………Cikin sauri Ammy ta k'walawa driver da Mai gadi kira su ka zo suka ciccibeshi aka sakashi acikin mota, kana akayi Asibiti dashi.....
Ammy in banda kuka babu abunda takeyi, ji take tamkar zata rasa shi kaman yadda ta rasa yan uwansa a sanadiyyar gobara, hawaye ta share a lokacin data ga sun isa asibitin su.
Ba tare da b'ata lokaci ba, akayi cikin Asibitin dashi, a bisa taimakon Dr. Aliyu Haidar akayi bangaren masu ciwonsa dashi.
Ammy tayi mamaki ainun jin wai yana da folder, a ranta take raya to yaushe ya samu ciwon Zuciyan da har ya kawo kansa Asibiti.
Akan wata kujeran dake facin D'akin da suka shiga Dr.Aliyu_Haidar ya zaunar da Ammy, bayan kwantar mata da hankali, kana shima ya bi bayansu, yana mai tausayawa abokin nasan.
*A chan cikin D'akin kuwa.*
Sun shafe da a kalla mintu arba'in (40) kafin su samu numfashin sa ya dawo dai-dai,Dukkansu hamdala sukayi a tare ganin numfashin ya dawo, sai kuma suka fara kokarin dai dai ta bugun Zuciyarsa ya dawo normal beat, kana suka masa abunda ya dace, daga haka sukayi mata alluran bacci....
.Ammy banda addu'an Allah ya tashi kafadunsa babu abunda take fad'a, sai kwallan da take sharewa lokaci zuwa lokaci.......
'''Bangaren Mummy'''
Zamansu ba laifi yanzu kam akan na da, sai dai har yanzu kullum Mummy sai tayi masa kuka akan rashin Afrah.
Abba kuwa dama horata yakeyi, hakan yasa daga baya ya ce shi kenan, kana ya saka wad'anda zasu nema masa.
Sai dai duk cikin gombe babu inda basu nemeta ba amma shuru, da suka gayawa Abba sai yace karsu damu sannan karsu gaji suci gaba da nema ko da na sati biyu ne wata kila a ganta, hakan yasa kullum sai sun nemi Afrah, sai dai shuru......
*Bagaren Sadiq*
Shima yanzu neman Afrah yake ido rufe, tare da taimakon su Babandi, haka kuma ko Mamy bata san me yake aikatawa ba.......
Dama kuma baya son ta sani, don yasan tsaffff Mamy zata hanashi, shi kuma baya jin zai iya yafe mata akan cin Amanan da tayi masa. Tana sa ne yana sonta ita kuma bata sonshi, amma baza iya gaya masa cewar yy hak'uri ba, sai kawai taci gaba da lobashi ta maidashi d'an iskan da bai san me yakeyi ba, daga karshe sai ta buge da gaya masa munanan maganganu, har da saka Mahaifinsa daya kwana kad'an a chan, to wallahi mai hanashi ya koya mata hankali sai dai Allah'n daya halicceshi.....
_A bangaren Simran._
Jiki Alhamdullh, ya warware sai dai kwata-kwata ya daina magana, don a rana baya fin sau d'aya yakeyi, shima sai ya zama dole, a da Ammy ta damu damu sai dai bayanin da Dr. Aliyu ya mata sai taji sanyi, kana itama ta masa nata, daga haka suka ci gaba da kallon SA tare da masa addu'an Allah ya bashi lafiya ya kuma bashi dangana don Simra kam an riga da an d'aura mata Aure.
Bayan kwanata uku aka salla meshi kana ya koma gida,
Da daddare kuwa Ammy ta kirashi ya zo palon, bayan ya zauna ne idanunsa suka sauk'a akan akwatunan, runtse idanun nasan yayi kana yy tamkar bai gani ba.
Kallon SA tayi kana ta ce.
"To ga kayan Aurenka an had'a, million goma da Rabin dana karb'a gasu a nan, sai motan 6.million dana siya 4.½ kenan, shi kuma na sayi gold babba na million 3.½, kana sai na saka K'udina akan sayi wadannan kayan, 40boxes.
30 nata sai na dangi, biyar dangin Uwa biyar na Uba, kuma gobe in sha Allah za'a kai su gidansu fatan ka gane.