37

7 0 0
                                    

……Su Daddy na gama adduo'in da zasu masa, aka zo yan Uwa da abokan arziki suka had'u suka mik'a Ahmad gidansa na gaskiya, sai fatan Allah jikanshi da Rahma, Allah kuma ya gafarta masa yasa ta huta.....


Su Mamy sun cika wa Sadiq wassiyarsa na cewar kar a ayi masa zaman makoki, haka kuwa akayi ba'ayi ba, daga cikin gidan har wajen.......


           ....*Bayan wani lokaci.....*

Sannu a hankali sai mutuwar ta fara bin jikinsu tana sakesu, har suka warware tamkar ko ina.....



Mamyyy danne damuwa kawai take, amma cike yake fallll a cikin ranta, dondon dai ba yadda ta iya ne.......


Sai dai kuka kam, bata sake masa ba, ko da kuwa na wasa ne......



Daddy shima a dá yayi kuka, sai daga baya ya daina daya tuna da maganansa wanda yayi na farko, da kuma maganan da wassu yara abokansa suka fad'a masa na tunin da yake musu akan alk'awarin da suka d'auka masa......



Haka ma Sadiq, yaji mutuwar Ahmad sosai, kasan cewar bashi da abokin daya wuce ci, shi ne abokin SA shine d'an uwansa, saboda zallan shakuwan da suka yi, kasan cewar junansu kad'ai su ke gani a cikin Gidan.….


Hakan yasa yana son yayi kuka ko zai rage rad'adi daci da kuma kewan daya addabi Zuciyarsa.….

Sai dai idan ya tuna alk'awarin daya d'auka masa, sai yaji komai ya fita kansa......



Haka kuma wannan lokacin tuni su Babandi sun zo kaman yadda Ahmad ya bukata, haka akayi suna zuwa akai-akai bayan tuban da sukayi, da kuma sunan yen da suka canja, don har Sana'a Daddy ya nema musu tunda dukkansu ba wanda yayi karatu, Yawancinsu yan no reading no writing ne.

Hakan yasa sau tari  idan Mamyy ta kalli su Muhammad (Babandi...) Sai ta tuna da  maganan Ahmad da yake ce mata ai zata iya samun wassu yaran ko da kuwa ba ita ta haifesu ba.


Hakan yasa ta godewa Allah, tare da addu'a wa Ahmad.



Haka  rayuwar gidan yayi ta tafiya ba wata matsala sai dai mu ce Alhamdullh, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talik'ai, mai Rahma mai jin k'ai, tsira da aminci suka k'ara tabbata ga fiyeyyen halitta, annabinmu Muhammadu, Sallallahu alaihi wa sallam......



*Bayan wata biyar*


'''Gidan Honourable Garba Abdullahi D'an_Buram '''
         ±

    
         "Zainab daga ina kike tun daxu mu ke ta nemanki? Cewar wata bak'ar mata mai tsananin kama da wannan yarinyar.....


Mui-mui-mui haka bakin ta yake tayi ba tare da ta amsa magana to d'aya.....

Nikam ya Zanyi ne da rayuwata? Ya kuke son nayi ne don Allah, ta fad'a cikin zallan damuwa a yayin da idanunta ke zubar da hawaye......

Kafin Uwar ta sake magana, kaman walk'iya sai ga wani saurayi ya shigo gidan kaman an jeho shi, cikin daga murya yake fad'in.....

"Ke Zeee ina kike don Ubanki? Uban me kikaje yi a sabon layi da aka ce min an ganki?

"Ubanka man,"

Gauuuuuu taji saukan mari har biyu akan kuncin ta, ba ta daddara ba taja masa tsaki......

Hakan yasa ransa ya k'ara b'aci, ya fara dukanta yana ball da Ita yana kai Mata duka ta ko ina, duk da kuma irin magana da fad'an da Mama keyi, amma baiji ba.....


Cikin tsautsayi ya kai mata duka a ciki, daya saka tayi wani irin k'ara na azaba, aiko kaman giftawar ido jini ya balle mata ya fara zuba.....



WATA UWARWhere stories live. Discover now