………Kafin Babandi ya iso inda suke ma already Mubarak yayi wa Ahmad babban illa, domin zuwa wannan lokacin babu abunda yakeyi sai bleeding, tuni idanunsa har sun fara kafewa, a yayin da bakinsa kuma ya bud'e ya fara wani irin hamma mai kama dana tafiyar rai, cikin wani irin yanayi yake kallon Babandi, kallo mai kama dana ban kwana, jin Babandi na ce masa, bari a kai shi Asibiti, yana bleeding, cikin sarkewar murya ya ce.......
"Kar ka damu d'an uwana, nikam nasan tawa ta k'are domin kuwa nasan mutuwa zanyi, amma kafin nan, ka kiraminsu Tiger, (sauran abokanan su.)
........Dukkansu zagayeshi sukayi , cikin mutuwar jiki, kallonsu yayi, kana yayi d'an guntun murmushi,
" kunga yadda Allah yayi dani, nasan zan rasu zan barku, haka kuma bansan me zan tarar ba, hakan yasa nake rokon ku, dan Allah ku ma ku tuba zuwa ga Allah, Kumurci, Shaho, Oxle, Labar-bar, Bubaldu, Tiger, nd Babandi, please ku tuba, tiger ko bayan raina, don Allah ka karb'i musulunci, ku min wannan alfarman kunji? Ya fad'a yana sauk'e wani irin numfashi, wanda daga gani ansan na wahala ne,
Cikin mutuwar jiki suka amsa masa da "in sha Allah," tiger kuwa a hannunsa ya karb'i kalman shadara,
Cikin sanyin murya dake nuna lallai rai ya kusan barin jiki ya ce "Dan Allah ku ne ma min gafara a wajen Mamy, sa bo da tafiyar da nayi ba tare da izinin ta, ba sannan ku ce ina son ta, kuma ta kasance mai min addu'a ita da Daddy da ya Sadiq suma su yafe min, sannan dan Allah karku bari Mamy na tayi kukan rashi na ko bayan raina, sannan ku shaidawa su Mamy, cewa *karsu manta da maganata wanda nayi tun a baya, ku ce musu yanzu lokaci yayi daya kamata a cikamun wasiyya ta....* daga haka wani irin tari ya sarkafe shi, nan ko ya fara aman bak'in jini, dake nuna jini ya tsinke masa ta ciki, tarin bai d'auki lokaci mai tsayi ba, kuwa bakin sa ya fara fad'in,
La'ilaha illallahu, Muhammadu-rasulullahi, sallall lahu alalihi wa sallama........Ya mai-mai ta hakan ya kai sau biyu ana ukun rai yayi halinsa, idanunsa suka kafe suka kalli sama, jikinsa ya sake bayan ya k'ara tsayi, yayi wani irin HASKE na ban mamaki, hasken dake nuna shi kenan ruhi yayi sama ya rabu da ganganar jikin da aka d'auki shekara da shekaru ana ginawa ta hanyar bashi abinci da na sha.......
_Abin da yasa masu iya magana su fad'in Malami yafi uba kenan..... Domin tsakanin uba da Malami ko wanne yana da daraja, sai dai kowa da inda yake ginawa......_
_Mahaifi shi ne mai kawo abinci, sutura, d'aukan nauyin komai na gida kaman yadda ya rayata a wuyan ko wani magidanci......_
_A yayin da Malami kuma ya kasance mai koyar da Alqur'ani da sauran littatafan da suka shafi addini, da kuma tarbiya....._
_Hakan yasa Uba ya kasance yana Gina gangar jiki ne, a yayin da Malami kuma ya kasance yana Gina ruhi....._
_Duk dad'in abincin da ka ci komai kyawun sa haka kuma tsad'arsa karshensa k'asa ne, idan ma bai aikata mai kyau ba, karshe tsutsa ne zai ci duk wannan ginuwar jikin....._
_Allah ya tak'aita mana wahala, ubangiji ya tsare mu ha tsare mana imanin mu, Allah ya d'auki ran mu akan tuban mu, Uban giji shiryemu shiriya irin ta addinin musulunci, Allah yasa muyi kekkyawan k'arshe......._
***
Hakan kuwa yayi dai-dai da bugawar da kirjin Mamy yayi, gabanta ya fad'i, kana kanta ya Sara mata, cikin azama ta mik'e daga kam sallayan data kasa bari tun bayan idar da sallan, tana jin tsinkewar jinin data kwana biyu dashi yana k'aruwa......