁴*.......

       Ahmad yana *ss³* sai dai abunda yakeyi yafi na d'an jami'a ma, don har operation suke fita idan dare yy, haka kuma yana cikin yaran da idan anzo zabe ake d'aukan hayansu sa bo da tada tarzo ma, jikinsa baya rabuwa da makami, especially waist d'insa baya rabuwa da k'ananan wukake.....

      *...Bayan ...Wani ...Lokaci*

        A zuwa nan, Sadiq ya jima da Gama gama degree d'insa na farko, hakan yasa ya fad'a a na biyu wato (master's)....


      Ahmad kuwa, tunda aka samu ya gama secondary d'in ma, don daga shi ya dasa aya, da Daddy ya damesa ma sai ce masa da yayi ai shi ya gama boko.....

     Hakan yasa kawai suka zuba masa ido, musamman Mamy, wacce har halinsa yaja mata ciwon hawan Jini, da Karin kuma akan dangi Mahaifinsa ne, da suke d'aura laifin akanta......

  

                ★★★

  Fad'a ce - fad'a ce, shaye -shaye, Sara da suka, fada makami, wadannan sune halayen Ahmad, sai dai shi abunda bayayi shi ne neman mata, kwata-kwata mace bata bata gabansa, a cewarsa mata suna da raini, shi kuma a rayuwarsa idan akwai abunda ya tsana to a bayan raini yake......

     Idon kaga Ahmad aka ce maka d'an Alhaji Isma'il ne, sai ka kama baki sbd mamaki, domin kuwa albasa batayi halin ruwa ba


       Ahmad idan akan halinsa ne, sai dai na ce likkafa taci gaba, don masifa taci Uban na da, tuni Zuciyarsa ta kyankyashe, ya dawo baya tsoron kowa, jikinsa duk ciwo, prison ya je yafi yau goma sha, cell kuma ba'a magana ma, don tamkar D'akin Mamy haka ya dawo da cell domin babu ranan da baya zuwa, daga karshe sai daya zama customer......


        Farin yaro tuni shaye-shaye ya dishar dashi, kansa yasha askin Dada, wanda yy dying dinsa, still kuma ya mummurd'ashi, jikinsa duk cike yake da ciwo, tamkar mai wasan boxing.....

      Haka wata rana za'a dawo wa da Mamy shi bai san ko inda kansa yake ba.....


   Uwa ce, haka zata saka Sadiq gyara shi, ba yadda suka iya....


   Tayi fad'an, tayi holo, tayi nasihan, wata rana sai kawai ta fashe masa da kuka tana rokonsa, sai dai kawai ya ce mata ki yafe min kaddara ta ce a haka Mamy, nima ba'a son raina nakeyi ba, sai ya kare da ce mata "so rajapo,"
         Daga haka sai ya tafi abunsa.......

                     .....Haka rayuwa tayi ta yi tafiya, komai yana canjawa.....

   Har zuwa wannan lokacin Sadiq baiyi Aure ba, yana nan zaune, Mamy tayi magana har ta bari, sai ya ce mata yana jiran wata yarinya ne kawai ta taya shi da addu'a.....

       Ahmad ba abunda ta canja na daga halayensa, sai ma abunda yayi gaba, sai dai lokaci zuwa lokaci yakanji  yana daffff da canjawa......



     ~!....Bayan kwana biyu....!~

    Sannu a hankali, sai halayensa suka fara canjawa daga munana zuwa masu kyau, haka kuma sai rashin dariyar'r nan ya dawo tamkar a da chan.....

       Mamy da Daddy sunji dad'in wannan al'amari ainun, especially ma  Mamy, don sai dai data jera kwana bakwai tana azumtarsu sa bo da godewa Allah mahalicci daya shirya mata d'anta a lokacin da batayi zaton haka ba, haka ma Sadiq.....

        Haka rayuwarsa taci gaba da gudana, ba wata matsala, don a yanzu basu da damuwa ko kad'an saboda dama damuwar ta sun bata wuceAhmad d'in ba ne.....

            Wata rana Ahmad ya fita da yammacin ranan ba tare da Mamy ta sani ba, saboda hanashin da tayi, tàce masa kwata-kwata bata son yayi nisa da ita, tanajin wani irin yanayi akan hakan.......

            Da yamma bayan ta shiga D'aki don yin sallan daya samu daman mata wayo wajen tura ta yinsa sabida shi ya rigata yayi nasa dalilin fitan da yake son yi, aiko tana shiga wuffff yayi shima ya kama hanyar waje........

 

                          ....a lokacin daya kai get na karshe a gidan, wanda zai sadashi da asalin K'ofar gidan, yayin daya d'aga kafarsa da niyyan fita, sai yaji wani irin yanayi na daban, hakan ya tilasta masa juyawa ya k'arewa gidan kallo......


      Kansa ya d'aga sama, dai dai kam window d'in D'akin Mamy, a nan kuwa yaci karo da ita tana tsaye acikin balcony d'in da ta zo rufe kofarsa, sbd iskan yammacin dake shiga mata D'aki, nan ko idanunsu suka cikin na juna, kallon da yake mata ba ko keftawa kaman yadda itama ta kura masa nata, wanda ruwan Hawayen da bata san ko na me ne ne ba,,,,, hannyensa ya had'a mata alaman rok'o kana ya ka[]a mata kai,

     Kai kawai ta jinjina masa alamun ta yafe ba komai,

         manuniyar yatsarsa na dama ya lonkosa kana ya mik'e babban yatsansa, sai hakan ya bada alaman Half_Heart kaman yadda kurame suke yi, ya saka dai dai kan kirjinsa ta dama inda Zuciyarsa take,   kana sai yayi tamkar ya mi[]a abun, alaman *"I love you"*.......

         Jinjina masa kai tayi, kana itama ta mayar masa tare da kara masa   alaman too, wato *"I love you too"*
A yayin da idanunta suke zubar da ruwan hawayen da bata san ko me ne ne ba, haka kuwa ka wani murmushi da ke fuskarta mai had'e da damuwa, at the same time tana dariya kuma hawaye suna zuba....


           Sai dai tana san a kasan Zuciyar ta wani irin yanayi takeji mai kama da rashi, kewa, da kuma rauni.......

        Cikin wannan da yake jin Zuciyarsa ya juya shima, ya d'aga kafarsa, yana jin tamkar KADA ya fita, sai dai wani abu yaje ji mai kama da ingiza, ji yake idan bai fita ba to komai zai iya faruwa.... Hakan ya tilasta masa daga kafarsa zuwa waje.....

        Cikin k'arfin murya, muryanta ya riski kunnuwansa, yaji ta ce 

       
      "Ahmaaaddd!!!

Juya wa yayi, kawai sai ya mata alaman bye-bye daga haka ya fita ko sake waiwayowa baiyi ba.......✍️

WATA UWARWhere stories live. Discover now