'•∞∞BANGAREN MUMMY∞∞•'''
…………Ta rasa inda zata saka ranta taji dadi, ta rame tayi baki, tafi ko yaushe ramewa, tuni damuwa suka samu gurbin zama a cikin Zuciyarta.
Yau ma kaman kullum, zaune take a jikin kujeran dake cikin palonta, ta rafka tagumi da Hannu bibbiyu, abun duniya duk ya taru ya mata yawa.
Yau idan bata manta ba, kimanin shekaru uku ne da yan watanni rabon Afrah da gidan, ba inda bata nemeta ba,
Zuwa yanzu har ta fara saduda, tayi kukan har ta gaji,
Tana cikin tunanin kaman an tsikare ta mik'e tayi hanyar D'akin Abba.
Zaune ta samesa kaman ko da Yaushe ya jinjinu da allon gadon, a yayin da idanun sa su ke a lumshe, jin alamun bud'e K'ofar D'akin ya shi budesu.
Fararen idanunsa ya zuba mata, yana kare wa jikinta kallo, tamkar ba Hajiya Hauwa'u yar kwalisan nan ba.
Tunaninsa ne ya yenke lokacin data zube gwuiwowinta a gaban gadon, ta kama hannun sa cikin zubar da hawaye, ta ce......
"Nasan ni din mai laifin ne Abban Afrah, tun daga haihuwar Afrah zuwa Amrah, bansan da wani ido zaka kalleni ba idan na budi baki nace ka yafe min ba, sai dai bazan iya sanya ba wajen neman yafiyar ka, dan Allah ka jikai na ka yafe min ba don halin ba don Allah da manzonsa, ta k'arasa maganar tana had'a hannayenta a yayin da idanunta suke zubar da hawaye......
Numfashi ya sauk'e, kana ya jinjina mata kai, alamun ba komai,
Murmushi mai yalwa tayi, wanda ya bawa hawayen da suka taru a cikin idonta daman zubowa.
Ganin tayi shuru ne yasa Abba tab'a ta, ya mata alama da me ne ne?
Ai kaman jira take ta sake fashewa da sabon kuka, cikin muryan kuka ta ce
"Abban Afrah, Afrah ita ce damuwa ta, itace Ummul-khaba'isin jefani cikin wannan halin, ban san inda take ba ban kuma San inda zan neme ta ba, yau kimanin shekaru uku kenan, Afrah bata sake taka k'afarta cikin gidannan ba, na rasa yadda zanyi,
"Dan Allah ka nemo min ita,"
Take walwala, da kuma murmushi da yayi a cikin mintuna ya gushe, kaman a mafarki taji ya ce
"Hauwa!
Cikin kidima Mummy ke k'are masa kallo baki bud'e. Ba tare da ta samu lasisin k'ara magana ba, taji ya ce
"Duk abunda ya samu Hafsa (Afrah) ke kika jawo, kuma wallahi Allah zai saka min akan lalacewa da Hafsa tayi.
Ido kawai na xuba miki tun ba yau ba, na ci gaba da magana, haka kawai kika d'auki karan tsana kika d'orawa Khadijah (Simrah) da Aisha (Amrah) ba miki magana ba, sai dai ke kika sani, Afrah kuma kije ki nemeta da kanki, yana gama fad'an haka ya mai da idanunsa ya rufe.
Mummy dai yau taga ikon Allah, don ko dawowa daga jin muryan Abba batayi ba, ta sake shiga wani tashin hankali, ta rasa yadda zatayi da rayuwar ta.
Hakan yasa ta saka Abba a gaba da kuka da magiya,
Wanda shi kuma Abba sai daya silleta tasssss kafin ya ya ce mata shikenan,
Wannan shiryawan Mummy da Abba shi ya rage kaso arba'in cikin d'ari na damuwan ta.
Hakan yasa da dare yayi tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigan baccin cotton mai kyau, tana ta baza kamshi tamkar wacce tayi barin turare.