25

10 0 0
                                    

………Kallon zakici k'aniyarki ya mata, ganin bata ko d'ago ba ballen tana ta nuna  ta san da wanzuwar mutum a wajen……

   …Afrah kuwa sai data gama abunda takeyi a waya, kafin ta tashi ta shige toilet d'in bayan ta rage kayan jikinta,,,,,


     Wankan da bai d'auketa lokaci mai tsayi ba, ta fito jikinta na daure da madai-daicin towel, wanda ya d'an tsaya mata iya cinya, sai k'aramin dake hannunta tana goge daga gefen fuskarta zuwa cikin kunnenta zuwa wuya, bata ko kalli inda yake ba, (dama haka Allah yayi Afrah, akwai ji-ji da kai, da kyaliya tamkar yar gidan Uban wani) direct gaban mirrow ta je ta ja kujera ta zauna nan ko ta hau shafe-shafe da kayan data gani akai,   a yayin da shi kuwa Fahad ya kureta da ido kaman tsohon maye, don har wani lashe lips yake, sabida kallon da yake k'arewa halittan jikinta daya gaji da shan man bleaching, don shi d'in d'an iskan jarabebben ne na bugawa a jarida, da baya ganin mace ya kyale komin tsadarta, haka kuma komin wayonta, don wani irin wayo Allah diga masa, tamkar zomo……


    Bai ce mata komai ba, kaman yadda itama bata ce masa k'ala ba, sai dai a ransa yake raya "zakici Ubanki da mai da yaji, idan har tsautsayi ya kawoki hannunna,tunanin hakan da yayi yasa yayi kwafa ya ciji lips d'insa na k'asa, yana ayyana abubuwa  da dama a ransa.
    

'''


'''Har dare suna cikin gidan, hakan yasa tasan kwana zasuyi, don haka bata wani damu ba, sabida sabon da tayi dashi, tamkar wan Ubanta ko na Uwarta.




    …Da daddare suka kwana a daki d'aya,  gado d'aya, a cikin blanket d'aya, bayan wasanni masu tsayin da suka wanzu a tsakaninsu, kana suka shiga jikin juna sukayi bacci tamkar wassu mata da miji…





    Washe gari babu Salla haka sukaci gaba da shagalinsu, babu mai fita sai shi, time to time yana fita yana siya musu abinci, da ya dawo kuwa zasu shige jikin juna, hakan kuwa ya k'ara musu kusanci mai tsananin gaske,



     Fahad d'an duniya ne, yasan ta inda zai tafiyar da macen da daya lura da akwai irin wannan tsoron a ranta, hakan yasa ya 6ullowa Afrah ta haka,


   Hakan ko da yayi ba k'aramin nasara yayi ba, don hakan yayi ya samu nasaran tafiya da kaso tamanin da biyar cikin d'ari 85% na tsoron dake cikin Zuciyar Afrah. Hakan yasa har take jin tamkar ita dashi babu wani ban-banci, a yanzu tsoron daya ragewa  Afrah kawai na zafin da aka ce mata anaji a first night, bayan wannan babu wani tsoro……


    Wasa-wasa Afrah kwananta uku a gidan ita da Fahad ba tare da ta koma gida ko ta nemi Mummy ba, hasalima bata tuna wata Mummy,  sha'aninta rayuwarta kawai take gudanarwa…


     A yau da daddare dawowarsa kenan, daga siyo musu abincin dare daga AROMA RESTAURANT,tana zaune a kan kujera tamkar ba Sarakiya yaje kitchen ya d'auko musu plate da cups, ya zo ya juye musu abincin, nutri milk mai sanyi ya tsiyaya mata a cup d'inta, bata d'ago daga dannawa wayan da take ba, (don Afrah lamba d'aya ce, wajen jarabar Danna waya, sabida tiktok d'in da takeyi, a nan take koyan steps d'in rawe-rawen da takeyi,) hakan ko ya bawa Fahad daman fakaitan idonta yayi anfani da wannan daman wajen jefa  kwayar dake cikin hannunsa kana ya saka teaspoon d'in dake hannunsa ya dinga gaurawa  har sai daga tabbatar da narke kafin ya ce  "Sweetheart bissmilahi, sauk'o kici abinci," kasancewar tana jin yunwa sosai hakan yasa ba musu  ta sauk'o ta fara ci tana had'awa nutri d'in da ko d'ar bata ji ba akansa har ta kusan cinyewa, kafin tayi gyasa, hakan ya tilasta mata mikewa tayi D'aki, don yin brush……
'''


    '''(Don Allah iyaye ana yiwa Yaya addu'a, domin addu'an iyaye akan Yaya ba k'aramin tasiri yakeyi akansu ba……

Ko wani bawa bashi da iko ko hurumin goge zanen kaddaransa da alkami ya riga da ya zana, kaman yadda duk abunda aka zana sai ya faru, ana zana zanen kaddara daga lokacin daya cika kwana arba'in, ya canja daga gudan jini zuwa gudan tsoka, kaman yadda yazo a Hadith na hud'u cikin annawawi…… )

WATA UWARWhere stories live. Discover now