..........Zaune suke a D'akin Mummy, Anty Safiya, Afrah, SIMRAH da kuma Maman Twins wacce bata jima da zuwa ba, don Baby na hannunta, bayan anyi mata wanka an shiryata cikin kayan sanyi na jarirai mai shegen kyau, kalan pink mai haske.
Ruwan d'umi Maman Twins ta diba a marfafin flaks kana ya fara bawa yarin yar dake ta ke kukan yunwa, Maman Ameer ce ta kalli Mummy cikin b'acin rai ta ce
"Wai ke Hauwa wani irin hali ne wannan? Kina nufin itama wannan jinjiran tagayyarar da ita zakiyi kaman SIMRAH? Me yake damunki ne haka? Kina halitta ne? Ko kina gyara halitta?
"Wannan ai shiga hurumin Allah ne, haka kawai ki d'auki karan tsana ki dorawa Yara, su suka halicci kansu ne don suna bak'ak'e?
"Ai Maman Twins rabu da ita, na rasa me take nufi da muta ne, wai mutum ya haifi yaro amma ya ce baya sonsa, ni yanzu haihuwar nake nema ido a rufe amma Allah bai bani ba, cewar Anty Safiya.....
" Rabu da ita Safiya, abun nata, naga yana neman wuce gona da iri, tunda Allah ya halicceni ban tab'a ganin irin wannan abun ba, Wallahi Hauwa k'wanyar kanta yana da bukatar dubiya, don kaman kanta da motsi....
Duk abinda su Maman Twins suke fad'a, Mummy tana jinsu, sai dai ci kanku bata ce ba, hasalima hankalinta baya kansu.
Ba yadda Maman Twins da Anty Safiya basu yi ba, amma inaa abun ya faskara, har takai Anty Safiya tayi hatsala ranta ya b'aci, kasance warta mai saurin fushi....
Cikin kosawa da maganar Mummy ta ce "magana kawai kukeyi, amma ni na riga da na yenke decision, don wallahi nayi deciding orphanage (gidan marayu) zan kaita, don wallahi gidana ba ma tattaran ajiye *bak'ak'e 'Y'aya* ba ne.
Don haka Gidan marayu zan kaita shi ne matattataran ajiye ko wani irin yaro, ta ida maganr tana kallon gefe.
Naga ta kaina ni Khadijah, dama haka kike? Har yanzu kina kan wannan ak'idar taki na kin 'Ya'ya bak'ak'e?
Cewar Maman Twins."Tsaya Maman Twins please, wai akan menene Maman Afrah bata son wannan Baby'n? cewar Anty Safiya....
"Hmm barta da mummunar ak'ida da kuma banzan ra'ayi, wai sa bo da batason bak'ak'e ne shi ya sa, ita gata baturiya, kuma ba wannan ce kad'ai bata so ba, har da wannan yarinyar, ta k'arasa maganar tana nuna SIMRAH wacce kanta yake k'asa da hannu. Maman Twins ta bawa Anty Safiya amsa tana mai dallawa Mummy harara kaman idonta zai dawo.....
"Yau naga bone ni []ar mutum biyu, jikar mutum hud'u, dama haka ne? Aini bansan dawar garin....
"Yanzu akan Allah ya baki bak'ak'e shine kike wannan abun? Akan ki gode masa kin zabi gwara ki masa izgili akan kyautar da yayi miki, wanda ba Wanda zai iya baki irinsa??
....."Ni da kike kallo na nan, aurena shekara goma sha yakwas amma ko b'ari ban tab'a yi ba, neman haihuwar nake ido rufe.
"Amma ke sa bo da bak'in hali, da mugun hali irin naki, har kina da bakin zabe? Dama bawa shi yake zabawa kansa abu ko kuma mafi alkhairi zai nema a wajen mahaliccinsa Allah, Ubangijin kowa da komai? Idan futsari banza ne Kaza tayi mana, idan bayarwa da dad'i sai ki bawa kanki cikin, sannan ki sakasu su, su kasance farare, idan kinaso ma kar farinsu yayi kama dana mutane, suyi HASKE kaman Takarda, aikin banza kawai!
Anty Safiya ya kai ayar maganar cikin zallan b'acin rai...."Nifa wallahi kunne na ya gaji da jin ihunku, sannan kuna cikawa Yarinyata kunne da hayaniya, bayan wahalan da wannan shegiyar yarinyar ta bani kuma kunzo kuna k'aramin wani ciwon kai, ku barni mana na fama da damuwata.
"Sau nawa zan gaya muku especially ke Maman Twins, ai kinsani, wallahi da a wajen scanning ana gane skin colour'n yaro, wallahi da ba'a kai wannan matakin ba!
"Da tun cikin yana k'arami na kwab'ar da 'Yar iska kowa ya huta! Ai dama ra'ayi riga ne, kowa kuma da irin nasa, don haka daga kan wannan shegiyar yarinya, mai bak'ar fuska kaman bakin tauren na daina bawa bakake no-nona suna sha ba, don ni ba tagayyararrriya bace.
Ta k'arasa maganar tana nuna SIMRAH wacce kanta yake a sadde k'asa, tamkar bata jin duk abunda suke fad'a, sai dai d'aukan komai take daki-daki.
"Haba tunda na samu cikin nan nayi ban kwana da lafiya, kullum a kwance nake ko ruwa ya shafa min lafiya kaman a kaina aka fara haihuwa....
"Wad'annan bak'ak'en Yayan, ta fad'a tana nuna SIMRAH da Baby'n, nasha wahala a cikinsu kaman zan bakunci lahira, amma kinga cikin *YAR LELE NA* (Twinny na), *SHELELE NA* (Mrs Ibrahim) kuma *YAR GATA NA* sauk'i kaman Shan ruwa.
"Daga samun cikin zuwa haihuwarta banyi ciwon kai na good five hours ba. Amma kinga wad'annan sai da abinci ya gagareni ci don azaban ciwo.
"A haihuwar wannan yarin yar mai suna SIMRAH, a cikin labour room sai da nace a kiramin Mahaifiyata don muyi ganawar karshe sa bo da ta yafemun, don banyi tunanin zan tashi ba, haka ma wannan yarin yar, kaman zan mutu sa bo da azaba da wahala. Don wahalar dana sha, sai dana manta sunana dana Mahaifiyata, saboda bak'ar iziyar da ta shayar dani....
"Amma tsakani da Allah kiga yadda na haifi Afrah, cikin awanni kalilan, idan ba wai naji tsoron karya ba, wallahi sai nace bayan gari mai tauri ma yafi nak'udan Afrah zafi da ciwo da komai. (ke Mummy kiji tsoron Allah, karya fa zagin Allah ne.)
Amma banda wad'annan, musamman wannan mai Fuska kaman an sulala Karas, bayan wahala sai da ta barni da uban yanka a jikina, Wanda zan mutu dashi....
Cikin zallan b'acin ran da bata tab'a ganin Maman Ameer d'in a ciki ba, kana cikin kakkausar murya ta ce " ina neman wani alfarma idan zaki iya min.
"Fada koma mene indai baifi karfina ba zan miki Hajiya Kubrah, ai kin wuce haka a yanzu ke tamkar Uwa ce ko babbar Ya a wajena.
"Karki manta akwai k'ulelliyar alk'awari a tsakanina dake na haihuwar SIMRAH, don haka inason a d'ora na wannan Baby'n akan na SIMRAH.
Numfashi Mummy ta sauk'e kana ta ce "ai wannan ba matsala ba ne, sai dai baki fad'i lokaci ba.
"Dai-dai da lokacin Addarta itama, cewar Maman Ameer tana mai mikewa Baby'n a hannunta.
Gaban Mummy ta isa, kana dora mata yarinyar akan cinyarta, bayan ta ture kan Afrah dake kan kafafunta, wacce ta tashi tana zumbura baki.
"Kallon yadda ta tura Afrah tayi, sai dai bata yi magana ba sanin darun Maman Twins yaci Uwar nata, mussaman da yanzu ta riga da ta shak'a, kana ta ce "amma baki manta da shekarun ba ko? Daga 15 zuwa 18 idan baki cika alk'awari ba, zan iya kaiki k'ara kotu....
"Ba damuwa Hauwa'u babu abin da zai gagara insha Allah," inji Maman Twins.
"Amma wallahi ki sani duk abin da na kashe wajen siyan kayan wannan shegiyar Baby zaki biya ni, don bazan d'auki asara ba, Fad'ar Mummy.
Cikin muryan da bai gama watstsakewa daga b'acin rai ba, ta ce "zan biyaki K'udinki Hauwa'u, har ma da kari, amma ki sani daga yau no more *SHEGIYA*, tunda kinfi kowa sanin hanyar da aka bi, aka sameta, don haka kar a sake shegantamin *'Ya'ya* if not, wallahi zan kwashi adashen tsiya dake........