.........Bayan rasuwarsu d'an kwanaki kad'an, shagon Abba dake kasuwaa wanda ya hada hannu da kanin sa, ya kama da wuta, Wanda ba'a San daga ina ya fito ba, haka kuma ba'a fitar da komai ba, saboda da daddare gobaran ya tashi, hakan ya k'ara durgusar da Abba, ya zama ba "um ba um-um"....…
Haka rayuwarta yayi ta tafiya a gidan, ta zama tamkar wata bare, tamkar'Yar tsintuwa ce, bata da gata, bata da galihu, duka, zagi, hantara, kullum cikin kuka take, Mummy tamkar jira take tayi laifi, zata hau kanta tayi mata dukan sa'a.......
Ban-bancin da Mummy ke nunawa akan Afrah da SIMRAH yayi yawa, ko wa Yayan KISHIYA ba'a son wannan halin ballen tana cikinsu d'aya, hakan zai iya sawa su tashi basa jin son junansu, ko kuma d'aya zai rink'a yin wani tunani na daban.
_( *NOTE:* dan Allah iyaye ayi hakuri ana sirranta irin son da akewa d'aya daga cikin Yaya, saboda gudun faruwar wani abu.....)_
...Haka yafinyar k'arama ta tashi cikin bak'in ciki tsangwama da kyara. Idan bata wajen mutum uku ba bata samun sauk'i, Abba, Maman Twins sai kuma mai aikinta Larai......
A yayin da Afrah ta tashi a sangarce, ga rashin kunya ga futsara, tun bata iya magana sosai ba. Kuma hakan bai tab'a damun Uwarta ba, ko tayi abu Mummy bata kwabanta, sai ma ganim kaman dai-dai takeyi....
Tana cika shekara uku Mummy ta kaita wani private school mai tsadan gaske, a yayin da islamiyyah kuma ya zama ko oho, don ita a batayi niyyan saka Afrah islamiyyah ba.
Tafi mayar mata hankali a b’angaren boko, wanda bazai anfani lahirarta ba, komai ma Mummy tafi saka Afrah, ko wani buri tafi dorashi akan Afrah.
SIMRAH na cika shekara uku itama aka sakata school, amma bana Afrah, a cewarta kar aga taki kaita idon jama'a ya dawo kanta.
Shigan skull d'in da SIMRAH tayi ba k'aramin sauk'i ya sama mata daga zaman gidan ba, don ita kam gaba ta kaita wai gobaran titi a JOS, babu duka ba zagi, musamman da skull d'in ya kasance mai d'auke da islamiyya, hakan yasan suke wuni a islamiyyah bata dawowa sai yamma...
SIMRAH tana gane karatu sosai, duk da k'arancin shekarunta, sannan Uwa Uba ga hankali da nutsuwa tun yar k'ank'anuwarta, hakan yasa tayi farin Jini a wajen teacher's d'insu....
A yayin da Afrah kuma ta zama rasa kunya B’eran danga, don rashin kunya takeyiwa teacher's d'in, kuma basu da bakin magana ko hannun duka, don private school ne, wanda ba'a dukan yara, a takaice ma school dinsu, students sunfi teacher's mahimmanci, sa bo da son K'udin da principal d'insu yake dashi.....
***
*Bayan Shekara Bakwai*A shekaru bakwai d'in nan, abubuwa da dama sun faru,
Ciki har da Karin girman da Mummy ta samu, tuni ta canja musu gida, haka ma ta canjawa Afrah skull, amma banda SIMRAH.....
A wannan shekaru bakwai d'in kuwa, Allah yayiwa iyayen Mummy rasuwa, Mahaifinta shine ya fara rasuwa, bayan rasuwar Mahaifinta, da shekara uku, Allah ya karb'i na Mahaifiyarta, shi ke nan Mummy itama ta zama marainiyar gaba da baya, sai kaninta daya gagari kowa, karshe ma kayansa ya had'a, wai ya tafi yawon ganin duniya.....
Haka Mummy taci gaba da zuba mulkinta a cikin Gidan, a yayin da Abba yake ba um ba um-um, hakan kuma bai hana Mummy ta takashi yadda takeso ba.
Haka kuma a shekaru bakwai d'innan, har yanzu Abba bai ci gaba da magana da dariya kaman kowa ba.
Haka kuma Mummy bata daina masa gorin ya kasa tawakkali akan hukuncin Allah ba....
Tunda suka dawo wannan gidan, aikin komai na gidan dawo hannun SIMRAH, ita take komai na gidan, duk da kuwa ba wassu shekaru gareta ba. Don tuni Mummy tayi wa Larai (mai aikinta tun tana k'arama) checking out, a cewarta yanzu kam, ga mai mata komai na gida....
SIMRAH tayi kyau, ya zama yan mata duk da kuwa 10yrs take dashi, sai dai za'a iya cewa ta kai 14 sa bo da jikin da take dashi.
Tuni ta zama black beauty, son kowa k'in wanda ya rasa, don SIMRAH ba k'aramin Allah ya mata ba, sai dai Mummy bata gani, haka kuma kamanninta da Abba tuni ya k'ara fitowa, ta zama tamkar yayi kaki ya tufar.
Haka kuma Afraa ta girma, tayi kama da Uwarta tamkar yadda Uwarta taso, haka kuma ta samu farinta dai-dai gwargwado, amma Mummy bata gani ba.
Don Mummy ta raina hasken Allah ya bawa Afrah, hakan yasa tun tana yar shekara biyar Mummy ta fara mata bleaching, zuwa wannan lokacin tuni Afrah ta zama balarabiyar Kenya, tayi wani irin shegen hasken da tun daga nesa zaki ganta tayi bau tamkar Zabiyan,
sai dai tuni ta zama mara kunya fitsarerriya, bata kunyar kowa bata shakkan koway, haka kuma bata shayin kowa, ko da kuwa Mummy ce.
SIMRAH tana da shekara goma, Allah sake bawa Mummy wani ciki, wanda ta d'auki son duniya ta d'ora masa kaman zata fito dashi tun watanninsa basu kaiba.
Son cikin Allah ya d'ora mata tamkar jarrabawa, magana daya biyu idan na haihu, kullum K'udinta a yiwa abun ciki siyayya yake k'arewa, a yayin da cikin yake mugun wahalar da ita, kaman zata mutu.
Ko aiki da kyar take zuwa, tuni aka gamawa ciki siyayya, komai Mummy sai daya siyeshi, kaman kayan hauka.
SIMRAH ma ba k'aramin farin ciki taji ba, da taji Mummy na d'auke da ciki, dad'i takeji don a cewarta ko ba komai zata samu 'Yar Uwar da zata nayin tadi da ita.
A yayin da Afrah bata ta cikin, don ita babu abunda ya shafeta da wannan abun, domin ita mutum ce bata damu da damuwar wani ba, tana kyaliya, hakan yasan Mummy bata sakata a wannan fannin, sanin ko tayi ma gwaleta zatayi.
Haka Mummy ta ci gaba da rainon cikinta, bisa taimakon kanta dana Maman Twins, wacce ke zuwa lokacin zuwa lokaci, sai kuma SIMRAH da bata dauk'ansa a komai, hakan yasan take samun kulawa sosai.
Tuni Mummy ta riga da ta gama siyayya, tun cikin yana watanni biyar ta sayi komai na Baby_girl hatta labour kid ta had'a ta ajiye tana jiran zuwan labour, sai dai Allah ya sauketa lafiya.
Haka rayuwar gidansu yaci gaba da tafiya yana gurgurawa, masu iya magana suka ce wai yau da dad'i gobe ba dad'i.
To, su dai nasu gidan ba haka ba ne, akasin haka ne. Domin kuwa yau d'inma ba dad'i ballen tana gobe, kullum gidansu cikin rashin dad'i ake.
Cikin Mummy na shiga wata Tara ciff, ranar wata juma'a ta tashi da labour, 2:00 suka tafi Asibiti, da taimakon Anty Safiya (Makobciyarmu) suka tafi Asibiti.
Hankalin SIMRAH a tashe yake, har kuka sai da tayi, don bata taba ganin mai nak'uda ba,
Mummy Tasha bak'ar wahala kafin ta samu Allah ya sauketa lafiya, nan ma sai da aka mata CS, inda ta samu 'Ya mace mai tsananin kama da SIMRAH kaman am raba kunu.
(Akwai k’ura kenan...!)Bayan kwana uku, da daddare bayan isha suka suka dawo, Anty Safiya na rik'e jinjirar, Mummy kuwa kallo d'aya mutum zai mata ya fahimci bayan wahala akwai damuwa ko nace bakin cikin da take ciki, don ko magana batayi, daga SIMRAH har Afrah, wacce yau bata ma wuni a gida ba, domin ko school yau Afrah bata je ba, haka kuma bata zauna a gidan ba....
Sannin Mummy bata da lafiya ya sata kin tafiya school, sannan kuma bata zauna da itan ba.
SIMRAH da Anty Safiya ne a kitchen suna fafutukan dora musu ruwan zafi don a samu mai jego da jinjiran suyi wanka.
A yayin da abinci kuma Maman Twins da sukayi waya da ita take shaidawa su Anty Safiya zata taho da abinci, don haka sukayi haramar d'ora ruwan zafi.........✍️
Sorry da jina shuru banajin dad'i ne.....
*#Comments*
*#share fisabilillah.**DAID’O GOD’D’O*