––––––––––––Yana fita bai zame ko inaba, sai inda suka saba zama shi da abokan banzan da suka kasance abokanan huld'anshi a da kafin Allah ya aiko masa da shiriya....
Wani irin yanayi yake ji mara misaltuwa, baya jin dad'i ko kad'an, don wuyansa har wanki d'aci-d'aci take masa, kana ga kuma sanyin dake shiga jikinsa ta hanyar bin K'ofofin gashin dake jikinsa.....
......Sai dai duk da wannan yanayin da yake ji, hakan bai hanashi zama a inda suka saba ba bayan ya samesu, suna ta holewansu kasancewar da yamma ne.
Sunyi farin ciki ainun da ganin sa ainun, nan suka fara masa gaisuwansu na Chauuu-chauuuu ⚔️⚔️⚔️ kalan dai nasu.....
_(Kasan cewar dama shi ne babba a wajensu, sai dai tubansa bai SA sun tuba ba, hakan yasa suka d'aura Babandi, saboda abokin Ahmad d'inne, haka kuma tamkar shi ne mataimakinsa a lokacin da yake wurin, suke ganiyar Sara suka.)_Baiyi magana ba, illa guntun murmushin da yayi musu.
Basuyi ba mamaki ba, sannan kuma hakan bai damesu ba, don dama idan miskilancin sa ya motsa hakan yake musu.
Zamansa da 5 minutes, kuwa aka kowa wa dabansu hari, nan abokansa suka mik'e aka fara wani irin fad'a mai kama da yak'i, dukkansu da makamai a tare dasu, akasin Sadiq, da babu komai a hannun sa, dai dai da pen, hasalima ko tashi daga wajen baiyi ba, sabida shi a wannan lokacin halin da yake ciki ma ya isheshi......
Sun d'auki a k'alla tsawon ¹5 minutes suna wannan fad'an, ba tare da ko wani 6angare ya ji ya gaji ba, sai dai zuwa wannan lokacin an samu nasaran kashe ko wani 6angare nasu.....
.....Kaman kyallawan ido, Mubarak d'an gidan _Hon. Garba Abdullahi D'an buram_ ya kalli Ahmad zaune, dama ya jima yana jin haushinsa, ga kuma abunda sukayi wa kanwarsa, hakan yasa yayi murna da wannan operation d'in, cikin azama yayi kan Ahmad da wuk'a a hannunsa, don a wannan lokacin bashi da burin daya wuce ya kashe Ahmed ko zaiji ya huce....
Babandi (d'an team dinsu Ahmed ne na da) ya kalli abunda yake shirin faruwa, cikin tsoro da kuma gudun abunda zai faru ya k'walla k'ara da karfi ya kira sunan Ahmed yana mai shaida masa abunda zai faru......
.....Sai dai kashhhhh Ahmad bai ji ba, sakamakon nisan da yayi a wata duniya, a dai-dai wannan lokacin ne kuma Mubarak ya samu daman isa gaban Ahmed tare da daga Hannu ya caka masa Wuk'an, wanda ya sameshi a dai dai ciki ta gefen dama.....
......."Nooooooooo!!! Babandi ya fad'a da k'arfi, yana tahowa, wajen a mugun guje, kafin ya iso har Mubarak ya yi nasaran sake da6a masa wukar a karo na uku......
*•···–––––––*"Slimmmm,"
......Shi ne abin da Afrah ta fad'a a matsayin sallaman da addinin musulunci ya koyar, wato "Assalamu alaikum" wacce shigowar ta kenan daga yawon gantalin data sarawa Sanda......"Ke kuma daga ina haka Afrah? Kuma wannan shi ne sallaman da zaki min a matsayinki na musulma yar musulmai?
"Oh god Mummy," nifa ba zuwa gurinki ba a dami mutum daga zuwansa, zan iya zama?
"Yaushe kika fara tambaya na akan zama?
"a'ah to na sani ko an fara hana zama sai da neman izni, fad'ar Afrah.To rasa kunya, daga zuwanki zaki fara Sana'a, to wallahi tun kafin mu fara raba hali ki 6acewa ganina..... Mummy ta kai karshe maganar cikin b'acin ran ganin da tayiwa Afrah, kallon yadda Fuskarta ta k'ara kwailewa yayi haske na ban mamaki, a yayin da ita kuma ko lokacin shafa Vaseline ma bata dashi ballen tana wani shegen mai wai shi na bleaching....
Cikin halin ko ina kula Afrah ta ce " bama kwana zanyi ba nikam, atoh banyi wannan arahar ba ehe.," ta fad'a tana wucewa, a yayin da bakinta yake raira Wak'ar.
_······″Wata rana zaku ga d'a na in saka mishi pamper's..... Ni da wanda nake k'auna ya bani K'udina rapers, sai inje kasuwa siyyayya kawaye na su min rakiya....._Da ido kawai Mummy ta bita, bayan minti biyar ta sake fitowa jakanta a hannunta.... Kallon Mummy tayi kana ta ce
Manage please, ku tsammaceni da dare in sha Allah....