'''_____Sai dai yayi Alk'alawarin bazai tab'a magana ba, muddin ba ita Mummy'n bace ta zo da niyyan neman taimakonsa a matsayinsa na Uba ba, muddin bata zo ba, wallahi sai suyi tayi, amma indai Uwa da Uba ne suka haifeshi, wallahi ko inda suke bazai sake kalla ba da sunan son gyarawa Afrah akan rayuwar da yaga ta za6awa kanta, domin duk abunda Afrah tayi to da taimakon Mummy tayi shi, don haka dole ya horar dasu, wannan karon dole zai nuna wa Mummy, maza su ne tsayayyu akan mata, kaman yanda Allah S.W.T ta fad'a acikin suratul-Nisa'i, sai ya nuna wa Mummy tasan Annabi ya kafu, zai nuna mata ba'a maraya sai rago…
Da wannan tunanin ya koma D'aki yana mai jin nauyin da Zuciyarsa ta masa yana k'aruwa,
Cikin D'akin ya koma, kana ya samu bakin Gado ya zauna,cikin sanyi murya ya ce
"Ya Allah ina ta wassuli da karatun nan, ya ubangiji ka bani ikon cinye jarrabobin da ka jarrabeni dasu, ubangiji ka saka min dangana, ya Allah bazan Iyaba ubangiji ka tallafeni, da karfina, astagfirullah Allah na tuba, Allah na tuba, ya kai ayar maganar yana fashewa da kuka
(Simra's team, azo ayi shagali Abba ya fara magana💃💃)
★★
" a'a yarinyar kirki me ha faru naga kun dawo??? Cewar Ammy wacce saukowa daga kan stairs,,,,,
Ammy munje kuma am riga da an shiga, sannan kuma shi kad'ai nake dashi, shi ne kawai na dawo, amma ya ce wai na zo zai koya min abunda akayi da daddare ta kai ayar maganar tana zama.
"Ok to ba damuwa," ranta kuwa sai cewa tayi
("Basai ka k'arawa kanka aiki ba, daga yau kuwa zanyi maganinka, kullum sai ka koya mata.){Chassssss da Ammyn mu🤸♀️💃}
***
Da daddare
"Adda, Ammy nd'on noddu ma"
," (Adda Ammy ta na kiranki) cewar Amrah"Toh, nmidom wara," ( toh ina zuwa)
Mikewa tayi ya fita, bayan fitan Amrah itama sai tabi bayan ta a yayin da take rike da handout a kehannun ta.....
"Ammy gani,"
"Kin manta xakuyi karatu ne? Wuce kije kuyi, har dare ya fara abunda ya kamata ku fara tun tuni...."To Ammy bari na d'auki hijab, "zaki wuce ne ko zan sa6a miki wuce,.
Kallo ta k'arewa jikinta, bu-bu ne a jikinta na kanti cotton mai kauri kalan blue mai ratsin read, sai kuma red d'in simple hat dake kanta wanda ta nade bakin gashin ta aciki, hakan yasa za'a ga tamkar tayi acuci dashi.......
"Ammy to Amrah ta rakani,
" a'a bazata je ba, bacci zatayi ai kinsan tana da skull gobeko???
"Ayye Ammy dai bansan wajen ba,,,,,, shuru Ammy tayi, kana ta kwatanta mata side dinshi don haka ta kama hanya cikin mutuwar jiki tamkar wacce batada lakka a jikinta......
Sallama tayi cikin siririyar muryanta, mai dad'in sauti kaman ana busa sarewa, wacce ya jita har tsakiyar kansa...
Hakan ko yasa ya amsa a kan le66ensa, yana mai k'arasa shirin da baiyi ba na bacci....
Zama tayi akan kujera, bai fito ba har sai da taji bacci ya fara fusgantaa, kafin ya fito, yana ta baza K'hamshi cikin kayan bacci wando da riga kalan red wad'anda suka dashe da farar fatarsa ta asalin Fulani....
Mikewa tayi, tana cewa "ina wuni..... Bata ji ya amsa ba duk da tana da tabbacin yaji gaisuwarta ta,.....
Handout d'in hannunta ya karb'a ya fara dubawa, nan ko ya fara mata bayanin abunda ke cikin handout d'in, kafin ya dora mata dana yau wanda ya tambayeta,
Karatun ya d'auke su lokaci mai tsayin gaske har kusan 12, duk da Alhamdullh duk abunda ya fad'a mata kanta yana catching, tamkar magnet haka kwanyar kanta take da karatu......
"Je ki kwanta," ya fad'a a hankali tamkar bashi yy maganan ba, mikewa tayi bakin ta d'auke da guntuwar hamma, wacce ta toshe bakin da bayan hannunta na hagu kaman yadda MANZON ALLAH S.A.W yy koyi da hakan, sbd daman dake rike da handout d'in.....
"Kafin ki kwanta ki kawo min coffee, duk kinsa wuyana yana zafi²,
Kallonsa tayi ganin ba ita yake kallo ba, yasa ta marairaice, kana tace " Thank-you,"
Ba tare da ya kalleta ba, ya jinjina mata kai, a yayin da ita kuma ta kasa daga ko da kafanta ne daga cikin palon.........
D'agowa yy ganin tana tsaye yasa, ya kalleta tamkar yadda ta kalleshi, ya ido ya mata me ne ne....
Shagwa6e Fuska tayi, kana da kanta ta nuna masa K'ofa, sannan ta kad'a kanta, gane me take nufi ne yasa ya mik'e ba tare da yace komai ba ya kama hanyar fita waje, ba shiri ita ma ta bishi,,,,,,,
Yana gaba tana biye dashi a bawa har cikin palon Ammy, tamkar zaiyi waje sai kuma ya fasa ya shiga ciki.....
Kallonsa tayi ganin ya nemi waje akan []aya daga cikin kujerun dake cikin palon ya zauna...... Hakan yasa tayi hanyar kitchen d'in....
¹⁴Minute ne ya d'auketa had'a coffe d'in, nan ta fito hannunta RI[]e da k'aramin teray mai dauke da k'aramin flask, sai mug, teaspoon, Honey an sugar.....
Ba tare da yace komai ba ya karb'a, a wajen ya had'a, kana ya kama hanyar sa yy waje abunshi ba tare da ya ce uffan ba....
Bayansa tabi ta kulle K'ofar, kan ta dawo, cikin palon ta kashe wutan daga haka tayi D'akin Ammy, sbd wutan data gani a kunne......
Da sallama a bakinta ta shiga D'akin, nan ta hango Ammy zaune akan sallaya, da carbi a hannunta tana lazimi……
A gefenta ta zauna, kana ta d'ora kanta akan kafad'an Ammy sannan cikin shagwaba ta
ce……… '''