______"Afrah! Afrah!! Afr.........
"Chaiiiiii Innanillahi wa inna illahirraji'un, wannan wani irin k'ira ne kaman na karb'i bashin ki Mummy? Kira da sassafe haka? wallahi ni dai idan bazaki kyaleni ina hutawa ba wallahi zan bar miki gidanki, don kuwa ina mai gaya miki nema na zakiyi ki rasa batttt tamkar yadda Buhari yasa aka canja kudi a karo na biyu ba ba tare da kowa yayi tsammani ba, Afrah ta ida maganar tana juya ido.
"Hmmmm rasa kunya 6eran danga, nikam ba wani abu bane, illa aikin da zaki kama min a kitch………
Ewwwww! Disgusting…… Mummy kiiiiiii what? Ni Afrah ne zan shiga kitchen da sunan girki?? God forbid wallahi…
Yaushe kika canja haka? Karki manta ke ce kika sanar dani cewa ni ba irin matan da zan ke wahala bane, ko ba haka ba? Sai kuma yau zaki bijiro min da maganan k'wa-k'wai? Chapppppp banyi wallahi, (ni ko nace ko dai baki iyaba ba)
Numfashi Mummy ta sauk'e, a ranta kuwa take fad'in " magana zarar bunu, Ashe rana irin wannan zai riskeni, lallai nayi nadaman zaunar da Afrah ina tusa mata karatun da bashi anfani, nikam naga ta kaina Hauwa'u,"
Karan da wayan Afrah yayi ne ya katse mata tunani,
"Hello Sadeey, duniya shuru Kin 6uya,Dariya tayi kana ta ce, lafiya nake, ya Anty? Masha Allah,
Daga haka tayi cikin D'aki.....
Da ido Mummy ta bita a yayin da idanunta kuwa suka kada sukayi
ja kaman Borkono, Lallai Afrah tana da masifa da rashin kunya, sai dai tasan abun ya k'aru, ba kaman da ba, kuma ta lura a wannan tafiyar ne komai ya canja, bata san ina taje ba, tayi-tayi ta gaya mata inda taje amma abun ya faskara…….Gaskiya da sakel wannan lamari akwai rud'arwa aciki, dole ta San me ke damun Afrah kwata-kwata ta kasa gane kanta....
(Gashi ita ba mota ba, ballen tana a bata ammasco ko da kuwa vital 500sm ne)
Washe gari
"Mummy Sadeey zata zo da masoyiyar ta, wacce ta zo daga Katsina, me zaki dafa musu?????
"Ni ce ma mai dafa musun sbd baki da hankali kanki ba Ongaa? Ki shiga man ki dafa musu, wallahi ki shiga ruwan hankalinki,"
Mui-mui haka bakin Afrah ke yi, "ohh yau d'in ma k'unkunin kike min? Wallahi zan dauje bakin ki Allah kuwa, ke sbd baki da hankali ni Uwarkin ce mai dafawa k'awayenki abinci ke me kikeyi daga garin Allah ya waye? Kina nan kaman kashin maciji ba taki ba magani, kullum kwance kaman ruwa, daga charting sai waya,"
"Wallahi Mummy na gaji da goranta min da kikeyi, wai da kike maganan girkin kam, kin koy min ne? Tunda baki koya min ba ai sai kina min, tunda ba ni na hana a koya min ba,
"Ai nima an cuce ni, tunda aka barni ban iya girki ba, haka kawai a dakeka kuma a hanaka kuka, Allah yayi ma inada masoya da yawa, gari da yawa maye baya ci kansa ba, tsaya ki gani, ta fad'a tana d'aukan wayanta, yan danne-danne tayi kana ta k'ara wayan kunnen ta,
Baki hangame Mummy ke kallon Afrah jin yadda take zubawa wani k'alutan mak'atulan shagwa tamkar mijinta......
Sai data gama gaya masa yadda tayi missing d'insa kafin ta gaya masa abunda take so, nan yace mata wani restaurants take so......