Don jikinsa har rawa yake, wanda hakan ke nuna tabbas ransa ya kai k’ololuwar baci KO kuma ba k'aramin tabashi abun yake ba......
Kuka yake sosai, don har tanajin saukan hawayensa a tsakiyar bayanta.
Dukkansu rungume juna sukayi su uku, sukayi ta kuka tamkar wad'anda aka saukar wa da sakon mutuwan iyayensu.
"Innanillahi yau naga abunda yafi tsare tsayi. wannan wace irin rayuwa ce??
"Atoh nikam wallahi jam d'ina, haka siddam za'a zajamin fitina, a roka min bone, saboda jin dad'in duniya zaku had'e kai kuyita kuka???
To kukan na mene?? na jin dadi ne? Ko dai na haka kawai?
Cewar Mummy wacce ta shigo D'akin da niyyar kiran SIMRAH, cikin maganan sama taci gaba da cewa
"Allah wadaran naka ya lalace wallahi, Yusuf wace irin rayuwa ce haka?
'Kawai Saboda koyawa Yara iyayi da tsugudidi, ka wani had'a Yara ka sakasu a gaba kana kuka kaman wani k'aramin Yaro?
"Wallahi na gaji da halin ka, halinka ya fara isana.!
"Wannan wani irin rashin dangana ne? abun tun 14 amma har yau kana zaman kukansa?
"Ni nawa iyayen basu mutu bane? ko iyaye sunfi iyaye ne?
"Ina dalilin bawa ya d'auki rayuwar kunci ya d'ora wa kansa saboda rashin wadatan imani, ai wannan son shiga hurumin Allah ne.
"Kafi Allah sonsu ne? da zaka zauna ka had'a kan yara kana kuka?
"Ni wallahi banason wannan abun, na fara gajiya atoh.
"ku kuma ku tashi ku bar D'akin nan, kafin naci Ubanku! Yan iskan Yara kawai! ta ida maganar tana dakawa su SIMRAH tsawa,Wad'anda suka bar jikin Abbansu tun sanda Mummy ta fara magana, a yayin da SIMRAH da Amrah suka rungume juna, suna masu ci gaba da kuka, don ba k'aramin tsoro fad'an mummy ya haifar musu ba.
Kallon SIMRAH Mummy ta sukeyi a karo na biyu, cikin tafasan Zuciya tace " ke kuma, ba abunyi kike nema ba? tunda abunyi kike nema bari na baki, don dama da aiki nazo.
"Abincin da kika dafa yau bai yiwa Yarinyata ba, don haka cikin 30-40minutes zaki shiga kitchen ki dafa mata abinci.
Kuma wallahi kima dafa wanda bai mata ba, na rantse da Allah zakici Ubanki da mai da yaji.
" Kin daiji na gaya miki, don bazaki kashe mun Yarinya da yunwa ba.
Ba tare da tace komai ba ta kama hannun Amrah suna fita daga D'akin, tana juyawa don kallon Abba, dake zaune har wannan lokacin, haka kuma idanunsa basu daina zubar da hawaye ba.
Kitchen ta nufa, haka kuma daga kitchen d'in tanajin yadda Mummy take surfawa Abba masifa kaman d'an cikinta.
*Wace ce SIMRAH???*
Cikekken sunanta shine Maryam Yusuf Sale, Haifaffun yan jihar Gombe ne,
Yusuf Sale haifeffen d'an jihar Gombe ne, wanda aka haifeshi a anguwar fantamu.......
Yusuf su uku Iyayensa suka haifa, maza biyu mace d'aya, wacce ta rasu a garin haihuwar yarta ta fari, hakan yasa yasa rikonta ya dawo hannun Innayi, sai kaninsu da baiyi Aure ba , inda suke zaune acikin Family house d'insu, da yan Uwan Babansa, suma da matansu da Yayansu.
Gidansu Family house ne babba, wanda a yake d'auke da Part k'waya goma sha hud'u.
Yusuf ya taso da tarbiya gaba da baya, haka kuma ya samu wadataccen ilimin addini dana zamani daidan gwar-gwardon iko.
Yusuf mutum ne mai sanyin hali, wanda bashi da hayaniya ko kad'an.
A lokacin da Yusuf ya isa Aure, har ya samu aiki a jihar Bauchi, indai ya Auri wata tsohuwar budurwasa, mai suna Hauwa.
Hauwa wata masifafiyar Yarinya ce, wacce Allah ya d'iga mata ruwan masifa tamkar dangin Fir'auna. bata da hak'uri ko kad'an. Sai d'an karan masifa da dambe kaman yar kaji........
*Wace ce Hauwa'u*
'Ya ce wajen Malam Dauda da Hansai, Malam Dauda da Hansai, mutane ne da Allah ya halitta ya ajiye, basu da kunya basu da kirki, ballen tana wani abun wai shi mutunci.
Hakan yasa 'Yayansu tasowa tamkar dabbonin da basu da mai su.
Hauwa'u itace babba, sannan kaninta Yusha'u, dukkansu tijararrarun 'Ya'ya ne da suka addabi kowa a anguwar Pantami.
Malam Dauda ba mai kudi bane, amma sangancir da yayiwa 'Ya'yansa ko attajirin mai kud'i albarka.
Hakan ya bawa 'ya'yansa daman da suke tsulawa jama'a tsiya yadda suke so, kuma mutum bai isa ya tanka ba.
Don yanzu zakayi magana iyayen su had'u su maka rashin mutunci. Za'a iya cewa su Hauwa'u gadon halayensu sukayi a wajen iyayensu.
***
Lokacin da Yusuf ya nunawa iyayensa wacce yake so, basu bada goyon baya ba, especially Mahaifiyarsa Innayi, don tafi kowa d'aukan d'umi.......
Sai dai masu iya magana sukace wai rabo dangin ajali, haka kuma matar mutum kabarinsa.
Hakan ne ya kasance a wajen Yusuf.
Batare da b'ata lokaci ba, akayi Auren, inda suka tattara suka koma Bauchi sa bo da sabida kasuwancin sa dake can........'''