10

19 0 0
                                    

...Daga shigarsa cikin D'akin, kallo ya k'arewa D'akin, da kuma yanayin yadda suke kwance, kallonsa ya mayar kan Mummy, wacce kallo d'aya ya mata ya gane ba bacci take ba, kawai dai tayi shuru ne. Duba da yadda take lank'wasa yatsun kafarta na hagu.....

K'arasa shigowa cikin D'akin yayi, kana ya tsaya a kanta...

Cikin danne b'acin ran dake taso masa ya ce "Hauwa'u, Hauwa'u, Hauwa'u!! na ukun ya k'ira da k'arfi, bata amsa ko guda d'aya ba, illa juyowan da   tayi kana ta masa kallon "how far,?

"Amma bakiji Yarin 'yar nan tana kuka bane? fad'an Abba, "Kai ma daka fito daga waje kaji ballen tana ni  da muke D'aki d'aya.  Mummy ta bashi amsa kanta tsaye."

Abba ne ya k'ara fad'in "Amma kuma kika barta tana kuka haka?

"To me kakeso nayi mata? inji Mummy, Abba ne ya kalleta kana ya ce "to please ki d'aga ta mana.

"Nikam bazan iyaba, don na gaji, tunda garin Allah ya waye nake abu guda d'aya, Yarin yar sai shegen kuka, kuma idan baka son jin kukanta, ga ci kaman wuta, ai zaka iya mata abunda zanyi matan, ta ida maganar tana kallon gefe.

kallonta Abba yayi cikin danne wani kullutu daya tokare masa makoshi,  ya ce "Haba Hauwa'u, wannan wani irin abu ne haka? kiyi hakuri ki d'auketa don Allah. Kinga yarinya ce, bata san komai da ke wakana a duniya ba, kiyi hakuri ki bata kinji Kuluna."


Sai da Abba ya bata lokaci mai tsayin gaske yana rarrashi Mummy kafin ta jawo Yarinyar ta hanyar janyo kafarta guda d'aya.

Idanunsa ya runtse lokacin da  Mummy ta jawo kafarta d'aya, ba tare da ya ce komai ba yasa kai ya bar cikin D'akin, sa bo da gujewa Abunda zaizo ya dawo, don za'a iya kai matakin da Zuciyarsa bazata iya jurewa ba....


Domin yasan muddin ya tsaya to wallahi abun bazai musu kyau ba, shi dai mutum ne mai hak'uri, sai dai dama ance ja guji fushin mara fushi......

   D'akinsa ya koma, yayi wanka kana ya kwanta akan gadonsa, ya jingina da allon gadon yana tunanin abunda ya canja Mummy daga wannan haihuwar......



Kwata-kwata ya lura tayi mugun canjawa akan wannan haihuwar, abubuwan da  batayi yanzu su takeyi, meyasa bata wannan rawan kan da tayi tayi a lokacin data haifi Afrah?

Ko dai haka mata suke basa farin cikin haihuwa ta biyu kaman na fari?

Kenan hakan na nufin sunfi son haihuwar fari akan sauran haihuwar da zai biyo baya? Kenan bayan haihuwar fari basa k'ara son na bayan???

     Duk mata haka suke kodai tashi matar ne a haka? me yake faruwa da Mummy???


    …… Mene ne mussabin wannan canjin da yake hangowa a tattare da ita??? kodai shi kad'ai ne mai ganin wannan canjin? haihuwar Afrah ta banbanta dana wannan Yarin yar ne????


   ...Ganin bashi da wad'an nan amsoshin ya shi sauk'e numfashi, kana ya lumshe idanunsa ba tare da ya motsa daga inda yake ba......



Mummy kuwa ba tare da tayi tunanin Yarinyar bata koshi ba, ta tugeta  daga Shan no-non.

Jin an cire no-non a  bakinta yasa ta bud'e baki tare da fara kuka, aikuwa Mummy yatsunta biyu ta saka ya doki bakin Yarin yar, sanadiyyar hakan yasa Baby'n yin k'ara, wanda  yasa Abba shigowa D'akin ba shiri.

Kallonta  yayi, cikin rashin yadda ya ce "Hauwa'u, meke faruwa ne haka Yarin yar nan take wannan ihun, ya ida maganar yana karasowa cikin D'akin.


" taya zan san abunda yake damunta bayan ba magana take yi ba, ni wallahi na gaji, inji da  kaina ko inji ihunta, cewar Mummy da idanunta ke kan Afrah wacce ke zaune tana rik'e da k'aramin roban na 'Fresh yoo'

Matsowa Abba yayi da niyyar sake magana, sai dai inda idanunsa suka fad'a ne yasashi razana.

Cikin sauri ya wafce Yarinyar daga hannun Mummy, yana kallon bakinta daya fashe har yana d'an zubar da Jini kasancewar ta mai sabon fata....

Cikin tsawa ya ce "Hauwa'u! me kika mata!

Mummy ta tsorata jin yadda ya kira sunanta, amma sai  ta dake ta ce"Baka gani ne da sai ka tambayeni ko kuma idanunka ne suka samu matsala?
cewar Mummy,


Abba ne ya kalleta kana ya ce
"Me kike nufi da Yarin yar nan? tunda aka haifeta na lura.kwata-kwata bakya sonta, duk akan mene ne? ita ba 'Yarki ba ne? ko tana da bam-bam ci da Afrah?   rashin imanin har ya kai ki daketa  tana Yar Jinjira haihuwar cikin satin nan?

Kiga bakinta, Yarin yar da bata gama tan-tan ce mene ne duniya ba, amma har kin iya d'aukan Hannu ki daketa, kiga yadda kika fasa mata baki.

"Idan ba rashin sanin ciwon kai ba, ina aka tab'a jan yayeyye a jiki, a watsar da wanda aka haifa a yanzu-yanzu? ke wani irin hankali Allah ya miki?

" kalan hankalin daya maka!, kuma wallahi ya isheka haka Yusuf! kar kaga nayi shuru kayi tunanin tsoronka ne yasa  haka, wallahi ko kad'an, sannan ka sani kana cikamun kunne ni da Yarin yata.


"Duk abunda kakeson ka fad'a ka fad'a nayi kuma zanci gaba dayi, kayi abunda zakayi,

"Sonta ne banayi, haka kuma bazan yi ba,  ai ba dole ba ne, ba kuma lallai-lallai ba ne sai ka so abunda ka  haifa ra'ayi ne,  don haka bana sonta, kuma bazan so ta ba! numfashi taja kana taci gaba da ce wa

"Wallahil- Azeem idan baka daina cikamun kunne ba, Allah d'aukan wannan shegiyar Yarin yar zanyi nayi firo da ita,  sa bo da na gaji, daga ni har 'Yata. Yo idan ba ciki ba mezai sa ta zauna a cikina har na zo na haifi wannan abun, ta ida maganar tana nuna Babay'n da ke hannun Abba,

Cikin danne b'acin ran dake tunkaro taso masa ya ce " Hauwa'u ko wad'i a yid'a gel, ba no gid'irda  bandigel? (Hauwa'u meyasa bazaki so ta ba, kaman yadda kikaso Yar Uwarta ba?)

"Eh me yid'a gel bo mi yid'ata gel, cewar Mummy,

Abba wanda idanunsa tuni suka canja colour sa bo da zallan b'acin ran da ya ke ciki ya ce......









*#Comment,*
And
*#Share fisabilillah.*



*'Yar Gata ce*

WATA UWARWhere stories live. Discover now