17

9 0 0
                                    

..."Wallahi na gaji da abunda kikeyi akan wannan Yarinya, ki sani ina kyaleki, ina kuma hak'uri akan halayenki, amma wallahi karki kuskura ki k'ure hak'urina, don abun bazai miki kyau ba!

"Ya jima bai min kyawun ba Yusuf, wallahi kayi kad'an ka sani abunda banyi niyya ba, baka isa ka sakani dole akan abunda banyi niyyan yinsa ba, ai sonta  ba dole ba ne, Zuciyata ce, kuma a cikin  kirjina  take, kaga sai wanda na gadama zatan sakata ta so kenan.....

"Duka wannan ma na mene ne,? ai dama ka riga da  ka sani a  tarihin rayuwata bana son bak’ar Yarin ya, ita kuma daga kallon skin d'inta a yanzu na gane wallahi kai ta d'auko kuma baki zatayi, don haka sai ta nemi *WATA UWAR* amma wallahi badai Hauwa ba.....

"Don haka kayiwa kanka, sannan kuma kayi mata, tunda ita dai shegiya ce bata san halacci ba, ai dole nace bata san halacci ba, to ta sanshi ne?

"Idan tasan halacci zata zauna a cikina ne bata d'aukoni ba, ai wannan iskanci ne, irin na mutanen farko....

     "Tunda dai ta zauna acikina kuma bata daukeni ba, to wallahi na yafewa kai ita, dama duk wacce zan haifa ta zama haka,

"Wannan hukunci ne, dana tanadarwa duk shegiyar Yarin yar data kuskura ta d'auki Ubanta bata daukeni ba.......



     Ta ida maganar tana dallawa Abba harara, wanda zuwa wannan lokacin komai nashi ya daina aiki sa bo da zallan mamakin wad'annan maganganun Mummy takeyi tamkar wata jahila, wacce bata san me ilimi ba....


Kallon ta Abba yayi kana ya ce
" Innanillahi wa innanillahirraji'un, Hauwa'u abun nakin har ya kai wannan matakin,?


"Ai yama wuce nan Yusuf, cewar Mummy wacce ta tari numfashin Abba....


Numfashi Abba ya sauk'e kana ya nemi waje ya zauna a bakin gadon, haka kuma har zuwa wannan lokacin Yarinyar na jikinsa, wacce zuwa wannan lokacin tuni tayi bacci, a yayin da take sauk'e ajiyar Zuciya na kukan da tasha....


Dama ance ita mace idan ta birkice to wallahi tafi gaban bala'i n namiji ya sakata saukowa, sai dai dole ya saukar da  kansa.

Hakan ne ya kasance a wajen Abba da Mummy, daga karshe shi ya saukar da  zafin ransa ya hau rarrashi Mummy, SA kyar ta samu ta sauk'o.


Basu tashi a wajen ba, sai da sukayi yarjejeniyar no-no ne kad'ai zai had'ata da Baby'n, bayan wannan babu abunda zata sake mata.kaman yadda Mummy ta ce, hakan ne ya kasance, don babu abunda yake shiga tsakanin su, idan ba shayarwa ba.

Ko kwana da Abba take yi, a yayin da ita kuma take kwana tana mak'ale da Afrah, tamkar zata maidata cikinta.

Bayan Abba yayi koma wajen aiki, ya nemawa SIMRAH mai kula da da ita.

Abunda yake faruwa ba k'aramin ciwo yayi wa Abba ba, sai dai ba k'aramin dannewa yakeyi ba, sa bo da  gudun abunda zai zo ya dawo, sa bo da  har yanzu bai manta  maganganun da akayi tayi akan  aurensu ba.

Sa bo da hakane yasa yake  danne wassu abubuwan, ba tare da ya nuna abun yana damunsa ba, sai dai na ciki na ciki, don masu iya magana sunce wai abun cikin ciki sai hanji, don haka ya adana komai a ransa.


Cikar SIMRAH shekara d'aya yayi dai-dai da faruwar  wata mummunan kaddara,Ba hawa ba sauka sai dai sakon mutuwan da aka aikawa Abba na rasuwar iyayensa sakamakon gobaran daya tashi a side d'insu,

Ba bata lokaci suka shirya sukayi gombe, tun daga mashigar anguwar yasan lallai babu lafiya, duba da cikan da mutane sukayi, ga kuma hayakin dake fitowa daga cikin Gidan, Wanda ke nuna cewa ba'a jima da kashe gobaran ba.


Nan ya  isa K'ofar gidan da kyar ya iya daga k'afarsa zuwa cikin Gidan,

Gabansa yaji ya fad'i, haka kuma a lokacin yaji Zuciyarsa ta tsinke a time d'in da yayi arba da gawawwaki guda biyar a jere akan taburma, an rufesu da fararen kyallaye.

Wani mutum dake gefensa, wanda ya kasance d'an Bappansa, ya tsinkayi muryansa  yana cewa.

"A nan gawan Inna ne dana Baba, sai kuma fa'e (wacce take gaban Inna, yar kanwarta) sai na Abdul-Majeed, (kaninsa) daya zo hutu, shi da yayansa guda uku, sannan Maryam (yar addarsa data rasu) ba'a iya ko ganesu don duk jikinsu ya kone ya soye yayi baki, kum....

Iya abunda Allah ya bashi ikon ji kenan, tun daga nan bai sake sanin inda kansa yake ba, sai bayan kwana uku daya farka ya ganshi a asibitin,

Kuma tun daga wannan ranar bakinsa bai sake bud'ewa da sunan magana ba.

Haka kuma bai sake dariya ba, tun daga ranar rayuwar kunci ya auresa, tun daga wannan ranar kuka, tunani,Wani mutum dake gefensa, wanda ya kasance d'an Bappansa, ya tsinkayi muryansa  yana cewa.

"A nan gawan Inna ne dana Baba, sai kuma fa'e (wacce take gaban Inna, yar kanwarta) ba'a iya ko ganesu don duk jikinsu ya kone ya soye yayi baki, kum....

Iya abunda Allah ya bashi ikon ji kenan, tun daga nan bai sake sanin inda kansa yake ba, sai bayan kwana uku daya farka ya ganshi a asibitin,

Kuma tun daga wannan ranar bakinsa bai sake bud'ewa da sunan magana ba.

Haka kuma bai sake dariya ba, tun daga ranar rayuwar kunci ya auresa, tun daga wannan ranar kuka, tunani, damuwa, da kuma bakin ciki suka zama abokan rayuwarsa.

Hakan ne ya bawa Mummy daman gaya masa bak'ak'en maganganu akan bashi da wadataccen imani, a cewarta da shi mai  mai imani ne ai da tuni yayi hak'uri ya fawwalawa Allah komai.

Haka suka karkato  suka dawo Bauchi bayan anyi sadakan  arba'in.

Haka kuma rayuwar gidan yaci gaba da tafiya, sai dai tunda Abba bai taka wajen aiki ba, hakan yayi mugun k'ular da ita, a cewarta ai iskanci ne zaisa yana kulle kansa a D'aki, ganin ba sarki  sai Allah yasa taje wajen ogansu, wanda dama idon sani ne, a nan sukayi magana ta maye gurbin Abba a wajen aiki, bayan yan cike-ciken da akayi.Daga haka ragomar gidan ya dawo hannun Mummy, ita take komai na gidan, don Abba ko magana bai sakeyi ba, tunda yayi arba da  gawawwakin iyayensa ya yanki jiki ya fad'i shikenan.


Mummy tayi fad'a tayi mita, sannan ta yi masifa,  har ta gaji, don Abba ba jin maganganun ta yake ba, domin idan ana mishi magana baya daga ko kai ya kalli mutum, infact baya ma nuna wa yasan da zaman mutum a wajen.


Tunda Mummy ta fara wannan aiki ta kuma  rik'e wannan gidan shikenan ta samu hanyar wulatanta Abba da SIMRAH,  abu kad'an zata haushi ta masifa da fad'a kaman danta, kai hatta Afrah da take 'Yarta bata surfa mata masifan da take yiwa Abba.



SIMRAH tana da shekara d'ayan nan, Mummy ta tugeta daga shan no-no, duk da kuwa ba wanj girman jikin azo a gani take dashi ba, haka ta yayeta tare da cewa iya rabonta kenan.

Haka zata kwana tana kuka ta wuni tana kuka, duk da kuwa dama Mummy bata bi ta kanta, ko da kuwa tana kuka, ballen tana a yanzu. Don tunda Mummy ta yaye SIMRAH bata sake shiga harkanta ba, haka kuma bata sake dagata ba ko da kuwa lafiya ne bata dashi, idan bata da lafiya sai dai ta ce wai mai aikinta  ta dauketa ta kaita asbiti, kar ta mace mata a gida hukuma ta kamata.

A yayin da Afrah kuma ko yaushe tana gan-ganta, don basa rabuwa ko nan da can, ko office d'inma da kyar take rabuwa da ita, gani take kaman idan ta tafi ta barta akwai abunda zai sameta.

Don idan ta barta a gida taje office, kullum idan ta dawo sai ta bincika jikin Afrah, ta duba ko ina.


Abba bai tab'a nunawa Mummy yana jin haushin abunda takeyi ba, ko data yaye SIMRAH bai nuna  mata ba. Don baya shiga sabgar kowa a gidan, SIMRAH kad'ai yake d'agawa, idan tana kuka.

Hakan yasan SIMRAH ta tashi  bata da  sama da Abba,  don ita bata saka Mummy a lissafin masu sonta ko wad'anda suka damu da damuwarta.....✍️




*Fans ya kamata ku gayawa Mummy gaskiya.....!*

WATA UWARWhere stories live. Discover now